Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan zargin cewa an cire kimanin Naira biliyan 1.5 daga kuɗaɗen ma’aikata a lokacin tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Abdullahi Musa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin Ranar Ma’aikata, inda ya ke mayar da martani ga zargin da Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) reshen jihar Kano, Kabiru Inuwa, ya gabatar. Abba Kabir Yusuf ya ce, ya riga ya umarci Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), Umar Faruƙ Ibrahim, da ya kafa kwamiti na musamman domin binciken zargin.
Ya kuma sha alwashin cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace kan duk wanda aka samu da laifi, tare da tabbatar da mayar da duk wani kuɗi da aka karɓa ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, “Daga jin wannan zargi, nan take na kira SSG, na kuma umarce shi da ya kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamarin. Ina tabbatar muku cewa duk wanda aka samu da hannu, gwamnati za ta ɗauki matakin da ya dace, kuma za a dawo da kuɗin.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa ta riga ta biya naira biliyan 32 daga cikin naira biliyan 48 na bashin giratuti da kuɗaɗen fansho na mutanen da suka rasu da ta gada daga gwamnatin baya. Ya yi alƙawarin cewa za a biya sauran naira biliyan 16 kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa.
Ya ce, “Mun gaji bashin giratuti da alawus-alawus da ya haura naira biliyan 48, wanda ya jefa masu ritaya da iyalansu cikin mawuyacin hali. Amma cikin ƙoƙari mai ɗorewa, mun biya naira biliyan 32 daga ciki, kuma muna da niyyar kammala saura kafin wa’adin gwamnati ya ƙare.”
Haka kuma, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta kafa wasu muhimman hukumomi da nufin inganta jin daɗin ma’aikata da bunƙasa ƙwarewarsu a aikin gwamnati. Ya bayyana cewa kafa Hukumar Kula da Ayyukan ƙananan Hukumomi ya taimaka wajen daidaita tsarin ci gaban ma’aikatan ƙananan hukumomi da na sauran ma’aikatan gwamnati.
Bugu da ƙari, ya ce an inganta jin daɗin masu ritaya ta hanyar ƙara mafi ƙarancin fansho daga naira 5,000 zuwa naira 20,000, matakin da ya ce ya taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar tsofaffin ma’aikata.
Tun da farko, Shugaban NLC na jihar Kano, Kabiru Inuwa, ya roƙi gwamnatin jihar da ta binciki zargin na naira biliyan 1.5 da ake yi wa tsohon Shugaban Ma’aikata. Haka kuma ya buƙaci gwamnati da ta magance bambancin albashi tsakanin ma’aikatan ƙananan hukumomi da na gwamnatin jiha, domin ƙara ƙwarin gwiwar ma’aikata da tabbatar da daidaito.
