ukarofi

12568 Posts
APC ta sanar da 9 ga Mayu don tantance Barista Kashim Musa a Yobe

APC ta sanar da 9 ga Mayu don tantance Barista Kashim Musa a Yobe

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar APC ta sanya ranar Asabar, 9 Ga Mayu, 2026, don tantance Barista Kashim Musa Tumsah a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen takararsa na gwamna a Jihar Yobe. Abubakar Ahmed, jakakin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen sa yayi wannan jawabi cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gusau yau Juma'a. A cewarsa, kwamitin da shugabannin APC suka kafa zai gudanar da tantancewar kuma an shirya gudanar da ita da ƙarfe 1:00 na rana a Transcorp Hilton, Abuja. Ahmed ya jaddada cewa ana ganin taron a matsayin wani muhimmin mataki biyo bayan bayyanar Tumsah…
Read More
‘Yan sandan Nasarawa sun cafke masu garkuwa da mutane

‘Yan sandan Nasarawa sun cafke masu garkuwa da mutane

Daga JOHN D WADA a Lafia Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta kama mutum takwas da ake zargi da garkuwa da mutane sannan ta kashe mutum ɗaya cikinsu yayin wani sintiri na musamman da jami'an suka gudanar jim kaɗan da samun labarin garkuwa da mutanen. Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Nasarawa Mohammed Shatima Jauro ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Alhamis a ofishin sa dake Lafia. Ya bayyana rahoto kan wannan gagarumin nasara da rundunar ta samu a yaƙi da masu garkuwa da mutanen da sauran laifuffuka masu tashin hankali a…
Read More
Tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa ya bayyana niyyar tsaya wa takarar Majalisar Dattawa

Tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa ya bayyana niyyar tsaya wa takarar Majalisar Dattawa

Daga JOHN D WADA a Lafia Tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa Hon. Silas Ali Agara ya bayyana a hukumance niyyar sa ta tsayawa takarar kujerar sanata ta Arewacin jihar Nasarawa a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Silas Agara wanda kwanan nan ya sauka daga muƙamin Daraktan Janar na hukumar samar da aikin yi na tarayya wato NDE domin amsa abin da ya kira “kiran gaggawa” daga mutanen mazaɓarsa. Da yake jawabi ga kwamitin gudanarwa na jihar na APC a sakatariyar jam’iyyar da ke Lafia a ranar Alhamis Hon. Agara ya roƙi shugabannin jam’iyyar da su tabbatar da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta haramta wa masu digirin girmamawa amfani da kalmar ‘Dakta’

Gwamnatin Tarayya ta haramta wa masu digirin girmamawa amfani da kalmar ‘Dakta’

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da sabuwar doka wadda ta hana duk wanda aka ba wa digirin girmamawa, wato ‘Honorary Doctorine Degree’, amfani da laƙabin “Dakta” a farkon sunansa a kowane fanni na hukuma, ilimi ko sana’a, tana mai cewa hakan na nuni da yaudara da karkatar da gaskiyar cancantar ilimi. Ministan Ilimi, Malam Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja yayin ganawa da ’yan jarida, inda ya ce an amince da sabuwar manufar ne a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) domin daidaita tsarin bayar da digirin girmamawa a…
Read More
Wanda ya kafa CNN, Ted Turner, ya rasu

Wanda ya kafa CNN, Ted Turner, ya rasu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ted Turner, fitaccen ɗan kasuwa kuma wanda ya kafa shahararriyar kafar yaɗa labarai ta CNN, ya rasu yana da shekaru 87 a duniya. Rahotanni sun bayyana cewa Turner, wanda ya yi suna a harkokin kasuwanci, wasanni da kafafen yaɗa labarai, ya rasu ne ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026. Kamfanin Turner Enterprises ya tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da ya fitar, sai dai bai bayyana musabbabin mutuwar ba. Tun a watan Satumban 2018 ne Turner ya bayyana cewa yana fama da cutar Lewy body dementia, wata cuta mai lalata jijiyoyin ƙwaƙwalwa da ke shafar…
Read More
Ba ni da wurin zama da ’ya’ya 10, inji matar da aka saki a kotu

