Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da gyaran dokokinta na cikin gida, inda ta taƙaita cancantar tsayawa takarar Shugaban Majalisar Dattawa ga ‘yan majalisar da suka riga suka yi aiki a Majalisar ta 10.
An yanke wannan hukunci ne bayan wani dogon zama na sirri da sanatoci suka yi a ranar Talata, inda suka amince da sabbin ƙa’idoji da nufin ƙarfafa tsarin matsayi, gogewa da kuma ƙwarewa a cikin majalisar.
A ƙarƙashin sabon tsarin, an tanadi cewa sai sanata da ya yi aƙalla wa’adi biyu ne zai iya tsayawa takarar muƙaman shugabanci a majalisar, ciki har da kujerar Shugaban Majalisar Dattawa.
Haka kuma, dokar ta ƙara da cewa dole ne ɗaya daga cikin wa’adin ya kasance na kusa da lokacin da ake shirin tsayawa takara, abin da ke rage yawan waɗanda za su iya neman muƙaman jagoranci a majalisar.
Sabon gyaran da aka yi wa Dokar Tsari ta 4 (Order 4) ya fayyace cewa za a riƙa zaɓar shugabannin majalisa ne bisa tsari da matsayi na sanatoci, wanda ya haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa, tsofaffin manyan shugabanni a majalisar, sanatocin da suka yi aƙalla wa’adi guda, da kuma waɗanda suka taba zama ‘yan Majalisar Wakilai.
A bisa wannan tsari, sanatocin da ke Majalisar ta 10 ne kaɗai za su samu damar tsayawa takarar shugabanci a Majalisar ta 11 idan suka sake lashe zaɓe, wanda hakan ke ƙara taƙaita damar sababbin sanatoci.
Majalisar ta bayyana cewa manufar wannan gyara ita ce tabbatar da cewa waɗanda ke riƙe da manyan muƙamai suna da isasshen gogewa da fahimtar aikin majalisa, tare da kiyaye al’adar da aka daɗe ana bi wajen tsarin matsayi a majalisar.
Wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani gagarumin sauyi a tsarin tafiyar da harkokin Majalisar Dattawa, wanda ka iya yin tasiri ga yadda ake zaɓen shugabanni a nan gaba.
