ukarofi

12565 Posts
ACI: Rikicin ACF abin kunya ne ga Arewa

ACI: Rikicin ACF abin kunya ne ga Arewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar haɗin kan arewacin Nijeriya da zaman lafiya da bunƙasa, wato Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative (ACI) ta nuna rashin jin daɗinta kan rikicin shugabanci da ke addabar ƙungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), tana mai bayyana lamarin a matsayin abin kunya da ya jefa Arewacin Nijeriya cikin ba’a da raini a idon jama’a. A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na ƙungiyar, Dr. Abdullahi Idris, ya aikewa da manema labarai, ACI ta bayyana damuwarta kan yadda rikice-rikice, zarge-zarge da rarrabuwar kai suka yi ƙamari a cikin ACF. Kungiyar ta ce rikicin…
Read More
Taron ƙasashen Afirka da Faransa: Tinubu ya buƙaci a yi adalci wajen hada-hadar kuɗi na duniya

Taron ƙasashen Afirka da Faransa: Tinubu ya buƙaci a yi adalci wajen hada-hadar kuɗi na duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa Bola Tinubu a ranar Talata ya jagoranci tawaga zuwa taron ƙasashen Afirka da ƙasar Faransa (Africa Forward Summit) wanda aka yi a babban ɗakin taro da ke Nairobi a ƙasar Kenya. Shugaba Tinubu ya nemi a yi sauye-sauye ta fuskar tsarin hada-hadar kuɗi ta duniyar da ƙarfafa tattalin arziƙin Afirka ta hanyar mai da hankali ga bunƙasar masana’antu da yalwar arziƙi. Taron ƙasashen Afirka da Faransa an gudanar da shi ne bisa jagorancin Emmanuel Macron da William Ruto da kuma ya ƙunshi shugabannin ƙasashe sama da 30. Antonio Guterres, shugaban majalisar ɗinkin…
Read More
Hajjin 2026: Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta ba asibitocin NAHCON lasisin aiki

Hajjin 2026: Ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta ba asibitocin NAHCON lasisin aiki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), ta samu amincewa da lasisin gudanar da ayyukan lafiya daga Ma’aikatar Lafiya ta Masarautar Saudiyya domin cibiyoyin lafiya da wuraren bayar da kulawar jinya da ta kafa domin kula da alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin shekarar 2026. Rahoton ya bayyana cewa samun wannan lasisi ya bai wa tawagogin lafiya na hukumar damar fara gudanar da ayyukan kula da lafiya ga maniyyatan Nijeriya da ke ƙasar Saudiyya. A matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen kiwon lafiyar alhazai, NAHCON ta tanadi asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya a wurare daban-daban domin samar da…
Read More
‘Yan Nijeriya za su nuna wa ‘yan siyasa turjiya a zaɓen 2027 — Makinde

‘Yan Nijeriya za su nuna wa ‘yan siyasa turjiya a zaɓen 2027 — Makinde

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa tasirin gwamnatin tarayya ba zai iya sauya sakamakon zaɓen 2027 ba, yana mai cewa ‘yan Nijeriya za su fito su zaɓi shugabannin da suke so ba tare da tsoron tasirin siyasa ba. Makinde ya bayyana hakan ne a yayin taron bunƙasa yawon buɗe ido na jihar Oyo da aka gudanar a cibiyar taruka ta jami’ar Ibadan, inda ya ce al’umma ba za su ci gaba da zama masu kallo kawai ba a siyasa. Ya kuma ce gwamnatinsa ta kafa tsare-tsare masu ɗorewa da za su tabbatar…
Read More
Ana lalata jiragen ƙasa ta hanyar jifar su a hanyar Abuja zuwa Kaduna – NRC

Ana lalata jiragen ƙasa ta hanyar jifar su a hanyar Abuja zuwa Kaduna – NRC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Daraktan Hukumar Kula da Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), Dakta Kayode Opeifa, ya nuna matuƙar damuwa kan yawaitar lalata kayayyakin layin dogo da kuma jifan jiragen ƙasa da duwatsu a hanyar Abuja zuwa Kaduna. A cikin wani rubutu mai taken “Kare Layin Dogo, Kare Makomar Mu”, Dakta Opeifa ya bayyana cewa wasu ɓata-gari da ke fakewa a al’ummomin da ke kusa da layin dogo na kai hare-hare kan jiragen ƙasa yayin da suke tafiya, inda suke fasa tagogi tare da lalata gilashin gaba na wani jirgi da ke ɗauke da fasinjoji marasa laifi. Ya bayyana…
Read More
Ficewar Obi da Kwankwaso ya sa jam’iyyarmu ta zauna lafiya – ADC

