ukarofi

12565 Posts
Sojoji sun yi kuskuren kashe fararen hula 13 a Neja

Sojoji sun yi kuskuren kashe fararen hula 13 a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wasu hare-haren sama da rundunar sojin saman Nijeriya ta kai a ƙarshen mako a Jihar Neja sun yi sanadin mutuwar fararen hula 13, kamar yadda majiyoyin yankin suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, yayin da sojoji suka ce harin ya kashe ’yan bindiga sama da 70. An kai hare-haren ne a ƙaramar hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, yankin da kwanakin nan ya zama mafakar wasu mayaƙan Boko Haram da kuma ƙungiyoyin ’yan bindiga masu kai hare-hare kan ƙauyuka da ƙaƙaba haraji a wuraren da gwamnati ba ta da cikakken iko. Sai…
Read More
’Yan siyasa su kula da sha’anin marayu da masu buƙata ta musamman – Sani Kuɗai

’Yan siyasa su kula da sha’anin marayu da masu buƙata ta musamman – Sani Kuɗai

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA An buƙaci attajirai da ’yan siyasa masu jagorantar al’umma a matakai daban-daban da su ƙara mayar da hankali wajen tallafa wa marayu, marasa galihu da masu buƙata ta musamman domin rage musu raɗaɗin rayuwa da kuma inganta walwalarsu. Shugaban Gidauniyar Kowa Ya Ga Girman Na Gaba APC Youth Forum reshen Jihar Jigawa, Alhaji Sani Abdullahi Kuɗai, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya haɗa masu ruwa da tsaki da ’yan siyasa daga ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa. A cikin jawabin nasa, Alhaji Sani Abdullahi Kuɗai ya jaddada muhimmancin amfani da ribar dimokuraɗiyya…
Read More
Inganta harkar ilimi na daga cikin manufofin Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Jahun — Abdullahi Abubakar

Inganta harkar ilimi na daga cikin manufofin Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Jahun — Abdullahi Abubakar

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano Shugaban Kwalejin Nazarin Harkokin Lafiya, Kimiyya da Fasaha ta Jahun da ke Jihar Jigawa, Malam Abdullahi Abubakar, ya bayyana cewa inganta harkar koyo da koyarwa na daga cikin manyan manufofin kwalejin domin samar da ƙwararrun jami’an lafiya da za su taimaka wajen bunƙasa harkar kiwon lafiya a ƙasa. Malam Abdullahi Abubakar ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa, inda ya ce bayar da cikakken goyon baya ga ilimin yara mata musamman a fannin lafiya na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantattun ma’aikatan lafiya da za su kula da…
Read More
Masalahar fidda ɗan takarar Gwamnan Gombe zalunci ne — Pantami

Masalahar fidda ɗan takarar Gwamnan Gombe zalunci ne — Pantami

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Aliyu Isa Pantami, ya bayyana cewa tsarin da aka bi wajen tsaida ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC ta hanyar maslaha bai bi ka’idojin doka da adalci ba. Pantami, wanda ke neman takarar gwamnan jihar Gombe, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai bayan ayyana Alhaji Jamilu Isyaku Gwamna a matsayin ɗan takarar APC na zaɓen 2027. Ya ce tsarin maslaha ko “consensus” yana da ka’idoji guda uku da dole sai an bi kafin a ce an yi sahihin tsaida ɗan takara.…
Read More
2027: Matasan Arewacin Nasarawa sun bayyana goyon bayansu ga Dakta Silas Agara

2027: Matasan Arewacin Nasarawa sun bayyana goyon bayansu ga Dakta Silas Agara

Daga JOHN D WADA a Keffi Shugabannin matasa a yankin mazaɓun sanatan Arewacin jihar Nasarawa sun bayyana goyon bayansu na musamman ga ɗan takarar kujerar sanata a 'yankin wato Dr. Silas Ali Agara a zaɓen kujerar sanatan don saka masa da alherin tallafawa matasa da cigaban al’umma da suka ce ya daɗe yana yi. Shugabannin sun bayyana haka ne ranar Juma'a 15 ga Mayu 2026 bayan wani taron masu ruwa da tsaki na shugabannin matasan ƙabilu daban-daban da wakilan matasa daga ƙauyuka da ƙananan hukumomi a faɗin yankin wanda aka gudanar a otel din Esslah Guest House a Akwanga. A…
Read More
Ronaldo ya kafa tarihi bayan zura wa kowace ƙungiya a Saudi League ƙwallo

