ukarofi

12565 Posts
Matuƙan jirgi sun yi gargaɗi kan ƙarancin mai a Nijeriya

Matuƙan jirgi sun yi gargaɗi kan ƙarancin mai a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Matuƙan Jiragen Sama da Injiniyoyi ta ƙasa (NAAPE), ta yi gargaɗin cewa ƙarancin man jiragen sama da aka fi sani da Jet A1 na barazana ga tsaron zirga-zirgar jirage, ɗorewar kamfanonin sufurin jiragen sama da kuma zaman lafiyar ma’aikata a harkar sufurin jiragen sama a Nijeriya. A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Kyaftin Bunmi Gindeh, ya fitar a Abuja ranar Lahadi, ya bayyana lamarin a matsayin matsala mai matuƙar muhimmanci da ke buƙatar gaggawar shiga tsakani daga gwamnatin tarayya. Gindeh ya yi gargaɗin cewa gajiyawar da ma’aikatan jirage ke fuskanta sakamakon jinkiri da tangarɗar zirga-zirgar…
Read More
Sojoji sun ceto mata da yara shida daga hannun Boko Haram a Borno

Sojoji sun ceto mata da yara shida daga hannun Boko Haram a Borno

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta soji a Arewa maso Gabas, wato Operation HADIN KAI, sun sanar da ci gaba da samun nasarori a hare-haren da suke kai wa ’yan ta’adda ƙarƙashin atisayen Operation DESERT SANITY, inda suka ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su tare da kama waɗanda ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a ranar 13 ga Mayu, 2026, ya bayyana cewa dakarun sun samu nasarar ceto mata da yara shida da aka sace bayan wani samame…
Read More
ADC ta yi alhinin rasuwar Hon. Abba Anas

ADC ta yi alhinin rasuwar Hon. Abba Anas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jam’iyyar ADC ta bayyana alhininta kan rasuwar tsohon ɗan Majalisar Wakilai daga Jihar Jigawa, Alhaji Abba Anas Adamu, wanda aka kashe bayan sace shi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ranar Laraba, ta ce rasuwar marigayin ta girgiza ta matuƙa, tana mai bayyana shi a matsayin jajirtaccen bawan jama’a mai tawali’u, gaskiya da kishin siyasar ƙasa. Marigayi Abba Anas Adamu ya wakilci mazaɓar tarayya ta Birniwa/Guri/Kirikasamma a Majalisar Wakilai ta Tarayya tsakanin shekarun 2007 zuwa 2011. Jam’iyyar ta bayyana cewa marigayin ya kasance mutum mai natsuwa da sauƙin…
Read More
2027: Idan mafaɗin magana wawa ne -Gwamnati ta yi wa Obi shaguɓe kan alƙawarinsa na yin wa’adi ɗaya

2027: Idan mafaɗin magana wawa ne -Gwamnati ta yi wa Obi shaguɓe kan alƙawarinsa na yin wa’adi ɗaya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da Fadar Shugaban ƙasa sun shiga cacar baki kan furucin da ya yi cewa zai yi wa’adi guda ɗaya kacal idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a shekarar 2027. Rahotanni sun bayyana cewa Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na News Central, inda ya ce ko da an ɗora masa bindiga a kai ba zai zauna kan mulki fiye da shekara huɗu ba. “Ina son zama shugaban ƙasa mai wa’adi ɗaya ne saboda samar da daidaito da…
Read More
Hajjin 2026: Nuru Khalid ya buƙaci maniyyatan Nijeriya su yi haƙuri da jigilar NAHCON a Makkah

Hajjin 2026: Nuru Khalid ya buƙaci maniyyatan Nijeriya su yi haƙuri da jigilar NAHCON a Makkah

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Nuru Khalid, ya buƙaci maniyyatan Nijeriya da su ƙara haƙuri tare da nuna fahimta ga hukumomin aikin Hajji yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da jin dazinsu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya. Sheikh Khalid ya yi wannan kira ne ranar Alhamis yayin da yake yi wa maniyyata daga Babban Birnin Tarayya Abuja da Jihar Oyo jawabi bayan isowarsu Makkah daga Madinah. Malamin ya bayyana cewa gudanar da ibadar Hajji, musamman a lokacin sanya harami, na buƙatar juriya da haƙuri sosai daga mahajjata. Ya ce akwai buƙatar sauyin hali…
Read More
Lakurawa sun kashe jami’an Kwastom biyu a Kebbi – Shugaban hukumar

