Kara jarin bankuna: Tinubu ya yaba da sauye-sauyen CBN wajen farfaɗo da tattalin arziki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yaba wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, bisa jagorantar sauye-sauyen da ake yi a fannin kuɗi, yana mai cewa manufofin da ake aiwatarwa na taimakawa wajen sake gina tattalin arzikin ƙasa domin samun ci gaba mai ɗorewa.

Tinubu ya bayyana hakan ne bayan wa’adin ranar 31 ga Maris, 2026 na cika sharuɗɗan ƙarfafa jari ga bankuna, inda ya bayyana Cardoso a matsayin shugaba mai ƙwazo da mayar da hankali kan gyaran tsarin kuɗi.

Ya ce, sauye-sauyen, ciki har da gyaran tsarin musayar kuɗaɗen waje da kuma tsauraran dokokin kula da harkokin kuɗi, sun ƙara amincewar masu zuba jari tare da ƙarfafa tsarin bankuna a ƙasar.

A cikin jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce: “Dole ne in yaba wa mutum guda, Olayemi Cardoso, bisa irin ƙoƙarin da yake yi domin ƙasar nan,” yana mai jaddada cikakken amincewarsa da ƙwarewa da gaskiyar gwamnan CBN wajen tafiyar da wannan muhimmin aiki.

Shugaban ƙasar ya kuma nuna gamsuwa da yadda aka tafiyar da shirin ƙarin babban jari, musamman yadda aka kula da wasu bankunan da ke cikin shirin gyara, da suka haɗa da Union Bank of Nigeria, Polaris Bank da Keystone Bank, waɗanda har yanzu suke ci gaba da cika sharuɗɗan saboda wasu ƙalubalen doka da na tsari.

CBN ya tabbatar wa jama’a cewa duk da waɗannan ƙalubale, bankunan na ci gaba da aiki yadda ya kamata, suna da ƙarfi kuma suna iya biyan bukatun abokan hulɗarsu.

A cikin binciken da CBN ta gudanar, an gano wasu matsaloli a cikin bayanan kuɗi na Union Bank, wanda hakan ya kai ga rusa kwamitin daraktoci da manyan jami’an bankin a watan Janairu 2024. Wannan mataki ya haifar da shari’a, inda mai kula da bankuna ke ƙalubalantar hukuncin kotu da ya tambayi sahihancin wannan mataki. Haka kuma, shirin haɗewar Proɓidus Bank da Unity Bank na fuskantar wasu ƙalubalen shari’a, duk da cewa ana kyautata zaton za a warware su nan ba da daɗewa ba. Ga Polaris Bank da Keystone Bank, ana ci gaba da aikin cika sharuɗɗan ƙarin jari a ƙarƙashin sa ido na kusa daga hukumomi, bayan da CBN ya taɓa ceto su a baya.

Sabon tsarin ƙarin jari ya tanadi sabbin matakan kuɗi, inda aka ƙayyade mafi ƙarancin jari na naira biliyan 500 ga bankunan ƙasa da ƙasa, da kuma naira biliyan 200 ga bankunan ƙasa, matakin da ake kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka taɓa yi a tarihin bankuna a Nijeriya.

By ukarofi