ukarofi

12560 Posts
2027: Masu ruwa da tsaki na ƙabilar Migili a Nasarawa sun roki Gwamna Sule ya ba su muƙamin mataimakin gwamna

2027: Masu ruwa da tsaki na ƙabilar Migili a Nasarawa sun roki Gwamna Sule ya ba su muƙamin mataimakin gwamna

Daga JOHN D WADA a Lafia Shugabannin ƙabilar Migili a Jihar Nasarawa sun roƙi gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule da ya zaɓi ɗan asalin Migili a matsayin mataimakin wanda zai gaje shi a zaɓen 2027. Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Lafia ranar Litinin, kwamared Sunday Aleku, mai magana da yawun matasan ƙungiyar masu ruwa da tsaki na Migili yace rokon yana da nufin tabbatar da cewa an ji muryar ƙungiyar a matakin mulki mafi girma na jihar. A cewar Aleku, mutanen Migili sun kasance masu goyon baya ga gwamnatoci daban-daban da daɗewa kuma suna taka rawar…
Read More
DCP Ahmed ya kada Sanata Goje a zaɓen fidda gwanin APC na Gombe ta Tsakiya

DCP Ahmed ya kada Sanata Goje a zaɓen fidda gwanin APC na Gombe ta Tsakiya

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Gombe Ɗaya daga cikin masu neman takarar kujerar Sanatan Gombe ta tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, DCP Ahmed Muhammad (mai ritaya), ya bayyana ƙwarin gwiwarsa na lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, bayan yadda ya ce an gudanar da zaɓe cikin lumana a ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba. Da yake zantawa da manema labarai a Deba bayan sa ido kan yadda zaɓen ke gudana, tsohon mataimakin kwamishinan ’yan sanda ya ce an gudanar da aikin cikin tsari, natsuwa da bin doka ba tare da wata tangarda ba. Ya ce hakan na daga cikin alamun sauyin ra’ayi da…
Read More
Yusuf Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar sanata na APC a Daura

Yusuf Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar sanata na APC a Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗan tsohon shugaban ƙasa Yusuf Buhari ɗan takarar jam'iyar APC a majalisar wakilai a zaɓen 2026 ya yaba da yadda jam'iyar ta gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar majalisar dattijai na shiyar Daura. Yusuf Buhari ya yi wannan yabo ga manema labarai a wata makaranta firamare a garin Daura lokacin da ya zagaya wurin da aka gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar jam'iyar. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar katsina Rt Hon Nasiru Yahaya Daura da Abdulkarim Aliyu AK suka fafata a neman tsayawa takarar kujerar majalisar dattijai na shiyar Daura. Tsohon Sanata Hadi Sirika da Shehu…
Read More
Lawal Daura ya yi alƙawarin samar da tsaro da inganta rayuwar al’ummar Katsina

Lawal Daura ya yi alƙawarin samar da tsaro da inganta rayuwar al’ummar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Malam Lawal Musa Daura, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a shekarar 2027, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen samar da tsaro da bunƙasa rayuwar al’ummar jihar. Lawal Musa Daura wanda tsohon darakta janaral na hukumar DSS ta ƙasa ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da ya fitar yayin bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar ADC. Daura ya ce matakin da ya ɗauka na shiga takara ya biyo bayan tuntuɓa da ya yi da masu ruwa da tsaki da kuma kiraye-kirayen…
Read More
Zaɓen fidda gwani na APC: Manyan ‘yan takara a Nasarawa sun sha kaye

Zaɓen fidda gwani na APC: Manyan ‘yan takara a Nasarawa sun sha kaye

Daga JOHN D WADA a Lafia Jam’iyyar APC mai mulki a jihar Nasarawa ta gudanar da zaɓen fidda gwaninta na ‘yan takarar majalisar wakilai ta tarayya a ranar 16 ga Mayu na shekarar 2026 inda ta sanar da waɗanda suka lashe zaɓukan a cikin mazaɓu huɗu daga cikin biyar da ke jihar. Musa Shuaibu Guri wanda ya jagoranci kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwanin ne ya sanar da sakamakon kamar haka: Mazabar Karu/Keffi/Kokona:Daniel Ogazi ya lashe da ƙuri’u 13,083. Ya doke Danladi Jatau wato shugaban majalisar dokokin Jihar wanda ya samu kuri’u 5,873. Sauran sakamakon a cewar sa shine kamar…
Read More
Idan ba ki samu damar karatu ba, ki kama sana’a – Farfesa Sa’adatu Liman