Ba ni da wurin zama da ’ya’ya 10, inji matar da aka saki a kotu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata mata mai shekara 44, Zainab Isah, ta bayyana cikin kuka a gaban Kotun Shari’a da ke yankin Magajin Gari a Jihar Kaduna cewa ba ta da inda za ta nufa bayan mijinta ya sake ta, duk da cewa tana da ’ya’ya goma. Zainab ta shaida wa kotu cewa an aurar da ita tun tana da shekara 14 ga tsohon mijinta, Abdulhamid, inda suka shafe kusan shekaru 30 suna zaman aure tare. “Na haifa masa ‘ya’ya goma, kuma mun zauna lafiya tsawon lokaci,” inji ta. Ta ƙara da cewa, mijin nata ya sake ta ne a…
Read More
APC ta yi wa Tinubu rangwamen sharuɗɗan tantancewa gabanin zaɓen fidda gwani

APC ta yi wa Tinubu rangwamen sharuɗɗan tantancewa gabanin zaɓen fidda gwani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar APC ta sanar da cewa ta sallami sharuɗɗan tantance Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ba shi damar shiga zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa ba tare da sake bayyana a gaban kwamitin tantancewa ba. An cimma wannan matsaya ne a taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) karo na 188 da aka gudanar ranar Laraba, 6 ga Mayu, 2026, a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja. A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Feliɗ Morka, ya fitar, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bisa ikon da kundin tsarin mulkin…
Read More
Guguwa ta lalata gidaje sama da 1,200 a Jihar Neja

Guguwa ta lalata gidaje sama da 1,200 a Jihar Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata mummunar guguwa ta lalata gidaje sama da 1,200 a wasu al’ummomi da ke jihar Neja. Babban Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Kwamared Abdullahi Baba Arah, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayar da rahoton halin da ake ciki ranar Alhamis a Minna. A cewarsa, guguwar ta yi ɓarna a ƙananan hukumomi shida na jihar da suka haɗa da Mokwa, Bida, Laɓun, Katcha, Gbako da Mariga. Ya ce hukumar NSEMA ta fara gudanar da bincike cikin gaggawa domin tantance irin ɓarnar da guguwar ta yi da kuma buƙatun…
Read More
ACF ta afka rikici kan biliyoyin Naira

ACF ta afka rikici kan biliyoyin Naira

*An dakatar da Shugaban Kwamitin Amintattu Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamitin Zartarwa na ƙasa na ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ya dakatar da Shugaban Kwamitin Amintattu na ƙungiyar, Alhaji Bashir M. Dalhatu, bisa zargin almundahanar kuɗi da take ƙa’idojin kundin tsarin mulki, a wani mataki mai tsauri da ya ƙara ruruta rikicin shugabanci a cikin ƙungiyar. An yanke wannan hukunci ne a wani taron gaggawa na NEC da aka gudanar a Kaduna a ranar Laraba, a daidai lokacin da ake taƙaddama kan rahotannin hana shiga hedikwatar ACF da ‘yan sanda suka yi gabanin tarurrukan da aka shirya gudanarwa. Yayin da…
Read More
Tinubu ya jaddada ƙudurin gyaran tattalin arzikin Nijeriya ga masu zuba jari na duniya a Faransa

Tinubu ya jaddada ƙudurin gyaran tattalin arzikin Nijeriya ga masu zuba jari na duniya a Faransa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da manyan masu zuba jari na ƙasashen duniya a Paris, Babban Birnnin ƙasar Faransa, inda ya jaddada aniyarsa ta tabbatar da gaskiya, daidaiton kuɗaze da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki cikin gaggawa. Shugaban, wanda ya bar Nijeriya a ranar Lahadi domin wata ziyarar ƙasashe uku, ya bayyana cewa shirin gyaran tattalin arzikin gwamnatinsa ya ƙunshi matakan kawar da tangarɗar tsarin kuɗi tare da daidaita manyan alamu na tattalin arziki, domin shimfiɗa tubalin bunƙasa mai ɗorewa da haɗa kowa da kowa. Tinubu ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa na da niyyar…
Read More