Lakurawa sun kashe jami’an Kwastom biyu a Kebbi – Shugaban hukumar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS), Bashir Adeniyi, ya tabbatar da cewa wasu ‘yan ta’addan Lakurawa sun kashe jami’an hukumar guda biyu a jihar Kebbi. Adeniyi ya bayyana hakan ne ranar Laraba a birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara, inda ya ce jami’an sun rasa rayukansu ne yayin da suke ƙoƙarin daƙile hare-haren ‘yan ta’addan da misalin ƙarfe 3 na dare. Ya bayyana sunayen jami’an da suka rasu da ASC Bamigboye da DSC Dom. Babban jami’in na Kwastam ya bayyana hakan ne yayin gabatar da muƙalar buɗe taro a taron ƙasa…
Read More
Yadda jami’in banki ya tona mu’amalar asusun Malami ga NFIU

Yadda jami’in banki ya tona mu’amalar asusun Malami ga NFIU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wani jami’in kula da bin ƙa’idoji na Bankin Zenith Plc, Mashelia Bata, ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa bankin ya kai rahoton wata mu’amala da ake zargi zuwa Hukumar Bayanan Sirrin Kuɗaɗe ta Nijeriya (NFIU) dangane da wasu kuɗaɗe da suka shiga wani asusun da ake alaƙantawa da tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami. Jami’in ya bayyana hakan ne yayin shari’ar da ake yi wa Malami tare da matarsa da ɗansa kan zargin halasta kuɗaɗen haram da suka kai naira biliyan 8.7. Ana tuhumar waɗanda ake ƙara…
Read More
WhatsApp ta magantu kan yadda waɗanda ba su da lambar masu manhajar ke iya duba ‘status’

WhatsApp ta magantu kan yadda waɗanda ba su da lambar masu manhajar ke iya duba ‘status’

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin WhatsApp ya mayar da martani bayan wasu masu amfani da manhajar sun koka a kafafen sada zumunta cewa lambobin waya da ba su ajiye a cikin wayoyinsu suna iya ganin Status ɗinsu, lamarin da ya sake tayar da muhawara kan tsaron sirri a dandalin. Masu amfani da dama sun bayyana damuwa a shafin ɗ, inda suka ce lamarin ya ba su mamaki tare da jefa su cikin rashin jin daɗi, suna tambayar ko sabuwar matsala ce ta saituna ko kuma wata tangarɗa ce ta fasaha. Wasu daga cikin masu amfani da shafin sun nuna damuwa…
Read More
2027: Gwamna Makinde ya ayyana tsaya wa takarar Shugaban ƙasa

2027: Gwamna Makinde ya ayyana tsaya wa takarar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban ƙasar Nijeriya a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa ƙasar na buƙatar gaggawar sake fasalin siyasa da tattalin arziki. Makinde ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wani gagarumin gangami da aka gudanar a Ibadan domin ƙaddamar da haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyar PDP da jam’iyyar Allied Peoples’ Movement (APM). Ya ce matsalolin da Nijeriya ke fuskanta na buƙatar ƙarin shiga da jama’a za su yi cikin harkokin mulki, tare da haɗin kai mai ƙarfi tsakanin jam’iyyun adawa. Gwamnan ya buƙaci ‘yan Nijeriya…
Read More
Zamfara: Jirgi ya kai hari ne bayan isowar ’yan bindiga kasuwar Tumfa – Shaidu

Zamfara: Jirgi ya kai hari ne bayan isowar ’yan bindiga kasuwar Tumfa – Shaidu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da ce-ce-ku-ce ke ci gaba da ƙaruwa kan harin saman da ya halaka mutane da dama a kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, wani mazaunin yankin ya bayyana cewa jirgin yaƙin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ya kai harin ne jim kaɗan bayan isowar ’yan bindiga kasuwar. ƙauyen Tumfa, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, yanki ne da tattalin arzikinsa ya dogara da noma da kasuwanci. Kasuwar yankin na karɓar baƙuncin ‘yan kasuwa daga Nijar da kuma jihohin Zamfara da Katsina, musamman daga Shinkafi da Jibiya. Majiyoyin yankin…
Read More