ukarofi

12560 Posts
Kano: APC ta tabbatar da Tsamiyar Kara a matsayin ɗan takarar Gezawa

Kano: APC ta tabbatar da Tsamiyar Kara a matsayin ɗan takarar Gezawa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jam’iyyar APC ta tabbatar da Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara a matsayin ɗan takararta na kujerar Majalisar Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Gezawa a zaɓen 2027. Wakilan jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Ahmad Haruna Bichi tare da jami’an uwar jam’iyyar APC ta jihar Kano, wakilan hukumar zaɓe ta ƙasa, jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki ne suka shaida tabbatar da takarar tasa. An gudanar da taron ne ranar Laraba a harabar sakatariyar APC ta Gezawa. Da yake jawabi bayan tabbatar da shi, Hon. Tsamiyar Kara ya gode wa Allah bisa wannan nasara tare da bayyana…
Read More
Kamfanin Meta ya janyo cece-kuce bayan ɗaukar injiniyan AI tare da sallamar ma’aikata 8,000

Kamfanin Meta ya janyo cece-kuce bayan ɗaukar injiniyan AI tare da sallamar ma’aikata 8,000

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin Meta ya shiga cikin cece-kuce bayan da ya sallami dubban ma’aikata, tare da zuba jari mai yawa wajen ɗaukar ƙwararren masani a fannin fasahar ƙirƙirar basira ta na’ura mai kwakwalwa, wato Artificial Intelligence (AI). Rahotannin da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna cewa kamfanin ya sallami kusan ma’aikata 8,000 a rana guda da kuma ƙaddamar da sabon tsarin AI ɗinsa mai suna Muse, lamarin da ya haddasa muhawara kan yadda fasahar AI ke ƙara maye gurbin ayyukan mutane. Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun bayyana cewa wannan…
Read More
Yadda Tinubu ke tallata Nijeriya ga masu zuba jari na duniya

Yadda Tinubu ke tallata Nijeriya ga masu zuba jari na duniya

Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana abin da mutane da dama suka riga suka fahimta lokacin da ya shaida wa manema labarai a wajen Taron Shugabannin Kamfanoni na Afirka da aka gudanar a Kigali na ƙasar Rwanda cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na taka rawar gani wajen tallata Nijeriya ga masu zuba jari na duniya. “Abin farin ciki game da Shugaban ƙasa shi ne bai gajiya wajen tallata Nijeriya ba. Shi ne babban mai tallan ƙasar nan,” inji Oyedele. Tun bayan hawansa mulki, Shugaba Tinubu ya ɗauki Nijeriya zuwa gaban masu…
Read More
Gwamna ya lashe tikitin takarar gwamna na APC a Jihar Gombe

Gwamna ya lashe tikitin takarar gwamna na APC a Jihar Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI GOMBE Gombe Jam’iyyar APC ta bayyana Jamilu Ishiaku Gwamna a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Gombe domin zaɓen shekarar 2027, bayan kammala zaben fidda gwani da aka gudanar a faɗin jihar. Da yake sanar da sakamakon, shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na APC, Sanata Sani Abubakar Danladi, ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen ne cikin bin ƙa’idojin dokar zaɓe ta 2022 da kuma jagororin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC, tare da bin tsarin jam’iyya. Ya ce jimillar masu kaɗa ƙuri’a da aka tantance sun kai 556,081 a…
Read More
Yadda malami ɗaya ke koyar da yara fiye da 100 a Bauchi

Yadda malami ɗaya ke koyar da yara fiye da 100 a Bauchi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Fiye da yara 100 ne suke karatu a gindin bishiyoyi tun bayan iska ta rushe ginin azuzuwan makarantar Nomadic ta Kondawa da ke ƙaramar hukumar Jama'are a jihar Bauchi. Shugaban Yakubu Ƴanmiɗi ya bayyanawa Blueprint Manhaja cewa tun bayan rugujewar makarantar shekaru shida da suka gabata, shi kaɗai yake yake koyar da ɗalibai sama da 100 a ƙarƙashin bishiyoyi. Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al-umma (CITAD) a yau Alhamis, ta kai ɗauki makarantar ta hanyar rabon kayan karatu da kayan makaranta tare da samar da ƙarin malamai uku, yayin da masu ruwa da tsaki…
Read More
CITAD za ta horar da mata 15,000 a Arewacin Nijeriya kan ilimin fasahar sadarwa

