ukarofi

12565 Posts
2027: NDC ce kaɗai za ta iya cire wa ‘yan Najeriya kitse a wuta – Dogo Shammah

2027: NDC ce kaɗai za ta iya cire wa ‘yan Najeriya kitse a wuta – Dogo Shammah

Daga JOHN D WADA a Lafia Shugaban jam’iyyar Nigeria Democratic Congress [NDC] a jihar Nasarawa Hon. Dogo Shammah ya ce a yanzu haka jam’iyyar ta samu bunƙasa da farin jini cikin lokaci ƙalilan inda a yanzu tama zama babbar jam’iyyar adawa a fadin ƙasar nan. Ya faɗi hakan ne a jawabinsa a lokacin wani babban zaman hulɗa da 'yan takara a inuwar jami'iyyar da sauran masu ruwa da tsakinta na yankin Arewa ta tsakiya wanda aka gudanar a Lafia babbar birnin jihar ranar Juma’a. A cewarsa kasancewar wakilai daga jihohi shida na yankin Arewa ta tssakiyar da babban birnin tarayya…
Read More
Magoya bayan Jidda sun yi watsi da zargin maguɗin zaɓen fidda gwani na APC a Gombe

Magoya bayan Jidda sun yi watsi da zargin maguɗin zaɓen fidda gwani na APC a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE, Magoya bayan Hon. Zakariyya Jidda, ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye ƙarƙashin jam’iyyar APC, sun yi watsi da zarge-zargen cewa ana shirin yin maguɗi a tsarin sake tantance membobin jam’iyyar ta hanyar aiki da na'urar lantarki da kuma zaɓen fidda gwani a jihar Gombe. Ƙungiyar magoya bayan, ƙarƙashin jagorancin shugabanta Abubakar Saleh, ta bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe, balle makama da yaudara da kuma na siyasa, tana mai jaddada cewa Hon. Jidda da magoya bayansa suna goyon bayan sahihin tsari mai cike da gaskiya da adalci kamar yadda APC ta…
Read More
Jigawa 2027: Yadda haɗakar Badaru da Lamido ke barazana ga siyasar Namadi

Jigawa 2027: Yadda haɗakar Badaru da Lamido ke barazana ga siyasar Namadi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A jihar Jigawa, inda siyasa ta daɗe tana tafiya a ƙarƙashin manyan jiga-jigai masu ƙarfi, tsarin shugabanci mai zurfi da kuma ƙawance na siyasa da aka gina tsawon lokaci, fafatawar neman kujerar gwamnati gabanin zaɓen shekarar 2027 na ƙara zama zaya daga cikin mafi zafi da tayar da ƙura a tarihin dimokuraɗiyyar jihar. Abin da tun farko ya yi kama da tafiyar sake zaɓen Gwamna Umar Namadi cikin sauƙi, yanzu yana rikiɗewa zuwa wata babbar arangamar siyasa mai cike da sauyin aminci, rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar APC, dawowar jam’iyyar PDP da kuma haɗuwar wasu manyan…
Read More
Dalilin da ya sa na kai wa Kakakin Majalisar Wakilai fizga – Matashi

Dalilin da ya sa na kai wa Kakakin Majalisar Wakilai fizga – Matashi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani mazaunin garin Zariya mai suna Ahmad Sa’idu, wanda aka fi sani da Abba, ya bayyana dalilin da ya sa ya riƙe rigar Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Abbas Tajudeen, yayin wani taron siyasa da aka gudanar a birnin. Ahmad Sa’idu ya yi wannan bayani ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin a Zariya, inda ya kuma nemi afuwar Kakakin Majalisar kan lamarin da ya faru a lokacin taron bayyana aniyar Abbas Tajuddeen na sake tsayawa takara, wanda aka gudanar a filin Idi na Mallawa. Ya ce, abin da ya sa ya…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta wajabta gwajin miyagun ƙwayoyi kan ɗaliban sakandare

