ukarofi

12560 Posts
APC a Katsina ta tabbatar wa Sirajo Kwaskwaro da takarar majalisar dokoki

APC a Katsina ta tabbatar wa Sirajo Kwaskwaro da takarar majalisar dokoki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jam'iyar APC ta tabbatar wa Sirajo Abdu Kwaskwaro da takarar kujerar majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Kaita a jihar Katsina. Shugaban kwamitin fidda 'yan takarar wanda harwala yau shine shugaban ƙaramar hukumar Kaita Injiniya Bello Lawal Yandaki ya sanar tare da ƙaddamar da ɗan takarar. Ya ce samun nasarar kwaskwaro ya biyo bayan tsarin da uwar jam'iyar APC ta bi na gudanar da sasancin a tsakankanin 'yan takarar da nufin fidda guda ɗaya. Injiniya Bello Yandaki wanda ke riƙe da muƙamin shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta ƙasa ya tabbatar wa alummar ƙaramar hukumar…
Read More
Waɗanne hanyoyi ne ake iya sarrafa man jojoba?

Waɗanne hanyoyi ne ake iya sarrafa man jojoba?

Daga AISHA ASAS  Mai karatu barkanmu da sake kasancewa da shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyarmu.  Kamar yadda muka shafe makonni biyu muna tattaunawa kan wannan darasi mai muhimmanci. A wannan makon ma za mu sake ɗibo wani ɓangare ne daga wannan tsiro mai tarin albarka.  Ana iya amfani da man jojoba ta hanyoyi da dama, waɗanda ke iya taimaka wa wajen inganta fata tare da bata lafiya kan matsalolin ta da dama. Jojoba oil na da matuƙar amfani a fannoni da dama: 1. A matsayin mai cire kayan kwalliya (makeup remover): Masana fata sun sha…
Read More
Dandalin shawara: Matata bata taɓa godewa ƙoƙarina ba

Dandalin shawara: Matata bata taɓa godewa ƙoƙarina ba

Daga AISHA ASAS Malama Aisha sannu da ƙoƙari, ya iyali. Allah ya yi jagora. Don Allah ina so ki ja hankalin mata a shafinku na iyali akan mata masu ƙin godewa mazajensu, wallahi wasu matan ba su da imani, ko kaɗan ba su aminta da matsalar rayuwa da a ke ciki a yanzu ba. Matata shekara goma muna tare, amma ban taɓa barinta da yunwa ba, ba a taɓa ranar da ban kawo ba, sai dai wata rana da daɗi wata rana ba daɗi. Ba ta taɓa gode ƙoƙarina ba, sai dai duk ranar da na kasa kawo irin wanda…
Read More
Badu Bonsu: Sarkin Ghana da Turawa suka ajiye kansa fiye da shekaru 170

Badu Bonsu: Sarkin Ghana da Turawa suka ajiye kansa fiye da shekaru 170

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A tarihin nahiyar Afirka akwai labarai masu ɗauke da raɗaɗi, takaici da kuma darussa masu nauyi da suka nuna irin zaluncin mulkin mallaka da yadda Turawa suka muzguna wa al’ummomin Afirka. ɗaya daga cikin irin waɗannan labarai shi ne na Sarkin Ahanta na ƙasar Ghana, Nana Badu Bonsu II, wanda aka kashe a ƙarni na 19 sannan aka yanke kansa aka kai Turai inda aka ajiye shi tsawon sama da shekaru 170 kamar wani kayan tarihi. Labarin Badu Bonsu ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi tayar da hankali a tarihin hulɗar Turawa da…
Read More
Dabarun zama da miji mai saurin fushi da hanyoyin rage masa zafin rai (2)

Dabarun zama da miji mai saurin fushi da hanyoyin rage masa zafin rai (2)

Ci gaba daga makon da ya gabata Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D Kamar yadda muka faro a mako na baya an nuna yadda mace za ta mayar da hankali don inganta zamanta da mijinta da ya zamo mai saurin fushi ga cigaban wannan rubutu. Amma a wannan makon za mu mayar da hankali ne ga shi kansa mijin akan abin da zai yi don sauke zafin zuciya da kuma sakkowa akan lokaci ba tare da alaƙar aure ta ɓaci ba. Wannan bincike ya yi nazari kan matsalar saurin fushi a tsakanin maza a cikin aure da kuma rawar da…
Read More
Masarautar Katsina ta bayar da lambobin yabo ga hakimai da su ka yi zarra a hawan ƙaramar sallah

