ukarofi

12560 Posts
Goje ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwanin APC na Sanatan Gombe ta tsakiya

Goje ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwanin APC na Sanatan Gombe ta tsakiya

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Sanata Muhammad Danjuma Goje ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Gombe ta Tsakiya, inda ya bayyana sakamakon da ake yaɗawa a matsayin na bogi. Wani sakamako da jami’in tattara sakamako, Dakta Habu Ɗahiru, ya bayyana ya nuna cewa DCP Mohammed Ahmed ne ya lashe zaɓen tare da zama ɗan takarar jam’iyyar a babban zaɓen shekarar 2027, bayan da ya samu ƙuri’u 42,785 yayin da Sanata Goje ya samu ƙuri’u 10,425. Sanata Goje na wakiltar mazabar sanatan tun daga shekarar 2011. Sai dai a cikin wata sanarwa da…
Read More
Da ma siyasar Nijeriya ta Musulmai ce kaɗai?

Da ma siyasar Nijeriya ta Musulmai ce kaɗai?

Daga UNCLE LARABI Tambayar da ke bakina ita ce, da ma siyasar Nijeriya ta Musulmai ce kaɗai ko kuma dole sai wanda zai yaudare ku da son musulunci za ku zaɓa? Mutane suna ba ni mamaki akan Peter Obi wai ba ya son Musulunci. Yanzu ba kakanku, Musulmin ke mulki ba Omologo? Uban me ya tsinana muku na kasancewarsa Musulmin banda azaba da yake gana mana? To, bari ku ji. Yanzu na ƙara hankali, na ƙara ilimi, na ƙara wayo, idona ya buɗe. Nigeria ba ta Musulmi ba ce, bare Musulmin bogi. Don haka ba Peter Obi ba, wallahi ko Ojuku ne…
Read More
Matasa ku farka: Yaɗa bidiyon tsiraici na lalata tarbiyya, addini da makomar al’umma

Matasa ku farka: Yaɗa bidiyon tsiraici na lalata tarbiyya, addini da makomar al’umma

A yau, al’ummarmu na fuskantar wani babban ƙalubale da ke ci gaba da yaɗuwa cikin sauri musamman a tsakanin matasa, wato matsalar ɗaukar da kuma yaɗa bidiyon tsiraici ta kafafen sada zumunta. Wannan mummunar ɗabi’a ta zama tamkar wata cuta da ke cinye tarbiyya, mutunci da kuma kyawawan ɗabi’un Hausawa da Musulunci ya gina tun shekaru masu yawa. Abin takaici ne yadda ake yawan samun rahotannin wasu ’yan mata da samari suna shiga soyayya ba tare da iyaka ko tsoron Allah ba, har su kai ga ɗaukar hotuna ko bidiyoyi yayin aikata fasiƙanci. A wasu lokutan budurwar ce da kanta…
Read More
Ba ni ne ke burin zama gwamnan Nasarawa da kaina ba, inji Abubakar Giza

Ba ni ne ke burin zama gwamnan Nasarawa da kaina ba, inji Abubakar Giza

Daga JOHN DOGO WADA a Lafiya  Alhaji Abubakar Giza ɗan takarar kujerar gwamnan Jihar Nasarawa ne a inuwar jami'ar Zenith Labor Party (ZLP). A tattaunawar nan na musamman da Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Nasarawa, JOHN DOGO WADA, ya yi da shi ya bayyana dalilin fitowarsa takarar da ire-iren ayyukan cigaban da zai gudanar in ya yi nasara da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: MANHAJA: Me kake niyyar yi wa Jihar Nasarawa idan ka yi nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar? ALHAJI ABUBAKAR: Ba burina ba ne na nemi zama gwamna da kaina. Ina Amurka ne a lokacin da mutanena…
Read More
A kiyaye martabar aure da mutuncin iyalinmu

A kiyaye martabar aure da mutuncin iyalinmu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mai karatu, nasan ba za ka kasa jin labarin nan da ya karaɗe kafafen watsa labarai da zaurukan sada zumunta ba, wanda aka ce wasu mutane bakwai a garin Azare da ke cikin ƙaramar Hukumar Karagum suna musanyar matansu na aure a tsakanin su. Mutumin da ya ɓullo da wannan sabon tsarin ya ce a mafarki ya gani ana umartarsa da su fara musanyar matansu a tsakaninsa da abokanensa su bakwai, waɗanda suka yi imani da wannan aƙida mai suna "Huddadu". Binciken rundunar Hisba ta garin Azare ya gano cewa, an kwana biyu ana wannan musanyen…
Read More
Kabilanci haramun ne, abu ne mai muni

