ukarofi

12568 Posts
Buba Galadima ya buƙaci Atiku ya shiga NDC don haɗin kan ‘yan adawa a zaɓen 2027

Buba Galadima ya buƙaci Atiku ya shiga NDC don haɗin kan ‘yan adawa a zaɓen 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jigo a jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya shiga jam’iyyar, yana mai gargadin cewa zai iya zama sanadiyar gazawar haɗin kan ‘yan adawa idan bai yi haka ba kafin zaɓen 2027. Galadima ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels Tɓ, inda ya ce manyan ‘yan adawa na fara taruwa a ƙarƙashin NDC domin ƙarfafa haɗin gwiwa don kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki. Ya ce wasu fitattun ‘yan siyasa sun riga sun koma NDC, yana mai jaddada cewa dole ne a haɗa…
Read More
Jam’iyyar NDC ta warware rikicin shugabanci na Kano

Jam’iyyar NDC ta warware rikicin shugabanci na Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar NDC ta warware rikicin shugabanci da ya taso a reshen Jihar Kano, inda ta sake tabbatar da Husaini Isah Mai Riga a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar. NDC ta ɗauki matakin ne bayan da Mai Riga ya zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da yunƙurin ƙwace tsarin jam’iyyar a jihar. Rikicin ya biyo bayan shigar tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, cikin jam’iyyar. Zuwan Kwankwaso NDC ya haifar da tashin hankali a cikin reshen Kano, inda wasu mambobi suka fara tambayar makomar shugabancin Mai Riga. Mai Riga, wanda ya yi…
Read More
Muhawarar soyayyar Ross da Rachel a fim ɗin ‘Friends’ ta sake dawowa sabuwa bayan shekaru kusan talatin 

Muhawarar soyayyar Ross da Rachel a fim ɗin ‘Friends’ ta sake dawowa sabuwa bayan shekaru kusan talatin 

Daga AISHA ASAS  A duniyar fina-finan akwai labaran da lokaci ba ya iya share su. Daya daga cikin su shi ne rikicin soyayya tsakanin Ross da Rachel a cikin shahararren shirin barkwanci nan da duniya ta yi amo da shi, wato 'Friends' rikicin da ya haifar da sanannen  mai cike da ce-ce-ku-ce, wato “We were on a break.” Shekaru kusan talatin kenan, amma har yanzu waɗannan kalmomi guda uku na ci gaba da raba kan masoya shirin, inda wasu ke ganin hujja ce, wasu kuwa na ganin uzuri ne. Tsayin shekaru ana ja-ni-in-ja ka kan wannan muhawarar ta ko hujja…
Read More
Rikici ya ɓarke tsakanin Melania Trump da Jimmy Kimmel kan barkwancin da ya yi

Rikici ya ɓarke tsakanin Melania Trump da Jimmy Kimmel kan barkwancin da ya yi

Daga AISHA ASAS  *Uwargidan shugaban ƙasa ta zargi kalaman da haddasa ƙiyayya da tashin hankali *Trump ya nemi a kori mai gabatar da shirin, yayin da shiru ya mamaye ABC Wata sabuwar taƙaddama mai ɗaukar hankali ta ɓarke a Amurka bayan Uwargidan Shugaban ƙasa, Melania Trump, ta fito fili tana kakkausar suka ga fitaccen mai gabatar da shirin dare, Jimmy Kimmel, inda ta buƙaci tashar ABC ta ɗauki matakin ladabtarwa a kansa, har ma da yiwuwar korarsa. Wannan martani mai zafi ya biyo bayan wasu kalamai na barkwanci da Kimmel ya yi a cikin shirinsa na “Jimmy Kimmel Live”, inda…
Read More
Jihohi 32 da Abuja sun ci bashin Dala biliyan shida duk da ƙarin kuɗi daga Asusun Tarayya

Jihohi 32 da Abuja sun ci bashin Dala biliyan shida duk da ƙarin kuɗi daga Asusun Tarayya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bayanan da Hukumar Kula da Bashin ƙasa ta Nijeriya (DMO) ta fitar sun nuna cewa, jihohi 32 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun ƙara tara kusan dala biliyan 1 na sabon bashi na waje a shekarar 2025, duk da ƙarin kuɗaɗen da suke samu daga Asusun Rabon Kuɗin Tarayya (FAAC). Rahoton da jaridar News Point Nigeria ta samu ya nuna cewa jimillar bashin waje na jihohi 36 da Abuja ya tashi daga dala biliyan 4.80 a ƙarshen Disamba 2024 zuwa dala biliyan 5.68 a ƙarshen Disamba 2025. Wannan na nufin ƙarin dala miliyan 884.66, wanda ya…
Read More
Farashin mai ya sauka yayin da Trump ya yi alƙawarin taimaka wa jiragen ruwa a Hormuz

