ukarofi

12568 Posts
Yadda kitimurmurar siyasa a Yobe ta tilasta wa Ahmed Lawan janye neman takarar gwamna

Yadda kitimurmurar siyasa a Yobe ta tilasta wa Ahmed Lawan janye neman takarar gwamna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kokawar neman kujerar gwamnan jihar Yobe gabanin zaɓen 2027 ya ɗau wani sabon salo biyo bayan haɗa ƙarfi da ƙarfe da gwamna Mai Mala Buni da ministan hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta ƙasa, Ibrahim Gaidam, wanda hakan ya kawo ƙarshen burin da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ke da shi. Al’amura sun sauya ne bayan da Baba Malam Wali ya samu goyon bayan jam’iyyar APC domin zama ɗan takarar gwamna. Wali ya samu goyon bayan tsagin jjam’iyyar ne masu ƙarfin faɗa-a-ji wanda hakan ya tilasta wa Lawan janye ƙudurinsa na neman…
Read More
Maniyyatan Nijeriya 6,000 sun isa ƙasa mai tsarki

Maniyyatan Nijeriya 6,000 sun isa ƙasa mai tsarki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa zuwa yanzu maniyyata 6,635 daga Nijeriya sun isa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana. Bayanan cibiyar kula da jigilar alhazai ta hukumar sun nuna cewa an yi jigilar ne ta jirage 14 tun bayan soma jigilar maniyyatan a ranar 3 ga watan Mayu. Hukumar ta ce zuwa yanzu an yi jigilar maniyyatan da suka haɗa na jihohin Kebbi, Kogi, Nasarawa, Ogun, Oyo, Jigawa, Gombe da Osun, inda aka sauke mafi yawansu a biranen Madina da Jeddah. Bayanai sun ce kamfanonin jiragen sama da ke…
Read More
Kotu ta samu tsohon Ministan Lantarki da almundahanar biliyan N33.8

Kotu ta samu tsohon Ministan Lantarki da almundahanar biliyan N33.8

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta samu tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, da laifin halasta kuɗaɗen haram har naira biliyan 33.8. Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ya ce Hukumar Yaƙi da Rashawa EFCC ta tabbatar da tuhume-tuhume 12 da ake yi wa tsohon ministan ba tare da wata shakka ba. Kotun ta bayyana cewa, daga cikin jerin laifukan, an karkatar da kuɗin aikin wutar lantarki na Zungeru da Mambilla na aƙalla Naira biliyan 22 ta hannun wanda ake tuhuma da wasu na kusa da…
Read More
Kotu ta bai wa El-Rufai izinin zuwa jinya a Abuja

Kotu ta bai wa El-Rufai izinin zuwa jinya a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar Kotun tarayya da ke Kaduna ta bai wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, izinin zuwa neman maganin haƙori da ido a wasu asibitoci da ke Abuja ƙarƙashin kulawar jami’an ICPC. Mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, Okor Odey, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Sanarwar ta ce lauyan El-Rufai ya roƙi kotu da ta umurci ICPC ta ba wanda ake tuhuma damar samun kulawar lafiya. Kotun ta umurci ICPC da ta riƙa raka El-Rufai zuwa asibitocin da ya…
Read More
Amnesty ta yi Allah-wadai da bangar siyasa a Kano, ta buƙaci a binciki kisan mutane biyar

Amnesty ta yi Allah-wadai da bangar siyasa a Kano, ta buƙaci a binciki kisan mutane biyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International Nigeria ta buƙaci hukumomin Nijeriya da su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan kisan wasu mutane biyar da ake zargin wasu ‘yan daba masu dauke da makamai sun kai musu hari a jihar Kano. Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta yi Allah-wadai da lamarin tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan tashe-tashen hankulan siyasa da aka samu a jihar Kano cikin ‘yan shekarun nan. A cewar ƙungiyar, lamarin ya faru ne ranar Talata 5 ga watan Afrilu,…
Read More
Jiragen ruwa maƙare da fetur da abinci za su iso Nijeriya – NPA

