ukarofi

12560 Posts
Farashin mai ya tashi bayan Trump ya yi watsi da sharuɗɗan Iran

Farashin mai ya tashi bayan Trump ya yi watsi da sharuɗɗan Iran

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya yi tashin gwauron zabi bayan Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi watsi da sabbin sharuɗɗan da Iran ta gabatar domin kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya. Trump ya bayyana martanin Iran ga tayin zaman lafiya da Amurka ta gabatar a matsayin “abin da ba za a amince da shi ba ko kaɗan,” lamarin da ya ƙara tayar da hankulan duniya kan yiwuwar sake ɓarkewar rikici bayan makonni ana tattaunawar diflomasiyya. A wani saƙo da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta na Truth Social ranar Lahadi, shugaban na…
Read More
Manyan bankuna sun samu kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 18.2 a 2025

Manyan bankuna sun samu kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 18.2 a 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Manyan bankunan Nijeriya masu matsayi na farko sun fitar da rahotannin kuɗaɗensu na shekarar 2025, inda suka nuna haɗaɗɗen sakamako mai cike da ƙarfafa gwiwa ga masu zuba jari da tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya. Rahoton kuɗaɗen da aka tantance zuwa ranar 31 ga Disambar 2025 ya nuna cewa jimillar kuɗaɗen shiga na manyan bankunan ta ƙaru da kaso 7.69 cikin zari, daga Naira tiriliyan 16.9 a shekarar 2024 zuwa tiriliyan N18.2 a shekarar 2025. Kamfanin Access ne ya jagoranci wannan ci gaba bayan kuɗaɗen shigarsa sun tashi zuwa tiriliyan N5.52 daga tiriliyan N4.87 da ya…
Read More
Shigo da motoci ta jiragen ruwan Nijeriya ya ƙaru da kashi 67 a 2026 – NPA

Shigo da motoci ta jiragen ruwan Nijeriya ya ƙaru da kashi 67 a 2026 – NPA

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA), ta bayyana cewa yawan motocin da aka shigo da su ta tashoshin jiragen ruwa na ƙasar ya ƙaru da kashi 67 cikin ɗari a farkon shekarar 2026 idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2025. Bayanan da ke cikin rahoton nazarin ayyukan hukumar na watanni ukun farko na 2026 sun nuna cewa an sarrafa motoci 58,870 a tashoshin jiragen ruwa daban-daban na ƙasar tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar 2026, sabanin motoci 35,262 da aka samu a irin wannan lokaci a bara. Rahoton ya kuma nuna…
Read More
Da gaske jarumi Alex Ekubo ya rasu?

Da gaske jarumi Alex Ekubo ya rasu?

Daga AISHA ASAS  Rahotanni da suka bazu cikin gaggawa a kafafen sada zumunta sun jefa dubban masoya fina-finai cikin ruɗani da jimami bayan wasu bayanai sun yi iƙirarin cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Alex Ekubo, ya rasu yana da shekaru 40 a duniya. Jita-jitar ta fara ɗaukar hankali ne bayan wani saƙo da fitaccen jarumi Godwin Nnadiekwe ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana matuƙar kaɗuwa da alhini kan wani “mummunan labari” da ya ce ya samu. A cikin saƙon, ya bayyana Ekubo a matsayin baiwar da ba kasafai ake samu irinta ba a masana’antar Nollywood, yana mai…
Read More
Daga tarihin karramawa zuwa sabuwar alƙiblar Nollywood: Cikakken nazari kan manyan nasarorin AMVCA 2026

Daga tarihin karramawa zuwa sabuwar alƙiblar Nollywood: Cikakken nazari kan manyan nasarorin AMVCA 2026

Daga AISHA ASAS  Da yammacin ranar Asabar ne titunan yankin Victoria Island da ke Jihar Iko suka fara cunkoso tun kafin a isa lokacin fara bikin karramawa mafi girma a masana’antar fina-finai ta Afirka, wato Africa Magic Viewers’ Choice Awards 2026. Motoci masu tsada suna jerawa a kofar Eko Hotel & Suites yayin da dubban masoya nishadi, ‘yan jarida, masu ɗaukar hoto da masu sharhi daga sassa daban-daban na duniya suka mamaye wajen domin shaida abin da mutane da dama suka kira “daren da zai tantance sabbin sarakunan Nollywood.” Tun daga wajen jan kafet, ana iya fahimtar cewa AMVCA ta…
Read More
Nijeriya za ta iya zama cibiyar samar da magunguna a Afirka — Shugaban NAIP

