ukarofi

12567 Posts
Ba a magance tsaro cikin dare ɗaya – Dikko Raɗɗa

Ba a magance tsaro cikin dare ɗaya – Dikko Raɗɗa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsaro ba a magance shi cikin dare ɗaya, yana buƙatar fahimta mai zurfi da tsarin haɗin gwiwa: Inji-Gwamna Raɗɗa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa a yanzu Jihar Katsina ta zama wani abin koyi na zahiri wajen nazarin yadda ake haɗa kai da al’umma a harkokin tsaro, yana mai cewa zaɓen jihar domin wannan rangadin karatu ba haka kawai aka yi shi ba. Gwamna Raɗɗa ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin mahalarta jwasa-kwasai na manyan hafsoshi na 48 daga Kwalejin Horas da Hafsoshin Sojoji ta Rundunonin Najeriya da…
Read More
Oba Ewuare: Basaraken tagulla na birnin Benin

Oba Ewuare: Basaraken tagulla na birnin Benin

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Benin dai tana ɗaya daga ƙasashen yamma Afrika kuma ita ƙaramar ƙasa ce, da can ana kiranta da Dukome. A shekara ta 1894 ƙasar Faransa ta mamaye ƙasar, zuwa shekara ta 1960 ta samu ’yancin kanta. Benin tana da iyaka da ƙasashe huɗu, su ne, daga gabacinta Nijeriya, daga yammacinta Togo, daga arewacinta Nijar, daga arewa maso yammaci Burkina Faso. Benin ƙasa ce me tsuwo daga kudanci zuwa arewaci (650 )km, kuma tsawanta daga gabarce zuwa yammace ( 110 ) km, harshen Faransanci shi ne yaren ƙasar, tana kuma da yawan mutane kimanin (4,418,000 ). A…
Read More
Muhimman amfanin man jojoba ga fata

Muhimman amfanin man jojoba ga fata

Daga AISHA ASAS  Mai karatu sannunku da sake kasancewa da shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. A makon da ya gabata, mun yi shimfiɗa kan ɗaya dagacikin ababen tsiro masu matuƙar muhimmanci ga lafiyar fata, amma kuma ɓoyayyen abu musamman a ƙasar Hausa, wato man jojoba.  A wannan mako za mu yi duba kan tasirin sa ga fata da kuma yadda za a ribatu da shi. 1. Shayar da fata ruwa tare da daidaita kitse: Jojoba oil na samar da zurfin danshi ba tare da barin fata ta zama mai maiƙo ba. Saboda yana kwaikwayon sebum, wato yana aika saƙo…
Read More
Aure babu bincike: Son rai ko ganganci?

Aure babu bincike: Son rai ko ganganci?

Daga AISHA ASAS  Annabin Rahma (S.A.W) ya ce, "Idan ku ka samu wanda ku ka yarda da halinshi, to ku ba shi aure........." Ta yaya iyaye za ku iya gane halin mutum idan ba ku yi bincike ba? Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyarmu. Fatan Allah ya sa mu amfana da juna. Bincike wani muhimmin abu ne ko ince ɗaya ne daga cikin tubali da ake gina aure kansa, kuma za mu iya amincewa da cewa, dukka malamai sun yi ijtima'i akan yin sa shi ne mafi a'ala akan…
Read More
Gwamnati Katsina ta fara duba yiyuwar gina titin jirgin ƙasa na cikin gari

Gwamnati Katsina ta fara duba yiyuwar gina titin jirgin ƙasa na cikin gari

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta fara duba yiyuwar gina titin jirgin ƙasa na zamani na cikin gari domin inganta harkokin sufuri da bunƙasa ababen more rayuwa na zamani a faɗin jihar. A wani mataki na cimma wannan buri, gwamnatin ta kafa kwamitin ƙwararru da zai nazarci ƙudirin samar da tsarin jirgin kasa na cikin gari (Light Rail), tare da tantance yadda za a aiwatar da aikin. Kwamitin wanda kwamishinan ayyuka na jihar ke jagoranta, ya haɗa wakilai daga muhimman ma’aikatu da hukumomin gwamnati da suka haɗa da ma’aikatar kasafi da tsare-tsare, ofishin sakataren gwamnati (SGS), hukumar…
Read More
Mata da yara da dama sun mutu a Zamfara sakamakon harin sojoji