Jiragen ruwa maƙare da fetur da abinci za su iso Nijeriya – NPA

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) ta sanar da ana sa ran jiragen ruwa guda 36 ɗauke da kayayyaki daban-daban, ciki har da man fetur da kayan abinci, za su isa manyan tashoshin jiragen ruwa na Legas. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a rahoton ta na yau da kullum mai taken “Daily Shipping Position”, NPA ta bayyana cewa jiragen za su sauka ne a tashoshin Apapa Port, Lekki Deep Sea Port da kuma Tin Can Island Port tsakanin ranar 5 zuwa 10 ga watan Mayu. Hukumar ta ce daga cikin…
Read More
Yadda bashin Nestoil ya jefa bankunan Nijeriya cikin ƙalubale

Yadda bashin Nestoil ya jefa bankunan Nijeriya cikin ƙalubale

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fargaba na ƙaruwa a fannin bankunan Nijeriya bayan da wasu manyan bankuna uku suka gaza sanar da ribar masu hannun jari a sakamakon shekarar kuɗi ta 2025, sakamakon tarin basussuka masu nauyi, inda kamfanin mai na cikin gida, Nestoil Limited, ke da kusan bashin Naira tiriliyan 2.9. Masana na ganin wannan lamari na nuna wata babbar jarrabawa ga tsarin bankunan ƙasar, musamman a daidai lokacin da ake aiwatar da tsarin gyaran lissafin kuɗi. Daga cikin bankunan da lamarin ya fi shafa akwai United Bank for Africa (UBA) da Access Bank, waɗanda ba su fitar da ribar…
Read More
Baba-Ahmed ya yi kakkausar suka ga Obi kan ficewa daga Jam’iyyar LP

Baba-Ahmed ya yi kakkausar suka ga Obi kan ficewa daga Jam’iyyar LP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Datti Baba-Ahmed, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar LP, ya soki Peter Obi kan ficewa daga jam’iyyar a lokacin da ake fama da rikicin cikin gida a maimakon tsayawa ya yi ƙoƙarin warware matsalar. Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a ranar Litinin jim kaɗan bayan sauya sheƙa daga LP zuwa PRP a Abuja. An ɗauki kalaman nasa ne a wani bidiyo da yake yawo a shafin Facebook. Sukar tasa na zuwa ne bayan da Obi da Kwankwaso suka sauya sheƙa daga ADC zuwa wanda ya jawo hasashen cewa akwai…
Read More
An buƙaci APC ta bai wa Mu’azu Jaji tikitin takarar Gwamnan Taraba

An buƙaci APC ta bai wa Mu’azu Jaji tikitin takarar Gwamnan Taraba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani mai goyon bayan Injiniya Muazu Jaji Sambo a Jihar Taraba, Naseeru Taneemu Annuree, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC na ƙasa da na jihar Taraba da su bai wa tsohon Ministan Sufuri, Mu’azu Jaji Sambo, tikitin takarar gwamnan jihar Taraba domin ceto jihar da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’umma. Naseeru Taneemu Annuree ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai kan halin da siyasar jihar Taraba ke ciki da kuma shirye-shiryen jam’iyyar APC gabanin zaɓe mai zuwa. Ya ce babu shakka Mu’azu Jaji Sambo na…
Read More
An ɗaure matashi rai-da-rai kan yi wa yarinya fyaɗe

An ɗaure matashi rai-da-rai kan yi wa yarinya fyaɗe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata kotun sauraron ƙararrakin iyali da ke Kalaba a Jihar Kuros Ribas, ta yanke wa wani matashi mai suna Nyojole hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan samunsa da laifin yi wa wata yarinya mai shekara 13 fyaɗe.  Mai shari’a Blessing Egwu ta ce kotun ta gamsu da hujjoji da shaidu da aka gabatar, ciki har da takardun gwajin asibiti da suka tabbatar da aikata laifin. Shaidu sun bayyana cewa wanda aka yankewa hukuncin ya yaudari yarinyar zuwa wani kango a yankin ƙaramar Hukumar Kalaba ta Kudu, inda ya ba ta Naira 1,600 kafin aikata laifin. Kazalika,…
Read More