Masarautar Katsina ta bayar da lambobin yabo ga hakimai da su ka yi zarra a hawan ƙaramar sallah

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya gabatar da kofin da lambobin yabo ga hakimai da su kayi zarra a hawan ƙaramar sallah da ta gabata. Magajin Garin Katsina, Alh. Aminu Abdulmumini Kabir Usman shine ya zamo na ɗaya a hawan sallah ƙarama da ta gabata, inda Ƙauran Katsina Alh. Aminu Nuhu Abdulƙadir ya zamo na biyu sai Ɗan Galadiman Katsina Hakimin Ƙafur yazo na uku. Kurayen Katsina Alhaji Darda'u shine yazo na huɗu sannan daga na huɗu zuwa na goma an basu lambar yabo sannan sauran hakiman su 28 su ma an basu takardar…
Read More
Ƙungiyar APC Concern Group a Nasarawa ta nuna ɓacin rai kan yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani

Ƙungiyar APC Concern Group a Nasarawa ta nuna ɓacin rai kan yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani

Daga JOHN WADA a Lafia Ƙungiyar All Progressives Congress (APC) concern group a jihar Nasarawa ta nuna ɓacin rai kan yadda aka gudanar da zaɓukan fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar a faɗin jihar a yanzu inda suka bayyana tsarin a matsayin zamba. A cewar ƙungiyar dukkan tsarin zaɓen da aka gudanar a jihar kawo yanzu ya cika da maguɗi kuma bai bi ƙa’idar dimokuraɗiyya da adalci ba. Da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar ƙungiyar 'yan jaridu na jihar Nasarawa dake Lafia babban birnin jihar shugaban tawagar honorabul Abdullahi Yammani ya bayyana cewa an tsara zaɓukan da gangan…
Read More
‘Yan sanda sun ceto mutane 11 da ‘yan bindiga suka sace a Katsina

‘Yan sanda sun ceto mutane 11 da ‘yan bindiga suka sace a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta sanar da daƙile yunƙurin garkuwa da mutane a Ƙanƙara tare da ceto fasinjoji 11 da aka sace a hanyar Sheme zuwa Ƙankara. Haka kuma jami’an tsaron sun ƙwato shanu 25 da wasu ‘yan bindiga suka sace a Malumfashi bayan musayar wuta da maharan. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an bisa jarumtaka da gaggawar ɗaukar mataki. Ya yi kira ga alummar jihar da su taimakawa jami'an tsaro wajen bada bayanan sirri na maɓoyan waɗanan miyagun mutane. Yan sanda a shirye suke su kare rayuka…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta horar da masu sana’a 74 kan fasahar motocin lantarki

Gwamnatin Katsina za ta horar da masu sana’a 74 kan fasahar motocin lantarki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Katsina ta amince da horar da masu sana’a 74 kan ƙirƙira da haɓaka samfurin motocin lantarki (Electric Vehicle - EV), a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa matasa da bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire na fasaha a jihar. Mai kula da cibiyar koyon sana'o'i (Katsina Youth Craft Village), a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa shirin horaswar na tsawon watanni shida za a gudanar da shi ne a cibiyar, tare da haɗin gwiwar kamfanin Maglush Electric Vehicle, wani kamfanin EV na cikin gida mallakin ‘yan asalin jihar. Sanarwar ta ƙara da cewa an tsara shirin ne domin bai…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutane tara a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane tara a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan bindiga sun kashe mutane tara ciki har da ɗan banga (Forest Guard) da mace mai juna biyu a ƙaramar hukumar Bakori na jihar Katsina. Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Bakori Hon Abdulraham Ahmad Kandarawa ya sanar da haka a hira da manema labarai a Katsina. Ya bayyana cewa 'yan bindigan sun shiga ƙauyen Gidan Wawu da ke mazaɓar Guga inda suka kashe mutanen tare da raunata mutane biyar da yanzu haka suna asbiti suna amsar magani. Kandarawa ya ce tuni aka yiwa waɗanda suka rasu sutura. Ya Kuma bayyana cewa bincike da…
Read More