ukarofi

12567 Posts
Sojoji sun kama mutane shida da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a Katsina

Sojoji sun kama mutane shida da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sojoji na rundunar 17 Brigade da haɗin gwiwa na jami'an hukumar NDLEA sun kama mutane shida ɗauke da miyagun ƙwayoyi a wani samame da suka kai a ƙauyen Dawo a ƙaramar hukumar Malumfashi bayan samun bayanai na sirri. Majiya daga hukumar tsaron ya ce a yayin gudanar da samamen, jami'an tsaron sun sami garin tabar wiwi mai nauyin kilogram 82.5 a maɓoyar dillalan ƙwayoyin. Akwai kuma kilogiram 15.7 na Extol 5.1 da kilogiram 8 na D5 duk a maɓoyar ta su. A cewar rundunar sojojin,da zarar sun kammala bincike za su miƙa waɗanda ake zargi…
Read More
Zuwa ga mata da maza: Faɗakarwa kan batun yadda ake yaɗa bidiyon tsiraici a zamanin yau

Zuwa ga mata da maza: Faɗakarwa kan batun yadda ake yaɗa bidiyon tsiraici a zamanin yau

A cikin wannan zamani da fasahar sadarwa ta zama ruwan dare, an shiga wani sabon yanayi da ke haifar da babbar matsala ga tarbiyya da mutuncin al’umma. Abin da a da ake ɓoye shi a cikin sirri da kunya, a yau ya koma ana ɗaukarsa a matsayin abin wasa ko soyayya ta zamani. Musamman yadda wasu ’yan mata ke tura wa samari bidiyon tsiraici, ko kuma hotunan da ba su dace ba, yana daga cikin abubuwan da ke rusa ginin tarbiyyar al’umma cikin gaggawa. Wannan wasiƙa tana da manufar yin kira na musamman ga ’yan mata da maza baki ɗaya,…
Read More
Kamar Neja kamar Filato: Yadda za a magance matsalar tsaro a jihohinmu

Kamar Neja kamar Filato: Yadda za a magance matsalar tsaro a jihohinmu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A yayin da nake wannan rubutu, shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya amince da bayar da gudunmawar Naira Biliyan 2 da za a yi amfani da su wajen tallafawa waɗanda harin Anguwar Rukuba a Jos ya shafa, da ma rikicin da ya biyo baya. Shugaban ƙasa ya bayyana haka ne, a yayin taron masu ruwa da tsaki da ya kira zuwa fadarsa, domin tattauna hanyoyin magance rikicin da ya addabi Jihar Filato tsawon shekaru. Shugaban ƙasa ya shaidawa shugabannin al'umma da suka je ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Caleb Mutfwang, waɗanda suka haɗa da tsofaffin gwamnoni, tsofaffin ministoci,…
Read More
Mun rasa Saleh Shehu Ashaka!

Mun rasa Saleh Shehu Ashaka!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tun musamman ma samun kafafen sadarwa na yanar gizo ya zama kusan duk lokacin da mutum ya shiga yanar zai ga labarin rasuwar wani ko wata da batun shirya jana’iza. Hakanan akwai labarun rashin lafiya da wasu ma labarun masu sanya juyayi da zubar da hawaye. Ranar Lahadi 3 ga watan nan na Oktoba 2026 da misalin ƙarfe 3 na rana sai wayata ta yi ƙara na ɗauka na duba sai na ga mai taimakawa shugaba Tinubu kan harkokin labaru ne Abdul’ziz Abdul’aziz. Da ya ke mun saba yin waya kan harkokin labaru bai ɗauka wani…
Read More
1999 zuwa 2026: Yadda manyan ’yan siyasa ke farfaɗo da ƙananan jam’iyyu

1999 zuwa 2026: Yadda manyan ’yan siyasa ke farfaɗo da ƙananan jam’iyyu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAMD Tun bayan dawowar Nijeriya kan tafarkin mulkin dimukraɗiyyar Nijeriya a shekarar 1999 zuwa sauye-sauyen siyasa da ake gani a 2026, ƙananan jam’iyyun siyasa da ba su da ƙarfi sun riƙa samun karɓuwa, kuɗaɗen shiga da kuma fitowa fili ne ta hanyar shigowar manyan ’yan siyasa da ke sauya sheƙa daga manyan jam’iyyu sakamakon rikice-rikicen cikin gida, rashin nasara a zaɓen fidda gwani ko kuma dabarun sake tsarawa. Duk da cewa Nijeriya na bin tsarin jam’iyyu da dama, gasa ta fi karkata ne ga manyan jam’iyyu irin su PDP, APC da kuma LP. A ƙasa da wannan…
Read More
Gwamnan Katsina ya bada kyautar motoci ga ɗaliban KTISM a Katsina