Ronaldo ya kafa tarihi bayan zura wa kowace ƙungiya a Saudi League ƙwallo

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya sake kafa wani sabon tarihi a duniya bayan jagorantar ƙungiyarsa ta Al-Nassr zuwa gagarumar nasarar 4-2 a kan Al-Shabab. Ronaldo ya cimma wannan bajinta ne bayan ya zura wa dukkan ƙungiyoyin da ya kara da su a gasar Saudi Pro League ta bana ƙwallo, abin da ya ƙara tabbatar da matsayinsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasa mafiya tarihi a duniyar tamaula. Kafin wasan, Al-Shabab ita ce kaɗai ƙungiyar da Ronaldo bai samu damar zura wa ƙwallo ba a kakar 2025/2026. Sai dai tauraron ɗan wasan ya…
Read More
Dalilin da muka hana Obi da Kwankwaso tikitin takara — PRP

Dalilin da muka hana Obi da Kwankwaso tikitin takara — PRP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban jam’iyyar PRP, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana dalilin da ya sa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ba su shiga jamiyyar ba a yayin da Zaɓen 2027 ya gabato. Ya ce tattaunawar da aka yi da su ta rushe ne bayan sun buƙaci a ba su tikitin takarar shugaban ƙasa kai tsaye ba tare da an yi zaɓen fidda-gwani ba a jam’iyyar. Da yake magana a shirin siyasa na Hausa a DITɓ Kaduna, Baba-Ahmed ya ce PRP ta ƙi amincewa da hakan, tana…
Read More
Dumamar yanayi: Babura masu ƙafa uku za su koma amfani da batir mai caji

Dumamar yanayi: Babura masu ƙafa uku za su koma amfani da batir mai caji

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Matsalar ɗumamar yanayi na daga cikin manyan matsalolin da ke damun duniya baki ɗaya, musamman yadda hayaƙin ababen hawa da masana’antu ke gurɓata muhalli. Domin magance wannan matsala, wani kamfani mai suna Carbon Asset Nigerian Limited tare da haɗin gwiwar wata ƙungiya daga ƙasar Ingila mai suna Partnership for Agile Goɓernance and Climate Engagement sun ƙaddamar da wani shiri na mayar da babura masu ƙafa uku zuwa masu amfani da batir mai caji maimakon fetur ko gas. Shugaban kamfanin a Jihar Kano, Mukhtar Abdulhamid, ya bayyana cewa shirin haɗin gwiwa ne da zai taimaka…
Read More
An ƙaddamar da shugabancin kasuwar ‘yan shinkafa ta Kwanar Dawaki

An ƙaddamar da shugabancin kasuwar ‘yan shinkafa ta Kwanar Dawaki

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano An ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar masu sayar da shinkafa da sarrafa ta a Kasuwar Kwanar Dawaki da ke Kano. Da yake jawabi bayan ƙaddamar da su, sabon shugaban ƙungiyar, Alhaji Sham’unu Nasiru Saminu, ya gode wa Allah bisa nasarar da suka samu tare da kira ga ‘yan kasuwar da su ba su cikakken goyon baya. Ya ce tun bayan zaɓensu ne aka ba su shaidar kama aiki, tare da kira ga gwamnati da ta riƙa tallafawa ‘yan kasuwa domin bunƙasa harkokin kasuwanci. Sham’unu ya bayyana cewa tun kafa kasuwar shekaru 23 da suka…
Read More
Gwamnatin Kano ta kashe fiye da Naira biliyan huɗu wajen biyan kuɗin jarrabawar NECO

Gwamnatin Kano ta kashe fiye da Naira biliyan huɗu wajen biyan kuɗin jarrabawar NECO

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ta kashe fiye da Naira biliyan huɗu wajen biyan kuɗin jarabawar NECO ga ɗalibai a cikin shekaru biyu da suka gabata. Daraktar Hukumar Shirya Jarrabawa da Kula da Ayyukan Koyo da Koyarwa ta Jihar Kano (KERD), Hajiya Rabi Inuwa Hussaini, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishinta da ke Kano. Ta ce a shekarar da ta gabata gwamnati ta biya wa ɗalibai dubu ɗari da talatin da bakwai kuɗin jarrabawar NECO, yayin da a bana aka biya wa kusan ɗalibai…
Read More