Ficewar Obi da Kwankwaso ya sa jam’iyyarmu ta zauna lafiya – ADC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa jam’iyyar ta samu zaman lafiya bayan ficewar manyan ‘yan siyasa ciki har da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso. Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce duk da cewa ficewar jagororin biyu ta ba su mamaki, jam’iyyar ta wuce wannan mataki kuma tana ci gaba da kokarin gina hadakar jam’iyyun adawa domin kalubalantar gwamnatin APC. Ya ce ADC na ganin cewa hadin kan jam’iyyun adawa ne kadai zai iya ba su damar kayar…
Read More
Wani mahaifi ya koka bayan harin jirgin sama ya kashe ’ya’yansa uku a Neja

Wani mahaifi ya koka bayan harin jirgin sama ya kashe ’ya’yansa uku a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wani mazaunin jihar Neja mai suna Victor Solomon ya bayyana alhini da kuka bayan da ya ce ya rasa ‘ya’yansa uku sakamakon harin jirgin saman soji da aka kai domin kai farmaki kan ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar. Rahotanni sun bayyana cewa harin saman, wanda aka ce an kai shi kan maboyar ‘yan bindiga a yankin, ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama ciki har da ‘ya’yan Solomon. Majiyoyi da dama a jihar sun tabbatar wa manema labarai cewa sama da mutane goma ne suka rasa rayukansu sakamakon harin. Victor…
Read More
Kungiyoyi sun gudanar da taron goyon baya da yaba wa Dakta Danjuma

Kungiyoyi sun gudanar da taron goyon baya da yaba wa Dakta Danjuma

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Kungiyoyi sama da ashirin ne suka gudanar da wani gagarumin taron nuna goyon baya da yabawa ga Sakataren Musamman na Gwamnan Jihar Kano, Dr. Sani ɗanjuma, bisa yadda yake tallafawa al’umma ta fannoni daban-daban na rayuwa. An gudanar da taron ne a yankin Danladi Nasidi da ke garin Mariri a ƙaramar Hukumar Kumbotso a ranar Asabar da ta gabata. Da yake zantawa da manema labarai, ɗaya daga cikin jagororin tafiyar, Alhaji Sunusi M. Yola, ya ce ƙungiyoyi sama da ashirin ne suka haɗu domin nuna farin cikinsu kan yadda Dr. Sani ɗanjuma ke tallafawa…
Read More
Manufofin Tinubu kan tsaron abinci da sabuwar Dokar Samar da Abinci ta 2026

Manufofin Tinubu kan tsaron abinci da sabuwar Dokar Samar da Abinci ta 2026

A daidai lokacin da matsalar yunwa da ƙarancin abinci ke ƙara addabar miliyoyin ’yan Nijeriya, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sake fito da wani sabon shiri da take ganin zai taimaka wajen magance matsalar tamowa da rashin wadataccen abinci a ƙasar nan. Wannan mataki ya zo ne bayan Majalisar ƙasa Kan Samar da Abinci Mai Gina Jiki ta amince da sabuwar Dokar Manufofin Abinci da Gina Jiki ta ƙasa (2026–2035), wadda ake sa ran za ta zama tubalin da za a dogara da shi wajen bunƙasa wadatar abinci da inganta lafiyar al’umma a Nijeriya. A zahiri, wannan mataki ya…
Read More
An yaba wa Dikko Raɗɗa kan cigaba da biyan giratuti ga ma’aikatan ƙananan hukumomi a Katsina

An yaba wa Dikko Raɗɗa kan cigaba da biyan giratuti ga ma’aikatan ƙananan hukumomi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An yaba wa Gwamnan Katsina Malam Dikko Raɗɗa kan cigaba da biyan giratuti ga ma'aikatan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar Katsina. Tsohon shugabana ƙungiyar ma'aikatan lafiya ta ƙasa reshen jihar Katsina kwamred Mannir Suleiman yayi wannan yabo a hira da manema labarai a Katsina. Ya ce wannan ƙoƙari da Gwamnan yayi ya nuna tausayawa da ƙauna da yake wa ma'aikatan gwamnatin jihar baki ɗaya. Kwamred Suleiman Wanda shine shugaban ƙungiyar cigaban Funtua ya bayyana cewa yanzu haka tsaffin ma'aikatan ƙananan hukumomi na cike da farin ciki da annashuwa domin wannan mataki zai taimaka masu…
Read More