10
May
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta yi kira ga al’ummomin da ke gefen layin dogo na Abuja zuwa Kaduna da su taka rawar gani wajen kare jiragen ƙasa da kayayyakin layin dogo, sakamakon ƙaruwar hare-hare da lalata kayayyaki da ake fuskanta a yankin. Wannan kira na zuwa ne bayan karuwar ayyukan wasu bata-gari da ke kai hare-hare kan jiragen ƙasa tare da lalata sassan su, lamarin da hukumar NRC ta yi Allah-wadai da shi, tana mai cewa masu aikata laifukan sun samu damar aiwatar da ayyukansu cikin sauƙi a wasu wurare. Hukumar ta bayyana cewa…