Gwamnan Katsina ya bada kyautar motoci ga ɗaliban KTISM a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya bada kyautar sabbin mototoci da yayi alƙawarin ga ɗaliban da suka yi ƙwazo a makarantar kimiya ta KTISM da ke Katsina. Gwamnan ya miƙa motocin ga ɗaliban a harabar fadar gwamnatin jihar Katsina. Ɗaliban, Ibrahim Mainasara Bugaje daga sashen Networking and System Security da Aisha Isyaku daga sashen Computer Soft Engineering. Gwamnan jihar Katsina ya bayyana cewa ya godema Allah da ya bashi ikon cika wannan alƙawarin da ya ɗauka ga ɗaliban tare da masu addu"ar Allah yasa abinda suka karanta ya amfani al'umma. Shugaban makarantar Dr. Musa…
Read More
Zulaihatu ta nemi gwamnati ta ƙara zuba jari a harkar noma

Zulaihatu ta nemi gwamnati ta ƙara zuba jari a harkar noma

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Wata ƙwararriya a harkar noma da kasuwanci. Zulaihatu Labilwa Madugu, ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su ƙara zuba jari mai yawa a fannin noma, musamman ta hanyar tallafa wa matasa da filayen noma, kayan aiki, da kuma horo na zamani kan harkar. Zulaihatu ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakilinmu a Gombe, inda ta jaddada cewa noma na daga cikin manyan hanyoyin da za su iya rage matsalar rashin aikin yi, fatara, da kuma ƙarancin abinci a ƙasar nan. Ta ce duk da cewa noma na da wahala, amma…
Read More
APC ta fara tantance ‘yan takarar majalisar dokokin jiha a Zamfara

APC ta fara tantance ‘yan takarar majalisar dokokin jiha a Zamfara

Jam'iyyar APC a Jihar Zamfara ta ƙaddamar da fara tantance yan takarar ta ɓangaren masu neman kujerar majalisar dokokin Jihar a yau Litinin. Tantancewar yana gudana a Hotel din Karma Guest Inn dake Gusau babban nirnin Jihar. Masu neman tsayawa takarar sun halarci tantancewar wanda ake gudanar dashi cikin kwanciyar hankali da tsaro. Wakilin mu ya ruwaito cewar, ana saran a gobe kwamitin tantance yan takarar zai kammala aikin sa. Da aka tuntuɓe shi, kakakin jam'iyyar ta APC Hon. Ibrahim Muhammad Birnin Magaji, ya bayyana tantancewar a matsayin cikin kwanciyar hankali, yana mai nuni da cewar za su bada cikakken…
Read More
Sadiya Umar Farouq: Me ya sa ’yan Nijeriya ba sa farin ciki da farautar ta?

Sadiya Umar Farouq: Me ya sa ’yan Nijeriya ba sa farin ciki da farautar ta?

Daga NASIR S. GWANGWAZO Akasarin ’yan Nijeriya suna da damuwa kan yadda ake wadaƙa da dukiyar ƙasar ba tare da ɗaukar matakan gaske wajen magance matsalar ba, wacce tushenta shine cin hanci da rashawa, wanda ake ganin a matsayin matsalar da ta ƙarya ƙashin-bayan dukkan wani cigaba da bunƙasa a ƙasar. To, amma me ya sa a mafi yawancin lokutan idan gwamnatocin Nijeriya suka fara farautar waɗanda suka riƙe muƙaman gwamnati, kamar Sadiya Umar Farouk, sai ka ga ’yan ƙasar ba su nuna farin ciki da hakan, illa ma sai tir ne ya fi biyo baya?Manyan misalan a nan sune,…
Read More
Soja ya bindige maigadin otel a Keffi

Soja ya bindige maigadin otel a Keffi

Daga JOHN D WADA a Keffi Wani jami’in tsaro da ke aiki a Princess Sarah Hotel da ke Keffi a jihar Nasarawa da ba a bayyana sunarsa ba an harbe shi da bindiga har lahira yayin wani rashin jituwa da ya auku tsakanin sa da wani soja da ke aiki a baraki na 177 Guards Battalion dake birnin Keffi ƙarƙashin Operation MESA. Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:40 na safe ranar Asabar 2026 lokacin da dakarun sojan dake sintiri na musamman suka cikaro da saɓani tsakanin shi marigayi maigadin otal ɗin da wani mai babur…
Read More