Nijeriya za ta iya zama cibiyar samar da magunguna a Afirka — Shugaban NAIP

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙungiyar Masana Haɗa Magunguna ta Masana’antu ta Nijeriya (NAIP), Pharm. (Sir) Bankole Ezebuilo, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ƙarfafa tallafi ga masana’antun haɗa magunguna na cikin gida domin rage dogaro da shigo da magunguna daga ƙasashen waje tare da mayar da Nijeriya cibiyar samar da magunguna a nahiyar Afirka. Ezebuilo ya bayyana hakan ne yayin taron ƙasa karo na 29 na shekara-shekara da horaswar ƙungiyar NAIP da aka gudanar a Ilorin, babban birnin jihar Kwara. Da yake jawabi a taron mai taken: “Haɗin Gwiwa da ƙirƙire-ƙirƙire Domin Gina Mafita Ta Cikin Gida Don…
Read More
POWA ta nemi haɗin kan rundunar ’yan sanda don inganta walwalar iyalai

POWA ta nemi haɗin kan rundunar ’yan sanda don inganta walwalar iyalai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, CP Ahmed Sanusi, ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar Matan Jami’an 'Yan Sanda ta Nijeriya (POWA) reshen Abuja, ƙarƙashin jagorancin shugabarta, Hajiya Maimuna Sanusi, a hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Garki a Abuja. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Talata. A yayin ziyarar, shugabar POWA, Hajiya Maimuna Sanusi, ta yaba wa Kwamishinan ’Yan Sandan bisa amincewa da ziyarar tare da jinjinawa salon jagorancinsa da ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da…
Read More
Ya kamata mu kula da gyaran maƙabartu domin su ne gidajenmu na gaskiya – Malam Mai Gemu

Ya kamata mu kula da gyaran maƙabartu domin su ne gidajenmu na gaskiya – Malam Mai Gemu

Daga DAUDA USMAN a Legas An shawarci al’ummar Musulmi mazauna jihar Legas da ma Nijeriya baki ɗaya da su ƙara himma wajen gyara da kula da maƙabartu, kasancewar su ne gidajen gaskiya na kowa bayan mutuwa. Wannan kira ya fito ne daga bakin Malam Ibrahim Mai Gemu, ɗan asalin ƙaramar hukumar Rogo ta jihar Kano, wanda ke zaune a unguwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas, kuma shugaban kwamitin kula da gyaran maƙabartun yankin. Malam Ibrahim Mai Gemu ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar aikin cikon ƙasa a maƙabartun Mile 12 a ranar Lahadin da ta…
Read More
Kungiyar Wala Warabe Dure ta Gwoza ta gudanar da taron haɗin kai a Legas

Kungiyar Wala Warabe Dure ta Gwoza ta gudanar da taron haɗin kai a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Kungiyar Wala Warabe Dure ta al’ummar ƙaramar Hukumar Gwoza da ke jihar Borno, mazauna jihar Legas, ta gudanar da babban taron sada zumunta da ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobinta a jihar. An gudanar da taron ne a ranar Lahadin da ta gabata a yankin Marine Bridge da ke ƙaramar hukumar Apapa a jihar Legas, inda dumbin shugabanni, mambobi da matasan ƙaramar hukumar Gwoza mazauna sassa daban-daban na Legas suka halarta. Taron ya mayar da hankali ne kan bunƙasa haɗin kai, taimakon juna da kuma samar da hanyoyin da za su ƙarfafa zaman lafiya da ci…
Read More
An gudanar da taron goyon bayan ɗan takarar gwamnan Kano na ADC, Malam Ibrahim Khalil

An gudanar da taron goyon bayan ɗan takarar gwamnan Kano na ADC, Malam Ibrahim Khalil

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kungiyoyin magoya bayan Malam Ibrahim Khalil sun gudanar da gagarumin taron nuna goyon baya ga dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Malam Ibrahim Khalil, inda dumbin jama’a daga sassa daban-daban suka halarta. Taron ya samu halartar farfesoshi, malaman addinin Musulunci, wakilan Kiristoci, mata, matasa da sauran magoya bayan jam’iyyar ADC, wadanda suka hallara domin nuna goyon baya ga takarar Malam Ibrahim Khalil gabanin zaben da ke tafe. Masu jawabi daban-daban sun bayyana damuwa kan halin matsin rayuwa da matsalolin tattalin arziki da siyasa da al’umma ke fuskanta a jihar Kano…
Read More