ukarofi

12559 Posts
2027: Masu sharhi sun yi hasashen takarar Tinubu/Shettima, Atiku/Amaechi, Jonathan/Lamido da Obi/Kwankwaso

2027: Masu sharhi sun yi hasashen takarar Tinubu/Shettima, Atiku/Amaechi, Jonathan/Lamido da Obi/Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Masu sharhin siyasa na matakin ƙasa sun fara hasashen yadda manyan jam’iyyun siyasa za su fito da tikitin takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2027. A cewar masu sharhin, ana hasashen APC za ta sake tsayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Mataimakinsa Kashim Shettima, yayin da PDP za ta iya fito da tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan tare da Sule Lamiɗo. Haka kuma an yi hasashen cewa jam’iyyar NDC za ta iya tsayar da Peter Obi tare da Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da ADC za ta iya bai wa Atiku Abubakar…
Read More
Sai na bindige duk duk wanda ya ɗauki bidiyona a bakin aiki, inji wani ɗan sanda

Sai na bindige duk duk wanda ya ɗauki bidiyona a bakin aiki, inji wani ɗan sanda

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani mutum mai suna Newton Isokpehi, wanda ya bayyana kansa a matsayin jami’in Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya mai shekara 26 yana aiki, ya yi barazanar kashe duk wanda ya ɗauke shi bidiyo yayin da yake bakin aiki. Barazanar ta fito ne a cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda mutumin ya kuma yi kalamai masu zafi kan jama’a da kuma duk wani babban jami’i da yake zargin ya bayar da umarnin a riƙa ɗaukar jami’an ’yan sanda bidiyo yayin aiki. Isokpehi ya yi kalaman nasa ne da Turancin Pidgin, kafin daga bisani…
Read More
Ku kare kanku daga ta’adannci – Gwamnatin Tarayya

Ku kare kanku daga ta’adannci – Gwamnatin Tarayya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mai Bai Wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu Shawara Na Musamman Kan Yaɗa Manufofi da Sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a sassan ƙasar nan duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta. Bwala ya ce, Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya bai wa ’yan ƙasa damar kare kansu idan aka kai musu hari, musamman idan rayuwarsu na cikin haɗari. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba, yayin da yake tsokaci kan hare-haren da suka faru a aauyen Esiele da ke…
Read More
Kwankwaso na yi wa Tinubu aiki a ɓoye gabanin 2027 — Sanusi Bature

Kwankwaso na yi wa Tinubu aiki a ɓoye gabanin 2027 — Sanusi Bature

Daga RABIU MUHAMMAD a Kano Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya zargi tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu aiki a ɓoye domin shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027. Sanusi Bature ya kuma bayyana cewa haɗakar siyasa tsakanin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba za ta yi tasiri ba, musamman a jihar Kano. Da yake magana a wata hira da ya yi a shirin Morning Show na tashar Arise Teleɓision ranar Laraba, Bature ya ce Jam’iyyar NNPP ba ta da ƙarfin da za ta iya…
Read More
Rikici ya mamaye zaɓen fidda gwanin APC a Igabi, Sani Dakaci ya yi watsi da zargin yarjejeniyar sulhu

Rikici ya mamaye zaɓen fidda gwanin APC a Igabi, Sani Dakaci ya yi watsi da zargin yarjejeniyar sulhu

Daga ZUBAIRU JIBIA a Abuja Zaɓen fidda gwani na kai tsaye (Direct Primaries) na Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) domin tantance ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazaɓar Igabi a jihar Kaduna ya fuskanci ce-ce-ku-ce, zarge-zargen rashin adalci da kuma rikicin cikin gida, lamarin da ya jefa mambobin jam’iyyar cikin ruɗani. Zaɓen wanda ya haɗa da fafatawa tsakanin ESɓ Hon. Dr. Sani Abdulkadir Dakaci da Hon. Hussain Muhammad Jalo, ya gamu da matsaloli masu yawa da kuma rashin ingantaccen tsari a wurare daban-daban da aka tsara gudanar da zaɓen a ƙaramar Hukumar Igabi. Binciken da aka gudanar…
Read More
Hajjin bana: Za a fassara huɗubar Arfa da Hausa da Yoruba da wasu yaruka 33 – Saudiyya

