ukarofi

12565 Posts
Gina jami’o’i biyu a Kano ne ya sa muke son Kwankwaso — Hon. Sa’ad Darki

Gina jami’o’i biyu a Kano ne ya sa muke son Kwankwaso — Hon. Sa’ad Darki

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu yabo daga Hon. Sa’ad Ibrahim Darki, wanda aka fi sani da Janar, bisa irin gudummawar da ya bayar wajen bunkasa ilimi a jihar Kano. Hon. Sa’ad Janar ya bayyana cewa gina jami’ar Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUSTECH) Wudil a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2003, da kuma jami’ar Northwest University a lokacin wa’adin mulkinsa na biyu daga 2011 zuwa 2015, na daga cikin manyan dalilan da suka sa yake goyon bayan Kwankwaso. Ya ce Kwankwaso ya nuna kishin ilimi musamman ga ‘ya’yan talakawa,…
Read More
Yadda Hon. Abba Anas ya rasa ransa a hannun ’yan bindiga duk da karɓar kuɗin fansa

Yadda Hon. Abba Anas ya rasa ransa a hannun ’yan bindiga duk da karɓar kuɗin fansa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ’Yan bindiga sun sako gawar tsohon ɗan Majalisar Wakilai ta ƙasa kuma jigo a jam’iyyar ADC, Abba Anas Adamu, bayan da iyalansa suka biya kuɗin fansa har Naira miliyan 50. Rahotanni sun bayyana cewa an sace marigayin tare da wani ɗan siyasa daga jihar Jigawa, Ali Tukur Gantsa, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja domin halartar taron jam’iyyar ADC. Majiyoyi kusa da iyalan sun shaida cewa masu garkuwar sun fara neman Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa, kafin daga bisani aka sasanta aka rage zuwa Naira miliyan 50. An ce kuɗin ne ya…
Read More
An sace guzirin maniyyatan Jigawa uku a Saudiyya

An sace guzirin maniyyatan Jigawa uku a Saudiyya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Aƙalla maniyyata uku daga jihar Jigawa da ke shirin gudanar da aikin Hajjin bana na 2026 a ƙasar Saudiyya sun rasa kuɗaɗe da wasu kayayyaki masu muhimmanci sakamakon satar da aka yi musu a biranen Makkah da Madinah. ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, wani dattijo Bafulatani mai suna Baba Katanga daga ƙauyen Katanga da ke ƙaramar hukumar Kiyawa, ya bayyana cewa ya yi asarar dala Amurka 400 bayan hawa tasi daga Masallacin Harami zuwa otel ɗinsa mai suna Mahabbat Al Akhawin da ke Makkah. Maniyyacin ya zargi direban motar da amfani da…
Read More
Rashin hukunta masu laifi na lalata tsarin kwangila – Shugaban hukumar BPP

Rashin hukunta masu laifi na lalata tsarin kwangila – Shugaban hukumar BPP

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Hukumar Kula da Sayen Kayayyaki ta ƙasa (BPP), Dakta Adebowale Adedokun, ya bayyana cewa rashin ɗaukar tsauraran matakai kan masu karya ƙa’idoji da kuma ƙarancin ƙwarewar jami’an saye da kwangila ne manyan matsalolin da ke kassara tsarin saye da kwangilar gwamnati a Nijeriya. Adedokun ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja ranar Lahadi, inda ya yi bayani kan ƙalubalen da hukumar ke fuskanta da kuma matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana a harkokin kwangilar gwamnati. A cewarsa, tsawon shekaru ana kasa hukunta…
Read More
Zaɓen fidda gwani na APC: Hamza Sule Faskari zai yi takarar majalisar wakilai a Katsina

Zaɓen fidda gwani na APC: Hamza Sule Faskari zai yi takarar majalisar wakilai a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Masu ruwa da tsaki na jam'iyar APC ta tabbatar da takarar Hamza Sule zai wakilci al'ummar ƙananan hukumomin Faskari,Ƙankara da Sabuwa a zauren majalisar wakilai a zaɓen 2027. Bikin jaddada takarar da ya gudanar a Ƙankara da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyar sun yaba da yadda kwamitin sasancin ya gudanar da aikin sa. Shugaban kwamitin sasancin Injiya Tanimu Sabuwa ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki na jam'iyar da suka fito daga mazaɓu 31 na ƙananan hukumomin Faskari, Ƙanƙara da Sabuwa wanda suka wakilci ɗaukacin ya'yan jam'iyar suka tabbatar da takarar…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: An kammala zaɓen majalisar wakilai a wasu sassan Akwanga na jihar Nasarawa