Gwamnatin Tarayya ta wajabta gwajin miyagun ƙwayoyi kan ɗaliban sakandare

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da sabbin tsauraran matakai domin yaƙi da shaye-shaye da amfani da miyagun ƙwayoyi a makarantu, inda ta wajabta gwajin ƙwayoyi ga ɗaliban makarantun sakandare tare da tanadin dakatar da ɗaliban da aka samu suna ci gaba da amfani da ƙwayoyi bayan shan magani da gyaran hali. Rahoton ya nuna cewa sabbin matakan na ƙunshe ne a cikin Jagororin ƙasa Na Yaƙi Da Amfani Da Miyagun ƙwayoyi A Makarantu A Nijeriya, wanda aka tsara domin rage yawaitar shaye-shaye tsakanin ɗalibai da kuma samar da yanayin karatu mai aminci a makarantun faɗin ƙasa.…
Read More
Kungiyar masu sayar da kayan gyaran motoci ta sha alwashin samar da cigaba — Baban Uwani

Kungiyar masu sayar da kayan gyaran motoci ta sha alwashin samar da cigaba — Baban Uwani

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Sabon shugaban ƙungiyar masu sayar da kayan gyaran ababen hawa ta jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ahmad Baban Uwani, ya sha alwashin kawo gyara da cigaba a harkokin kasuwancin ƙungiyar. Ya bayyana hakan ne yayin bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar da aka gudanar a dakin taro na tunawa da Malam Aminu Kano da ke unguwar Gwammaja a Kano. Kungiyar, wadda aka fi sani da Kano State ɓehicle Spare Parts Sellers Association, ta gudanar da zaben shugabanninta ne ta hanyar maslaha domin jagorantar kungiyar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. A jawabinsa, shugaban ƙungiyar ya ce…
Read More
Hajjin 2026: Gwamnan Kano ya naɗa Sarkin Gaya a matsayin Amirul Hajj

Hajjin 2026: Gwamnan Kano ya naɗa Sarkin Gaya a matsayin Amirul Hajj

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗa Sarkin Gaya, Mai Martaba Alhaji Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin Amirul Hajj na jihar domin jagorantar aikin hajjin shekarar 2026. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Talata. Sanarwar ta kuma bayyana cewa an nada Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz, a matsayin mataimakin Amirul Hajj. Gwamnatin jihar ta ce Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano za ta bai wa Amirul Hajj da mataimakinsa cikakken hadin kai…
Read More
Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jamilu Chiroma ta rantsar da sabbin ɗalibai

Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jamilu Chiroma ta rantsar da sabbin ɗalibai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Jamilu Chiroma da ke Kano ta gudanar da bikin rantsar da sabbin ɗaliban da aka ɗauka domin fara karatu a makarantar. An gudanar da bikin ne a harabar kwalejin da ke kan titin Airport a Kano, ranar Asabar, tare da halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban, iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi. Da yake jawabi bayan rantsar da ɗaliban, wanda ya assasa kwalejin, Alhaji Jamilu Abubakar Chiroma, ya bayyana cewa makarantar na daga cikin cibiyoyin ilimi biyar da suka samu sahalewar Ma’aikatar Ilimi ta…
Read More
Siyasata ta nema wa al’umma mafita ce — Injiniya Bello Gwarzo

Siyasata ta nema wa al’umma mafita ce — Injiniya Bello Gwarzo

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyun ANPP da PDP, kuma tsohon Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadeja da Jama’are, Injiniya Bello Sani Gwarzo, ya bayyana cewa duk wata siyasa da yake yi manufarta ita ce samar wa al’umma mafita da inganta rayuwarsu. Injiniya Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a Kano, inda ya ce dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC shi ne saboda halin ƙunci da matsin rayuwa da al’umma ke ciki. Ya ce ba zai yiwu jama’a na cikin wahala ana kuka da…
Read More
Kashe mutane uku bayan rantsar da Garo: Wane mataki gwamnatin Kano za ta ɗauka?

Kashe mutane uku bayan rantsar da Garo: Wane mataki gwamnatin Kano za ta ɗauka?

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Bayan rantsar da Alhaji Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano, an samu tashin hankali da ya yi sanadin mutuwar wasu matasa uku a Kano. Rahotanni sun bayyana cewa dubban magoya baya ne suka halarci bikin rantsuwar wanda aka gudanar a gidan gwamnatin Kano cikin cunkoso da annashuwa. Sai dai bayan kammala bikin ne aka samu hatsaniya tsakanin wasu matasa a yankin Dan Dago, lamarin da ya kai ga rasa rayukan mutane uku. Wani rahoto daga gidan rediyon Premier ya ce ɗaya daga cikin matasan an kai masa hari ne yayin da yake…
Read More