Hajjin bana: Za a fassara huɗubar Arfa da Hausa da Yoruba da wasu yaruka 33 – Saudiyya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumomin Saudiyya sun sanar da cewa za su fassara huɗubar ranar Arafat ta aikin Hajjin shekarar 2026 zuwa harsuna 35 na duniya ciki har da Hausa da Yarbanci domin musulmi a sassan duniya su amfana da saƙon huɗubar. Shugaban kula da harkokin addini na Masallacin Harami da Masallacin Annabi, Sheikh Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais ne ya bayyana hakan yayin da mahajjata ke ci gaba da isa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana. Ya ce huɗubar ranar Arafat da Sheikh Ali bin Abdulrahman Al-Hudhaifi, limami kuma mai wa’azi a Masallacin Annabi da ke…
Read More
Marasa hankali ne kawai ke tunanin ina yi wa Tinubu aiki – Kwankwaso 

Marasa hankali ne kawai ke tunanin ina yi wa Tinubu aiki – Kwankwaso 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta zargin cewa yana yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu aiki a ɓoye domin tazarcensa a zaɓen 2027. Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Global Tɓ, inda ya ce mutane marasa hankali ne kawai za su yarda da irin wannan zargi.  Ya ce shi da magoya bayansa suna aiki ne kawai domin jam’iyyar NDC, ba domin wata jam’iyya ko dan takara ba. Ya ƙara da cewa duk da cewa Tinubu babban abokinsa ne tun shekaru da dama, hakan ba yana…
Read More
Sabon masallacin Sarkin Zazzau ya rufta har ya danne mutane uku

Sabon masallacin Sarkin Zazzau ya rufta har ya danne mutane uku

Daga MOH’D BELLO HABIB a Zariya Akalla leburori uku ne suka jikkata sakamakon rushewar wani ɓangare na babban masallacin Juma’a da ake ginawa a Zariya da ke jihar Kaduna na Sarkin Zazzau. Wasu shaidu da suka ga abin da ya faru sun ce an yi gaggawar kai waɗanda suka samu raunuka zuwa wani asibiti da ke Zariya domin samun kulawar likitoci. Manhaja ba ta samu jin ta bakin injiniyan da ke kula da aikin ginin ba, domin wasu daga cikin mutanen da ke wurin sun bayyana cewa yana cikin waɗanda suka yi gaggawar kai waɗanda suka jikkata asibiti. Kakakin Masarautar…
Read More
Nijeriya ba za ta rushe ba duk da ƙalubalenta – Gowon

Nijeriya ba za ta rushe ba duk da ƙalubalenta – Gowon

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya bayyana cewa Nijeriya ba za ta rushe ba duk da irin ƙalubalen siyasa, tattalin arziki da matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu. Gowon ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai shafi 859 mai taken My Life of Duty and Allegiance. Tsohon shugaban ƙasar, wanda ya cika shekaru 91 a watan Fabrairu, ya kuma gargadi ƴan siyasa kan abin da ya kira siyasar “a mutu ko a yi rai,” yana mai cewa…
Read More
Kano: APC ta tabbatar da Tsamiyar Kara a matsayin ɗan takarar Gezawa

Kano: APC ta tabbatar da Tsamiyar Kara a matsayin ɗan takarar Gezawa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jam’iyyar APC ta tabbatar da Hon. Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara a matsayin ɗan takararta na kujerar Majalisar Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Gezawa a zaɓen 2027. Wakilan jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Ahmad Haruna Bichi tare da jami’an uwar jam’iyyar APC ta jihar Kano, wakilan hukumar zaɓe ta ƙasa, jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki ne suka shaida tabbatar da takarar tasa. An gudanar da taron ne ranar Laraba a harabar sakatariyar APC ta Gezawa. Da yake jawabi bayan tabbatar da shi, Hon. Tsamiyar Kara ya gode wa Allah bisa wannan nasara tare da bayyana…
Read More