Da Ɗumi-ɗumi: An kammala zaɓen majalisar wakilai a wasu sassan Akwanga na jihar Nasarawa

Daga JOHN D WADA a Lafia A halin yanzu an kammala wasu daga cikin zaɓukan fitar da gwani na 'yan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) daga Arewacin jihar Nasararsa inda a yanzu ake cigaba da tattara ƙuri'un a VIP lodge dake nan cikin garin Akwanga hedikwatar karamar hukumar Akwanga a jihar. Wakilinmu ya ruwaito cewa an kaɗa ƙuri'un ne cikin kwanciyar hankali cikin tsarin ƙato bayan ƙato kamar dai yadda hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta tanadar. Wasu manyan masu faɗa aji a ƙaramar hukumar ta Akwanga ciki har da shugaban ƙaramar…
Read More
Zaɓen fidda gwani na APC: Hamza Sule Faskari zai yi takarar majalisar wakilai a Katsina

Zaɓen fidda gwani na APC: Hamza Sule Faskari zai yi takarar majalisar wakilai a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Masu ruwa da tsaki na jam'iyar APC ta tabbatar da takarar Hamza Sule zai wakilci alummar ƙananan hukumomin Faskari,Kankara da Sabuwa a zauren majalisar wakilai a zaɓen 2027. Bikin jaddada takarar da ya gudanar a Ƙankara da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki na jam'iyar sun yaba da yadda kwamitin sasancin ya gudanar da aikin sa. Shugaban kwamitin sasancin Injiya Tanimu Sabuwa ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki na jam'iyar da suka fito daga mazaɓu 31 na ƙananan hukumomin Faskari, Ƙankara da Sabuwa wanda suka wakilci ɗaukacin ya'yan jam'iyar suka tabbatar da takarar…
Read More
Zamfara ta Arewa 2027: Sanata Tijjani Ƙaura ya ayyana tsayawa takara

Zamfara ta Arewa 2027: Sanata Tijjani Ƙaura ya ayyana tsayawa takara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar All Progressives Congress APC, a mazaɓar sanata ta Arewa a Jihar Zamfara sun gudanar da wani babban gangami a garin Ƙaura Namoda don nuna goyon bayan yunƙurin Sanata Tijjani Yahaya Ƙaura na sake zaɓen sa don ⁰komawa Majalisar Dattawa a 2027. A wurin taron, Ƙaura ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a hukumance, yana mai jaddada aniyar sa don samar wa matasa ayyukan yi sama da 2,000 idan aka sake zaɓar sa. Ƙaura ya nuna tarihinsa a lokacin wa'adinsa na baya, yana mai cewa an ɗauki matasa sama da…
Read More
Hajji 2026: Maniyyatan farko daga Kano sun tashi zuwa Saudiyya

Hajji 2026: Maniyyatan farko daga Kano sun tashi zuwa Saudiyya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jirgin farko na alhazan jihar Kano ya tashi zuwa Saudi Arabia domin gudanar da ibadar hajjin bana. Rukunin farko na alhazan 558 ya tashi ne a jirgin Max Air daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano zuwa birnin Madinah da misalin ƙarfe 12:48 na dare a yau Asabar, 16/05/2026. Rahotanni sun nuna cewa alhazan sun isa Filin jirgin Madina da misalin ƙarfe 7:35 na safe. A cikin maniyata 558 da suka tashi 333 maza ne sai mata 225. Kazalika, alhazan da suka tafi sun fito ne daga ƙananan hukumomi Dala, Gwale Ungoggo da kuma…
Read More
Jamila Abdu Yandoma ta zama yar takarar kujerar majalisar wakilai a Katsina

Jamila Abdu Yandoma ta zama yar takarar kujerar majalisar wakilai a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jamila Abdu Yandoma ta zama yar takarar kujerar majalisar wakilai da ke wakiltar ƙananan hukumomin Mani da Bindawa a Jihar Katsina bayan kammala zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC a tsakaninta da Ahmed Sale da suka fito daga Mani. Ita dai Jamila ta doke abokin hamayyar ta Ahmed Sale da kuri'a 24989' shi Kuma ya Sami kuri'a 1056 Kamar yadda shugaban kwamitin zaɓe Shuaibu Duwan ya sanar a ɗakin taro na ƙaramar hukumar Mani. A jawabin ta Jamila Abdu Mani tayi godiya ga gwamna Dikko Raɗɗa da yaba mata dama suka shiga majalisar zartarwa ta…
Read More