09
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ‘yan bindiga sun ƙone sansanin sojoji da motocinsu biyu a ƙauyen Bagega da ke Anka a jihar Zamfara a ranar Asabar. Masu mazauna garin da sojoji biyu sun ji rauni a lokacin harin da ‘yan ta’addan suka kai waɗanda suka sace wa mutane kayayyaki a shagunansu. Mazaunan sun shaida wa Blueprint Manhaja cewa, ‘yan ta’addan sun so su tashi kasuwar Bagega da ake ci ne a ta mako-mako ne, amma sojojin da suke zaune a ƙauyen sun yi fito-na-fito da su inda aka kwashe awa biyu ana ba-ta-kashi kafin ‘yan ta’addan su gudu…
