ukarofi

12560 Posts
APC ta ƙasa ta ayyana zaɓen fidda gwani na majalisar tarayya a Zamfara gobe

APC ta ƙasa ta ayyana zaɓen fidda gwani na majalisar tarayya a Zamfara gobe

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar APC ta ƙasa ta shirya gudanar da zaɓen fidda gwani na 'yan takarar majalisar tarayya a gobe Litinin. Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen da jam'iyyar ta APC ta ƙasa ta turo a Jihar Dr. Auwal Abdullahi Aliyu ya bayyana hakan a zantawar SA da manema labarai a Gusau yau Litinin. A cewar sa, kwamitin su zai tabbatar da an gudanar da zaɓen fidda gwanin cikin adalci da nasara. Dr. Abdullahi ya ƙara da cewar, kwamitin sa ya samu labarin wasu sun ayyana kansu a matsayin kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwanin a Jihar Zamfara,…
Read More
An ƙaddamar da ƙungiyar ‘Grassroot Mobilization for Tinubu-Dikko 2027’ a Katsina

An ƙaddamar da ƙungiyar ‘Grassroot Mobilization for Tinubu-Dikko 2027’ a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar Grassroots Mobilisation for Tinubu-Dikko 2027 ta ƙaddamar da shuwagabannin ƙungiyar tare da basu takardar kama aiki domin bada gudunmuwa wajen tazarcen Tinubu-Dikko a zaɓen. Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Hon. Abubakar Tsanni Soja ta rantsar da mambobin ta a ofishin ta dake Kanbarawa a cikin birnin Katsina. Dr. Abubakar Soja Tsanni, wanda shi ne kodinetan ƙungiyar GMTD, ya ce an kafa ƙungiyar ne domin wayar da kan jama’a, haɗa matasa da mata, da kuma tallafa wa shirye-shiryen ci gaba da gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina. Da yake jawabi ministan gidaje da tsara birane Injiniya Dr.…
Read More
Attajiri ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen fidda gwani na APC a Balanga/Billiri

Attajiri ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen fidda gwani na APC a Balanga/Billiri

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya mai neman wakiltar mazaɓar Balanga/Billiri a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Hon. Alfred John Attajiri, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwani da aka bayyana, yana mai zargin cewa ba a gudanar da sahihin zaɓe ba a mazaɓar kafin sanar da sakamakon. Attajiri ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya ce sanar da sakamakon zaɓen da bai gudana ba barazana ce ga dimokuraɗiyya da kuma mutuncin jam’iyyar APC. Ya zargi tsohon kwamishina a Jihar Gombe, Hon. Mohammed Sa’idu Yila Fawu, da…
Read More
Gwamnatin Katsina ba ta da iko da DSS ko jami’an tsaro – Maiwada Ɗan Malam

Gwamnatin Katsina ba ta da iko da DSS ko jami’an tsaro – Maiwada Ɗan Malam

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnati a bisa tsarin mulkin Nijeriya ba ta da iko akan jami'an tsaro da DSS Inji Maiwada Dan Malam Darakta Janaral kan yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina. Ɗan Malam ya maida martani ne akan zargin da Ahamed Saleh Junior wanda ya nemi tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai na mazaɓar ƙananan hukumomin Mani da Bindawa ƙarƙashin jam'iyar APC. Saleh Juniya ya zargi gwamnatin Katsina da sanya a tsare shi har sai da aka kammala zaɓen fidda yan takara na jam'iyar a mazaɓar Mani da Bindawa. DG Ɗanmalam ya bayyana cewa DSS hukumar ce da take…
Read More
An tsare ni sai da aka kammala zaɓen fidda gwani na APC sannan aka sake ni – Ahmed Saleh Junior

An tsare ni sai da aka kammala zaɓen fidda gwani na APC sannan aka sake ni – Ahmed Saleh Junior

Ɗaya daga cikin masu neman takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a mazaɓar Mani/Bindawa da ke jihar Katsina, Ahmed Saleh Junior, ya zargi gwamnatin jihar da wasu shugabannin jam’iyyar APC da hana shi damar shiga zaɓen fidda gwani da aka yi na mazabar Mani/Bindawa ta hanyar tsare shi har sai da aka kammala zabe aka sake shi Wanda ya bayyana haka a matsayin rashin adalci. Saleh Junior ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a garin Mani inda ya ce jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama shi tare da tsare shi har sai bayan an kammala…
Read More
Gobara ta tashi a sakatariyar gwamnatin tarayya ta Jihar Nasarawa

