17
May
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, CP Ahmed Sanusi, ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar Matan Jami’an 'Yan Sanda ta Nijeriya (POWA) reshen Abuja, ƙarƙashin jagorancin shugabarta, Hajiya Maimuna Sanusi, a hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Garki a Abuja. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Talata. A yayin ziyarar, shugabar POWA, Hajiya Maimuna Sanusi, ta yaba wa Kwamishinan ’Yan Sandan bisa amincewa da ziyarar tare da jinjinawa salon jagorancinsa da ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da…
