Maniyyatan Nijeriya 6,000 sun isa ƙasa mai tsarki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa zuwa yanzu maniyyata 6,635 daga Nijeriya sun isa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Bayanan cibiyar kula da jigilar alhazai ta hukumar sun nuna cewa an yi jigilar ne ta jirage 14 tun bayan soma jigilar maniyyatan a ranar 3 ga watan Mayu.

Hukumar ta ce zuwa yanzu an yi jigilar maniyyatan da suka haɗa na jihohin Kebbi, Kogi, Nasarawa, Ogun, Oyo, Jigawa, Gombe da Osun, inda aka sauke mafi yawansu a biranen Madina da Jeddah.

Bayanai sun ce kamfanonin jiragen sama da ke gudanar da jigilar sun haɗa da Flynas, UMZA, MaɗAir da Air Peace.

NAHCON ta ce aikin na gudana cikin tsari yayin da dubban sauran maniyyatan ke dakon lokacin tasu jigilar zuwa ƙasa mai tsarki.

Hukumomin Saudiyya sun kuma sanya wa’adin rufe filayen jiragen da ke karɓar alhazai kafin fara manyan rukunan aikin Hajjin, lamarin da ya sa ake ƙara ƙaimi wajen kammala jigilar cikin lokaci.

By ukarofi