Gobara ta tashi a sakatariyar gwamnatin tarayya ta Jihar Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafia Wani sashe na wani babban sakatariyar gwamnatin tarayya da ake kira Muhammad Sidi Bage Federal Secretariat dake Lafia babban birnin Jihar Nasarawa ya kama da wuta da yammacin jiya Asabar inda lamarin ya jefa ma'aikata da mazauna kusa da sakatariyar cikin fargaba. A cewar ganau da abin ya auku a idonsu sun bayyana wa wakilinmu a jihar cewa wutar ta tashi ne daga wani ofis dake bene na biyu na ginin sakatariyar mai hawa uku inda hayaƙi mai yawa da kauri ya fara fita daga yankin da abin ya faru ya kuma mamaye sauran…
Read More
Yadda shari’ar “Farmgate” ke barazana ga makomar shugaban Afirka ta Kudu

Yadda shari’ar “Farmgate” ke barazana ga makomar shugaban Afirka ta Kudu

A yayin da siyasar Afirka ta Kudu ke ƙara shiga wani sabon yanayi mai cike da tashin hankali, shugaban ƙasar, Cyril Ramaphosa, na fuskantar ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen siyasa tun bayan hawansa mulki a shekarar 2018. Wannan na zuwa ne bayan sake farfaɗo da batun tsige shi daga mulki sakamakon wata badaƙala da aka fi sani da “Farmgate” lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce mai girma kan maƙudan kuɗaɗen ƙasashen waje da aka ce an ɓoye a cikin kujera a gonarsa. Rahotanni sun nuna cewa barayin da suka shiga gonar shugaban ƙasar sun yi awon gaba da dubban daloli da…
Read More
Mace ta gwabza faɗa da kada domin ceto karenta

Mace ta gwabza faɗa da kada domin ceto karenta

Wata mata a jihar Florida da ke ƙasar Amurka ta jawo hankalin jama’a bayan ta yi artabu da wani babban kada domin ceton karenta daga bakin dabbar. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a kusa da wani tafki yayin da matar ke yawo tare da karenta da safe. A cewar shaidu, kwatsam sai wani ƙaton kada ya fito daga ruwa ya cafke karen da bakinsa, lamarin da ya tayar da hankalin matar. Ba tare da tsoro ba, matar ta yi gaggawar bin dabbar inda ta fara bugunta tare da ƙoƙarin buɗe bakin kadar domin kwato karenta. Shaidu sun…
Read More
NDLEA ta kama hodar iblis ta biliyoyin naira a hannun wasu nakasassu

NDLEA ta kama hodar iblis ta biliyoyin naira a hannun wasu nakasassu

Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta kama wasu mutane uku masu larura bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a wasu samame daban-daban da aka gudanar a jihohin Anambra da Kwara. A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na hukumar, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun bi sahun wani mutum mai shekaru 60 mai suna Romanus Nwabara har zuwa dajin Akpaka da ke Onitsha a Jihar Anambra, inda suka kama shi da giram 250 na tabar wiwi nau’in skunk da aka shirya cikin ƙananan ledoji domin…
Read More
Hauhawar farashi: CBN ya gargaɗi gwamnoni kan kashe kuɗi ba tsari

Hauhawar farashi: CBN ya gargaɗi gwamnoni kan kashe kuɗi ba tsari

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (wato CBN) ya buƙaci gwamnatocin jihohi su ƙara nuna tsauraran matakan kula da kashe kuɗi da karɓar bashi yayin da bankin ke shirin rungumar sabon tsarin da zai mayar da hankali wajen rage hauhawar farashi a ƙasar. Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da manufofin tattalin arziki, Muhammad Sani Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar tare da jami’an gwamnatocin jihohi ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF). Ya bayyana cewa sabon tsarin kula da hauhawar farashi ba zai yi nasara ba idan gwamnatocin jihohi suka ci gaba da kashe kuɗi…
Read More