Idan ba ki samu damar karatu ba, ki kama sana’a – Farfesa Sa’adatu Liman

"Ni ƙwararriya ce musamman a fannin haƙƙin mata" Daga JOHN D. WADA  a Keffi  Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ita ce shugabar Jami’ar Gwamnatin Jihar Nasarawa da ke garin Keffi. Kwararriya ce a fannin ilimin addinin Islama kuma mace ta farko da aka taɓa naɗa wa a muƙamin shugabar jami’ar jihar bakiɗaya. A tattaunawar musamman da Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Nasarawa, JOHN D. WADA, ya yi da ita a ofishinta da ke jami’ar a garin Keffi ya gano cewa, farfesar a yanzu haka tafi kowacce mace a jihar ta Nasarawa samun lamboyin yabo daga ciki da wajen ƙasar nan bakiɗaya…
Read More
APC ta tabbatar da Majigiri a matsayin ɗan takarar majalisar tarayya ta Mashi/Dutsi

APC ta tabbatar da Majigiri a matsayin ɗan takarar majalisar tarayya ta Mashi/Dutsi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta tabbatar da Hon. Salisu Yusuf Majigiri a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na kujerar majalisar wakilai da zai wakilci mazaɓar Mashi/Dutsi a zaɓen shekarar 2027. An gudanar da taron tabbatarwar ne a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙaramar hukumar Mashi, ranar da jam’iyyar ta ware domin gudanar da zaɓukan fidda gwani a faɗin ƙasa. Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyya daga matakin ƙasa da jiha, masu ruwa da tsaki, jami’an tsaro, wakilan hukumar zaɓe da kuma ɗimbin magoya bayan jam’iyyar da suka hallara domin nuna goyon baya ga ɗan takarar. Hon.…
Read More
Ɗan takarar sanata na jam’iyyar NDC a Nasarawa ya yi alƙawarin ba wa mata da matasa fifiko

Ɗan takarar sanata na jam’iyyar NDC a Nasarawa ya yi alƙawarin ba wa mata da matasa fifiko

Daga JOHN D. WADA a Lafia Ɗan takarar kujerar sanatan Arewacin jihar Nasarawa a zaɓen fidda gwanin dake tafe ƙarƙashin jam’iyyar Nijeriya Democratic Congress [NDC] Arch. Duba Ishaya-Dodo yayi alƙawarin ƙarfafa tare da tallafa wa mata da matasa da bunƙasar ababen more rayuwa fifiko. Arch. Ishaya-Dodo ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Lafia fadar gwamnatin jihar. A cewarsa dalilin da yasa ya shiga takarar kujerar sanatan Arewacin Nasarawa shi ne saboda yana da sha’awar yi wa mutanen yankin hidima. Ishaya-Dodo ya ce yana da ƙarfin gwiwa da ƙwarewar da za ta ba shi damar…
Read More
Al-Makura ya bayyana goyon bayansa ga tsohon Sufeto Janar Adamu gabanin zaɓen fidda gwani na APC a Nasarawa

Al-Makura ya bayyana goyon bayansa ga tsohon Sufeto Janar Adamu gabanin zaɓen fidda gwani na APC a Nasarawa

Daga JOHN WADA a Lafia Umaru Tanko Al-Makura tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma mai kula da yankin Arewa ta tsakiya na ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ya bayyana goyon bayansa a fili ga neman tikitin gwamna na tsohon sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Abubakar Adamu. Sanarwar ta fito ne a ranar Lahadi a fadar mai martaba sarkin Lafia Mai Sheri'a Sidi Bagel inda Al-Makuran wanda shi ne kuma shugaban hukumar ilimi ta ƙasa na matakin farko yayi jawabi a ƙarshe na yawon shawara da Adamu yayi wa fadar sarakunan gargajiya a faɗin jihar. Al-Makura ya bayyana cewa dalilin da…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta dawo da aikin duba-gari

Gwamnatin Katsina za ta dawo da aikin duba-gari

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta yi gyara ga babbar dokar aikin duba gari ta ƙasa tare da sanya mata hannu domin bai wa malaman tsafta damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata da kuma gurfanar da masu karya dokokin tsafta a faɗin jihar. Mataimakin babban jami’in da ke kula da sashen duba gari na malaman tsafta a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina, Sanitarian Kabir Ahmad ne ya bayyana hakan yayin wani gangamin masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Katsina. Ya ce gyaran dokar wani muhimmin mataki ne na…
Read More