ukarofi

12565 Posts
SERAP ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin zargin ɓata sunan DSS

SERAP ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin zargin ɓata sunan DSS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar SERAP mai rajin kare haƙƙin jama’a da yaƙi da cin hanci ta bayyana cewa ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 5 ga Mayu, 2026, wanda ya umarce ta da biyan diyyar naira miliyan 100 ga wasu jami’an Hukumar Tsaro ta DSS bisa zargin bata suna. Tun farko dai SERAP ta bayyana hukuncin a matsayin “kuskure da rashin adalci.” Shari’ar mai lamba Cɓ/4547/2024 jami’an DSS biyu ne, Sarah John da Gabriel Ogundele, suka shigar. Sai dai SERAP ta bayyana cewa babban lauyanta, Tayo Oyetibo…
Read More
Wata mata ta cinna wa mijinta da amayarsa da ’ya’ya biyu wuta

Wata mata ta cinna wa mijinta da amayarsa da ’ya’ya biyu wuta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata matar aure mai shekara 28 mai suna Firdausi Musa tare da ’ya’yanta biyu ƙanana sun samu munanan ƙonewa, a yayin da ake zargin kishiyarta, Maryam Muhammad, ta zuba musu fetur tare da banka musu wuta a unguwar Hotoro da ke Jihar Kano. Faruwar wannan lamari a daren Litinin a yankin Mai Allo da ke unguwar Hotoro, ya jefa mazauna yankin cikin firgici, yayin da ake tsare da wacce ake zargin a ofishin ’yan sanda na Mariri. ƙananan yaran da suka ƙone sun haɗa da Khadija Ya’u mai shekara 7 da Isma’il Ya’u mai…
Read More
Mahara sun kashe mutane biyar, sun yi awon gaba da shanu a Kano

Mahara sun kashe mutane biyar, sun yi awon gaba da shanu a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 5 a ranar Litinin a garin Yankamaye da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na dare a lokacin da maharan suka shigo daga jihar Katsina tare da dirar wa ƙauyen. Mazauna garin sun ce ‘yan bindigar sun yi harbin kan mai uwa dawabi wanda ya jefa al’umma cikin tsoro da kuma mutuwar wasu da dama. Baya ga kashe al’umma, ‘yan bindigar sun sace shanu. Sunusi Abubakar, shi ne mai garin Yankamaye, kuma ya tabbatar wa da PREMIUM TIMES faruwar…
Read More
Majalisar Dattawa ta amince da sabbin ƙa’idoji kan rantsar da sanatoci da zaɓen shugabanni gabanin 2027

Majalisar Dattawa ta amince da sabbin ƙa’idoji kan rantsar da sanatoci da zaɓen shugabanni gabanin 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da wasu sabbin ka’idoji da suka shafi rantsar da sanatoci da kuma zaɓen shugabannin majalisar gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Majalisar ta cimma matsayar ne a zamanta na ranar Litinin, 11 ga Mayu, 2026. Daga cikin sabbin matakan da aka amince da su akwai cewa duk wani Sanata-zaɓaɓɓe da bai samu damar yin rantsuwar kama aiki da rantsuwar zama ɗan majalisa a ranar farko ta zaman majalisar ba, zai iya yin rantsuwar a duk wani zama na gaba ta hannun Shugaban Majalisar Dattawa. Majalisar ta kuma bayyana cewa idan…
Read More
Dole Afrika ta sarrafa albarkatunta domin yin gogayya a kasuwannin duniya – Tinubu

Dole Afrika ta sarrafa albarkatunta domin yin gogayya a kasuwannin duniya – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƙasashen Afrika da su ƙara haɗa kai ta fuskar tattalin arziki tare da ɗaukar manufofin da za su bunƙasa masana’antu da ci gaban nahiyar. Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taron Africa Forward Summit da aka gudanar a cibiyar taro ta Kenyatta da ke Nairobi, ƙasar Kenya, inda ya jagoranci tawagar Nijeriya ta gwamnati, jakadanci da masu zaman kansu. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana cewa tattalin arzikin teku na Nijeriya na da matuƙar…
Read More
2027: Ayala ya fice daga APC zuwa PDP bisa zargin nuna wariya

