Yadda kitimurmurar siyasa a Yobe ta tilasta wa Ahmed Lawan janye neman takarar gwamna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kokawar neman kujerar gwamnan jihar Yobe gabanin zaɓen 2027 ya ɗau wani sabon salo biyo bayan haɗa ƙarfi da ƙarfe da gwamna Mai Mala Buni da ministan hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta ƙasa, Ibrahim Gaidam, wanda hakan ya kawo ƙarshen burin da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ke da shi.

Al’amura sun sauya ne bayan da Baba Malam Wali ya samu goyon bayan jam’iyyar APC domin zama ɗan takarar gwamna.

Wali ya samu goyon bayan tsagin jjam’iyyar ne masu ƙarfin faɗa-a-ji wanda hakan ya tilasta wa Lawan janye ƙudurinsa na neman takarar duk kuwa da irin daɗewa a harkokin siyasa da sunan da ya yi tun daga tushe a ƙananan hukumomi shida na yankin Yobe ta Arewa.

“Na nemi a ban ɗan lokaci domin na fita waje na tuntuɓi magoya baya. Mu masu goyon bayan ne ga matakin da shugabancin jam’iyyar ya ɗauka,” in ji Lawan.

“Ina jaddada cikakkiyar goyon bayana kuma a shirye nake na janye aniyata ta neman takarar.”

Masu fashin baƙi sun alaƙanta matakin nasa da zahirin siyasar da ke faruwa da ƙabilanci da aka duba. Duk da cewa shi ya fito ne daga ƙaramar ƙabilar Badawa,

Lawan ya dogara ne da samun goyon bayan ‘yan ƙabilar Kanuri waɗanda su ne mafi rinjaye. Sai dai ƙalubalantar Wali, wanda ɗan ƙabilar Kanuri, na iya yuwawa dalilin da ya sauya wancan lissafi na Lawan.

Sannan nuna goyon bayan na nuna yadda aka yi lissafin siyasa ganin cewa yankin Yobe ta Arewa tun 1999 ba ta samar da ɗan takarar gwamna ba. Sai dai masu fashin baƙi sun ce duk da daɗewar Wali a matsayin sakataren gwamnati tun shekarar 2015, bai yi wani suna kamar Lawan ba.

Haka kuma masu fashin baƙin na ganin cewa siyasar jihar na neman zama gado saboda Gaidam ya mulki jihar Yobe na kusan shekaru 10 bayan gadar marigayi Mamman Ali a shekarar 2009 kafin miƙa mulki ga Buni wanda sirikinsa ne a shekarar 2019.

A yanzu kuma Buni na shirin kammala wa’adin mulkinsa na biyu kuma akwai rahotanni da ke nuna yana shirin tafiya majalisar datatwa inda zai maye gurbin sirikinsa a yankin Yobe ta gabas.”

Duk da cewa an cimma matsaya ta tsayar da Wali, an samu wasu da suke adawa da hakan. Sanata Ibrahim Bomai ya yi watsi da mara wa Wali baya da aka yi, yana mai cewa lamarin ya saɓa wa dimokraɗiyya.

“Rahoton mara wa wani baya a fili yake cewa an keta haddin manufofin dimokraɗiyya,” in ji Bomai. “Wannan abin damuwa ne sosai ganin yadda mutum ɗaya ke ƙoƙarin yanke abin da ya kamata miliyoyin mutane su yanke ta hanyar tsarin da aka tanada.”

Ya ƙara da cewa, “jihar Yobe ta al’ummarta ce, ɓa wai ta wasu ɗaiɗaiku ba ko wasu rukunin al’umma ba.” Ya sha alwashin ƙalubalantar matakin ta hanyar shiga zaɓen cikin gida.

Sauran waɗanda suke neman takarar ta haɗa da Usman Alkali Baba da mai rajin ganin an samar da cigaba Kashim Tumsah, waɗanda suka nuna damuwarsu kan rashin adalci da tauye dimokraɗiyya. Tumsah ya yi gargaɗin cewa rashin yin komai a buɗe ka iya yi wa jam’iyyar lahani da aminta da aka yi da ita gabanin zaɓen 2027.

Wannan dambarwa na haska wani abu da ya taɓa faruwa a siyasar jihar Yobe. A shekarar 2007, sauya Usman Albishir da Ali da shugabannin jam’iyyar suka yi ya jawo dambarwar siyasa wanda ke nuan irin tsamar da ke tsakanin ƙoƙarin nuna iko kan jam’iyyar a maimakon dimokraɗiyya. Sai dai daga baya kotun ƙoli ta tabbatar da halascin takarar Ali.

A yayin da ake shirin ɓarje gumi gabanin zaɓen 2027, APC tana tsaka mai wuya na daidaita tsakanin manyan ‘yan siyasa da dimokraɗiyya. A yayin da haɗakar Buni-Gaidam ta karfafa ikonsu, akwai waɗanda suka ja tunga waɗanda za su ja daga a jihar Yobe.

By ukarofi