Mata da yara da dama sun mutu a Zamfara sakamakon harin sojoji

Daga USMAN KAROFI Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa sama da mutum 72 ne ake zargin sun rasa rayukansu bayan wani harin sama da sojoji suka kai ya afkawa kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi a ranar Lahadi. Wasu majiyoyi sun shaida cewa mata da ‘yan kasuwa na daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su yayin da ake ci gaba da tantance adadin waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka jikkata. Wani jagoran al’umma mai suna Garba Ibrahim Mashama ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wasu gawarwakin sun lalace matuƙa har ba za a iya…
Read More
Jam’iyyar APC ta tantance ‘yan takarar majalisar jiha 115 a Zamfara

Jam’iyyar APC ta tantance ‘yan takarar majalisar jiha 115 a Zamfara

Jam'iyyar APC a Jihar Zamfara ta tantance adadin 'yan takarar majalisar dokoki 115 da suka nuna sha'awar tsayawa takara a zaɓen dake tafe a 2027. Kakakin Jam'iyyar a Jihar Hon. Ibrahim Muhammad Birnin Magaji ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala tantance yan takarar a Gusau yau Talata. A cewar sa, hakan ya nuna jam'iyyar tana da 'yan takarar majalisar dokoki 115 da suke neman kujera 24 dake a majalisar dokokin jihar. Ya bayyana cewar akwai ƙarin waɗanda har yanzu basu samu halartar tantancewar ba duk da sun sayi form na tsayawa takarar majalisar dokoki a ƙarƙashin Jam'iyyar. Yana mai…
Read More
Sai tubabbun ‘yan boko haram sun rantse da Qur’ani kafin maida su cikin al’umma – Gwamnatin Borno

Sai tubabbun ‘yan boko haram sun rantse da Qur’ani kafin maida su cikin al’umma – Gwamnatin Borno

Daga USMAN KAROFI Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa tsofaffin ‘yan ta’addan da suke cikin shirin gyaran hali da sake mayar da su cikin al’umma ana sanya su yin rantsuwa da Alkur’ani mai girma kafin a kammala shirin nasu. Gwamnatin ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin hana su komawa ayyukan ta’addanci bayan an sake su cikin al’umma. Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar, Zuwaira Gambo, ita ce ta bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na News Central. Ta ce yin rantsuwar da Alkur’ani shi ne mataki na ƙarshe…
Read More
Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu kan mutuwar ɗan tsohon takarar majalisar tarayya a hannun ‘yan bindiga

Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu kan mutuwar ɗan tsohon takarar majalisar tarayya a hannun ‘yan bindiga

Daga USMAN KAROFI Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna matuƙar baƙin ciki da fushi kan rasuwar tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Hon. Abba Anas Adamu, wanda aka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 3 ga Mayu, 2026. Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne bayan kwanaki tara yana hannun ‘yan bindiga duk da ƙoƙarin da iyalansa suka yi na ganin an kuɓutar da shi. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce mutuwar tsohon ɗan majalisar wata babbar shaida ce ta taɓarɓarewar…
Read More
Sace ɗaliban NSUK: ‘Yan sanda sun kama mutum biyu

Sace ɗaliban NSUK: ‘Yan sanda sun kama mutum biyu

Daga JOHN D WADA a Lafia Hedikwatar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa ta sanar wa jama'a samun wani babban nasara a binciken da ta ke gudanarwa a kan sace ɗaliban fannin karatun Injiniya na babbar jami’ar jihar da ke Gudi inda a yanzu haka tace ta cafke mutum biyu cikin waɗanda ake zargi da aikata ɗanyen aikin tare da ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya. Idan ba a manta ba a 'yan kwanakin nan ne jaridar Manhaja ta ruwaito labarin wasu miyagun mutane 'yan bindiga waɗanda suka kai hari fannin karatun Injiniya da ke garin Gudi a ƙaramar hukumar Akwanga inda…
Read More