2027: Ayala ya fice daga APC zuwa PDP bisa zargin nuna wariya

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Gombe mai wakiltar Billiri ta Gabas, Hon. Rambi Ibrahim Ayala, ya bayyana cewa rashin adalci da nuna wariya ga tsofaffin mambobi ne suka sa ya bar jam’iyyar APC ya koma PDP. Ayala, wanda yanzu ke neman takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Balanga/Billiri a ƙarƙashin PDP, ya bayyana haka ne bayan kammala tantance shi a sakatariyar jam’iyyar da ke Gombe. Ya ce tsarin sulhun da APC ta gudanar kwanan nan ya nuna ƙarara cewa jam’iyyar ta fifita sababbin shiga fiye da mutanen da suka daɗe suna aiki domin…
Read More
Gwamnatin Nasarawa ta kammala shirin zaɓen fitar da gwanin APC

Gwamnatin Nasarawa ta kammala shirin zaɓen fitar da gwanin APC

Daga JOHN D WADA a Lafia Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya sanar da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyya APC mai ci a jihar domin kujerun majalisar wakilai na tarayya wanda aka shirya za a gudanar a ranar Juma’a15 ga Mayu na shekarar 2026 da ake ciki a jihar. Gwamna Sule ya bayyana hakan ne yayin da yake wa manema labarai jawabi a sakatariyar ƙungiyar manema labarai ta ƙasa (NUJ) reshen jihar da ke Lafia babban birnin jihar. An wakilce gwamnan a taron ta hannun mataimakin sa na musamman kan harkokin hulɗa…
Read More
Ƙungiyar da’awa ta tallafa wa marayu da zawarawa sama da 2,000

Ƙungiyar da’awa ta tallafa wa marayu da zawarawa sama da 2,000

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Gombe Ƙungiyar da’awa da agaji ta Jihar Gombe ta bayyana cewa ta tallafawa sama da marayu da zawarawa 2,000 da aka yi wa rajista, tare da yin kira ga masu hannu da shuni, hukumomin gwamnati da sauran masu faɗa a ji da su taimaka wajen ci gaba da faɗaɗa shirye-shiryenta na jin ƙai. Shugaban ƙungiyar, Dakta Muhammad Lawan ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar ƙungiyar da ke Gombe. Dakta Lawan ya ce ƙungiyar na ci gaba da jajircewa wajen yaɗa addini da gudanar da ayyukan jin ƙai,…
Read More
Dalilina na rubuta tarihin yaƙin basasar Nijeriya – Gowon

Dalilina na rubuta tarihin yaƙin basasar Nijeriya – Gowon

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya bayyana cewa sabon littafin tarihin rayuwarsa da ya fitar an rubuta shi ne domin fayyace manufofi da matakan da gwamnatinsa ta ɗauka a lokacin Yaƙin Basasar Nijeriya, ba domin tayar da tsoffin raɗaɗin yaƙin ba. Rahoton da aka wallafa ya nuna cewa Gowon ya bayyana hakan ne gabanin ƙaddamar da littafin nasa mai shafuka 881, wanda za a yi a ranar 19 ga watan Mayun 2026 a Cibiyar Taro ta ƙasa da Aasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja. A cewar sanarwar da kamfanin Havilah…
Read More
CBN ya tilasta bankuna wallafa asusun da aka yi shekaru 10 ba a yi hulɗa da su ba

CBN ya tilasta bankuna wallafa asusun da aka yi shekaru 10 ba a yi hulɗa da su ba

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu manyan bankunan Nijeriya huɗu sun wallafa bayanan asusun ajiyar kuɗi 321,181 da suka daɗe ba tare da an yi hulɗa da su ba, domin bin umarnin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayar, lamarin da ya jawo muhawara kan yadda ake sanar da kwastomomi, kare sirrin bayanai da kuma sake ɗaga irin waɗannan asusu. Bankunan da suka fitar da jerin sun haɗa da Access, Union, Stanbic IBTC da Fidelity, bayan sabon tsarin da CBN ya fitar a watan Yulin 2024 wanda ya umarci bankuna su wallafa bayanan asusun da suka yi sama da shekara 10…
Read More