Farashin mai ya sauka yayin da Trump ya yi alƙawarin taimaka wa jiragen ruwa a Hormuz

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Farashin man fetur ya ɗan ragu a ranar Litinin, 4 ga Mayu, 2026, bayan Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasar Amurka za ta fara wani shiri na taimaka wa jiragen ruwa da suka maƙale a Mashigin Hormuz. Rahotanni sun nuna cewa farashin man Brent ya ragu da kashi 0.1 cikin ɗari, inda ya sauka da centi 6 zuwa dala 108.11 kan kowace ganga a lokacin 0400 GMT, bayan ya riga ya ragu da dala 2.23 a ranar Juma’a. Shi kuwa man West Teɗas Intermediate (WTI) na Amurka ya tsaya a dala 101.50 kan…
Read More
Otedola ya ƙaryata zargin tallafa wa matatar Dangote

Otedola ya ƙaryata zargin tallafa wa matatar Dangote

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fitaccen attajirin ɗan kasuwa a Nijeriya, Femi Otedola, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa shi ne ya tallafa wa gina Matatar Man Fetur ta Dangote, yana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya tsagwaronta da aka ƙirƙira a kafafen sada zumunta. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Otedola ya ce waɗanda ke yaɗa irin waɗannan rahotanni na ƙoƙarin jefa ruɗani da kuma haifar da saɓani tsakanin manyan ‘yan kasuwar Nijeriya. Ya ce, “Rahotannin da ke cewa Femi Otedola ne ya ɗauki nauyin gina Matatar Dangote ba gaskiya ba ne ko kaɗan.…
Read More
NNPC ya ƙulla yarjejeniya da kamfanonin Chana domin farfaɗo da matatun Fatakwal da Warri

NNPC ya ƙulla yarjejeniya da kamfanonin Chana domin farfaɗo da matatun Fatakwal da Warri

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC), ya sanar da ƙulla yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da wasu kamfanonin ƙasar Chana guda biyu domin binciko yiwuwar haɗin gwiwa wajen kammala gyare-gyare da kuma gudanar da ayyukan matatun man fetur na Fatakwal da Warri. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar 3 ga Mayu, 2026, wadda Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na kamfanin, Andy Odeh, ya sanya wa hannu. An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Jiaɗing na ƙasar Chana a ranar 30 ga Afrilu, 2026, inda Babban Daraktan Rukunin Kamfanin NNPC,…
Read More
Matashi ya yi barazanar ƙin biyan bashin PalmPay bayan yi masa fallasa

Matashi ya yi barazanar ƙin biyan bashin PalmPay bayan yi masa fallasa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani matashi ɗan Nijeriya ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan ya zargi kamfanin PalmPay da yi masa tsangwama dangane da biyan bashin da ya karɓa. A cikin wani bidiyo da ya bazu a yanar gizo, matashin ya bayyana cewa duk da cewa kamfanin OPay na binsa bashin naira 800,000, abin da suke yi kawai shi ne kiran tunatarwa cikin ladabi, saɓanin PalmPay da ya ce sun fara tuntuɓar mutanen da ke cikin jerin lambobinsa bayan kwanaki kaɗan da bashin ya ƙare. Ya nuna takaicinsa kan abin da ya kira salon karɓar bashi mai tsauri,…
Read More
Hajjin 2026: An shawarci maniyyatan Nijeriya da su gujewa kai miyagun abubuwa ƙasar Saudiyya

Hajjin 2026: An shawarci maniyyatan Nijeriya da su gujewa kai miyagun abubuwa ƙasar Saudiyya

Daga DAUDA USMAN a Legas An shawarci maniyyatan Nijeriya da ke shirin zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali a bana da su nisanci ɗaukar miyagun ƙwayoyi ko wasu haramtattun abubuwa, domin kauce wa shiga matsala a ƙasar Saudiyya. Babban Limamin Masallacin Juma’a na rukunin gidajen Unguwar 1000 a Victoria Island, Legas, Malam Suleman Ibrahim, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Izalatul Bid’a Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS) na Jihar Legas, ne ya bayar da wannan gargaɗi yayin huɗubar Juma’ar makon da ya gabata. A cikin huɗubar tasa, limamin ya jaddada cewa ya zama wajibi ga dukkan maniyyata su zama jakadun…
Read More