15
May
A daidai lokacin da matsalar yunwa da ƙarancin abinci ke ƙara addabar miliyoyin ’yan Nijeriya, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sake fito da wani sabon shiri da take ganin zai taimaka wajen magance matsalar tamowa da rashin wadataccen abinci a ƙasar nan. Wannan mataki ya zo ne bayan Majalisar ƙasa Kan Samar da Abinci Mai Gina Jiki ta amince da sabuwar Dokar Manufofin Abinci da Gina Jiki ta ƙasa (2026–2035), wadda ake sa ran za ta zama tubalin da za a dogara da shi wajen bunƙasa wadatar abinci da inganta lafiyar al’umma a Nijeriya. A zahiri, wannan mataki ya…
