11
May
Daga JOHN D WADA a Keffi Wani jami’in tsaro da ke aiki a Princess Sarah Hotel da ke Keffi a jihar Nasarawa da ba a bayyana sunarsa ba an harbe shi da bindiga har lahira yayin wani rashin jituwa da ya auku tsakanin sa da wani soja da ke aiki a baraki na 177 Guards Battalion dake birnin Keffi ƙarƙashin Operation MESA. Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:40 na safe ranar Asabar 2026 lokacin da dakarun sojan dake sintiri na musamman suka cikaro da saɓani tsakanin shi marigayi maigadin otal ɗin da wani mai babur…