Kabilanci haramun ne, abu ne mai muni

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Haƙiƙa ikirarin wai ASABIYYA ta taimaki Manzon Allah mai tsira da aminci, kawai dattin kiyayyace ga addinin tauhidi. Wai da a ka tasamma Manzon Allah SAW da barazanar kisa sai a ka mika aikin ga Banu Hashim su kuma su ka ki cika aiki don kare ƙabila! Duk wata hanya ko ta rubutu ne ko furtawa dab aka da ta taba darajar Manzon Allah to ba shakka akwai hatsari mai girma a ciki don ƙetare haddi ne da neman tsokana. Marubucin 'yan bazata ya kawo tarihi na cin zarafi ga Manzon Allah inda ya yI iƙirarin…
Read More
EFCC ta miƙa wa gwamnatin Katsina miliyan ₦837 na badaƙala

EFCC ta miƙa wa gwamnatin Katsina miliyan ₦837 na badaƙala

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa reshen Kano ta miƙa wa gwamnatin jihar Katsina kuɗaɗe da suka kai N837,485,389 da aka ƙwato daga wasu badaƙalolin karkatar da kuɗaɗen gwamnati. Hukumar ta ce an ƙwato kuɗaɗen ne daga bincike daban-daban da ta gudanar. A cewar EFCC, an ƙwato N547m daga wata badakalar karkatar da kuɗaɗen haraji da suka fito daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kamar WHO da MSF. Hukumar ta ce ana zargin wasu ma’aikatan hukumar tara haraji ta jihar da jami’an banki da hannu a lamarin. Ta ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda…
Read More
An tabbatar da Abdul’aziz ‘Yar’adua a matsayin ɗan takarar sanatan Katsina ta tsakiya

An tabbatar da Abdul’aziz ‘Yar’adua a matsayin ɗan takarar sanatan Katsina ta tsakiya

Daga UMAR GARBAa Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya jagoranci taron tabbatar da Sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Kanal Abdulaziz Musa Yar’adua mai ritaya, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC domin neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027. An gudanar da taron ne a Filin Wasa na Katsina Township Stadium, tare da halartar shugabanni, ‘yan jam’iyya da magoya baya daga sassan yankin. Shugaban Kwamitin zaɓe na APC daga hedikwatar jam’iyyar, Dakta Yakubu Macciɗo Ahmed, ya ce an cimma matsayar ne bayan yarjejeniya tsakanin masu ruwa da tsaki da sauran masu neman takarar. Shi ma shugaban kwamitin…
Read More
Majalisar Tarayya: Masu ruwa da tsaki a Giwa da Birnin Gwari sun buƙaci a mara wa Chiroma baya karo na biyu

Majalisar Tarayya: Masu ruwa da tsaki a Giwa da Birnin Gwari sun buƙaci a mara wa Chiroma baya karo na biyu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari sun yi kira ga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da ta sake bai wa ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Giwa/Birnin Gwari, Hon. Bashir Zubairu, wanda aka fi sani da Chiroman Birnin Gwari, damar tsayawa takara a karo na biyu domin ci gaba da ayyukan ci gaba da ya fara a yankin. Masu ruwa da tsakin sun bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar Giwa/Birnin Gwari Democratic Equity Forum ta shirya ranar Lahadi a Yakawada, inda suka bayyana cewa…
Read More
APC a Katsina ta tsayar da Nasiru Yahaya a matsayin ɗan takarar Majalisar Dattijai a zaɓen 2027

APC a Katsina ta tsayar da Nasiru Yahaya a matsayin ɗan takarar Majalisar Dattijai a zaɓen 2027

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jam'iyar APC a jihar Katsina ta amince wa kakakin majalisar dokoki na jihar Katsina ya zama ɗan takarar kujerar majalisar dattijai a shiyar Daura. Haka ya biyo bayan zaɓen fidda ɗan takara na cikin gida a jam'iyar da ya gudana a garin Daura tsakanin kakakin majalisar dokoki Rt Hon Nasiru Yahaya Daura da abokin hamayyar sa Alhaji Ahmed Kabir. Shugaban kwamitin zaɓe da Uwar jam'iya ta ƙasa Dr Yakubu Maccido ya fadi sakamakon zaɓen a tsakanin 'yan takarar biyu inda ya ce kakakin majalisar ya sami ƙuria 87,000 sai Ahmed Kabir ya sami ƙuria 2000…
Read More