CITAD za ta horar da mata 15,000 a Arewacin Nijeriya kan ilimin fasahar sadarwa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Aƙalla mata 15,000 ne ake sa ran za su samu horo kan ilimin amfani da fasahar zamani, tsaro da tsabtace amfani da yanar gizo domin cike giɓin da ke ƙara faɗaɗa tsakanin Arewacin Najeriya da sauran sassan ƙasar nan a wannan zamani na ci gaban fasahar sadarwa. Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al'umma Centre for Information Technology Development (CITAD) ta bayyana cewa horaswar ta zama wajibi duba da yadda yankin Arewa ke ci baya a ɓangaren fasahar sadarwa da bayanai (ICT), wanda babu wata gagarumar cigaba da za a samu ba tare da shi…
Read More
Raɗɗa ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar APC

Raɗɗa ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar APC

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jam'iyar APC ta tabbatar wa gwamnan jihar Katsina da zama ɗan takarar jam'iyar a zaɓen 2027. Shugaban kwamitin zaɓen yan takarar daga uwar jam'iyar APC Dr Muhammad Maccido ya bayyana haka a Katsina lokacin da ya ke gabatar da gwamnan a gaban dubban ya'yan jam'iyar. Tunda farko kafin ƙaddamar da gwamnan sai da shugaban kwamitin ya miƙa shaidar takara ga yan takarar kujerar majalisar jiha,ta ƙasa da ta dattijai waɗanda suka sami nasarar hayewa zuwa takarar a ƙarƙashin jam'iyar APC. A jawabin sa shugaban kwamitin sasanci kuma tsohon gwamnan jihar Rt Hon Aminu Bello Masari…
Read More
Dambe wasar maza, kowwayyi hankali ya barka: Waiwaye kan tarihin kiɗan dambe na Dan’anace (4)

Dambe wasar maza, kowwayyi hankali ya barka: Waiwaye kan tarihin kiɗan dambe na Dan’anace (4)

Daga IBRAHIM MUHAMMAD  (Danmadamin Birnin Magaji) Manazarta: Bunza, A. (2008) Gadon Feɗe Al’ada, Tiwal Nigerian Limited Lagos Dangambo, A. (2008) Rabe-Raben Adabin Hausa / Sabon Tsari, Amana Publishers, Kano Gusau, S. (1996) Makaɗa da Mawaƙan Hausa, Fisbas Media Serɓices, Kaduna Gusau, S. M. (1995) Dabarun Nazarin Adabin Hausa Fisbas Media Serɓices, Kaduna  Gusau, S. M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka Benchmark Publishers Limited, Kano Gusau, S. M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanonin Waƙoƙin Baka Na Hausa. Century Research and Publishing Company Limited, Kano. Gusau, S. M. (2011) Tarihi da Hanyar Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya. A Cikin Waƙoƙin Baka Na…
Read More
PDP ta tsayar da Hamisu Gambo takarar majalisar dattijai a Katsina

PDP ta tsayar da Hamisu Gambo takarar majalisar dattijai a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jam'iyar adawa na PDP a Katsina ta tsayar da Hon Hamisu Gambo a matsayi ɗan takarar jam'iyar a kujerar majalisar dattijai mai wakiltar Katsina ta tsakiya. Shugaban kwamitin da Uwar jam'iyar ta ƙasa ta turo Katsina domin shirya zaɓen fidda ɗan takarar Sanata Yakubu Lado ɗan marke ya sanar haka. Ya ce Hon Hamisu Gambo wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ya zama ɗan takara ba tare da wani hamayya ba irin girmamawa da ya'yan jam'iyar ke masa. Danmarke ya bayyana Hamisu Gambo a matsayin ɗan siyasa mai mutunci da farin jini a idon ya'yan jam'iyar…
Read More
Gwamnatin Kano ta bada hutun babbar sallah ga makarantu

Gwamnatin Kano ta bada hutun babbar sallah ga makarantu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da ranar fara hutun babbar sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar. A cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kai na ma’aikatar, Misbahu Yakasai, ya fitar ranar Laraba, an bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana za su fara hutu daga ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, 2026, sannan su koma makaranta ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, 2026. Sanarwar ta kuma ce makarantun je ka dawo za su tafi hutun sallah daga ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2026,…
Read More