ukarofi

12559 Posts
Kotu ta ci gaba da sammacin kama tsohuwar minista, Sadiya Farouƙ

Kotu ta ci gaba da sammacin kama tsohuwar minista, Sadiya Farouƙ

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Babbar Kotun Tarayya da ke Apo a Abuja ta ci gaba da tabbatar da sammacin kama tsohuwar Ministar Harkokin Jin ƙai da Agaji, Sadiya Umar Farouƙ, kan zargin almundahanar kuɗi har dala miliyan 1.3 da kuma naira miliyan 746.7. Mai shari’a Jude Onwuegbuzie ne ya bayyana a ranar Litinin cewa sammacin kama da kotun ta bayar tun ranar 16 ga Afrilu, 2026, zai ci gaba da aiki har sai an gurfanar da ita a gaban kotu. Hukumar EFCC na tuhumar Sadiya Farouƙ tare da Bashir Nura Alkali da Sani Nafiu Mohammed kan zarge-zargen haɗa…
Read More
Desmond Elliot ya janye daga zaɓen fidda gwanin APC na Majalisar Dokokin Legas

Desmond Elliot ya janye daga zaɓen fidda gwanin APC na Majalisar Dokokin Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar Surulere I, Desmond Elliot, ya sanar da janyewarsa daga zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC na kujerar majalisar dokokin jihar. Desmond Elliot ya bayyana hakan ne bayan isa filin wasa na Paddington Mini Stadium tare da magoya bayansa, inda ya zargi jami’an gudanar da zaɓe da hana yawancin magoya bayansa shiga wajen kaɗa ƙuri’a. Da yake magana da manema labarai, ɗan majalisar ya ce ya yi ƙoƙarin roƙon jami’an zaɓe da su bai wa magoya bayansa damar shiga wurin zaɓen, amma ba a saurare shi ba. Tun da…
Read More
Tirela ta halaka ‘yar sanda da wani mutum a Gombe

Tirela ta halaka ‘yar sanda da wani mutum a Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a yankin Sabuwar Mile 3 da ke kan hanyar Gombe zuwa Yola ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, ciki har da wata jami’ar ’yan sanda, tare da jikkatar wasu da dama. Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, lokacin da wata babbar mota ƙirar DAF wadda ke ɗauke da buhunan hatsi, ta yi hatsari ta kuma kutsa cikin babura uku, masu tafiya a ƙasa da kuma wasu shaguna da ke gefen hanya. Binciken farko da rundunar ’yan sanda ta gudanar ya nuna cewa direban motar ya yi…
Read More
Juyin mulki: An shirya kutsa wa Fadar Shugaban ƙasa ta ƙofar motocin gaggawa – Wanda ake tuhuma

Juyin mulki: An shirya kutsa wa Fadar Shugaban ƙasa ta ƙofar motocin gaggawa – Wanda ake tuhuma

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD A wata shari’a mai cike da zarge-zarge a Babban Kotun Tarayya da ke Abuja, wani wanda ake tuhuma da hannu a shirin juyin mulki ya bayyana yadda ake zargin wasu suka shirya kutsawa Fadar Shugaban ƙasa ta hanyar amfani da ƙofar shigar motocin gaggawa, wato ambulance entrance, a wani ɓangare na abin da ake zargi da yunƙurin kifar da gwamnati. Wannan bayani ya fito ne a zaman kotu na ranar Laraba a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, inda aka gabatar da shaidar bidiyo da ke da alaƙa da ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma, Zekeri Umoru.…
Read More
Tinubu ya umarci hukumomin gwamnati su rungumi tsarin aiki da fasahar zamani

Tinubu ya umarci hukumomin gwamnati su rungumi tsarin aiki da fasahar zamani

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zamanin tafiyar da aikin gwamnati cikin jinkiri da dogaro da takardu na hannu ya kamata ya zama tarihi, yana mai jaddada cewa dole ne Nijeriya ta rungumi tsarin aiki mai sauri, gaskiya da amfani da fasahar zamani wajen gudanar da mulki. Saboda haka, shugaban ƙasar ya umarci dukkan Ma’aikatu, Sassa da Hukumomin Gwamnati (MDAs) da su ƙara zurfafa amfani da tsarin dijital a dukkan harkokin gudanar da ayyukansu. Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da Taron ƙasa da ƙasa kan Aikin Gwamnati na 2026 da aka gudanar…
Read More
Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon Shugaban JAMB

Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon Shugaban JAMB

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon magatakardan Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta ƙasa (JAMB), inda zai gaji Farfesa Is-haƙ Oloyede wanda wa’adinsa na zangon mulki na biyu zai ƙare a ranar 31 ga Yuli, 2026. Farfesa Aina, wanda zai cika shekaru 40 a watan Yulin 2026, fitaccen masani ne a fannin ilimi da tsarin fasaha, tare da gogewa mai yawa kan tsarin gudanar da jarabawar ƙasa, fasahar zamani da gyaran hukumomin gwamnati. Ya yi digirin farko na Bachelor of Engineering a fannin Computer Systems Engineering daga…
Read More
2027: Dan uwan Fubara ya sayi fom ɗin takarar gwamna a NDC

2027: Dan uwan Fubara ya sayi fom ɗin takarar gwamna a NDC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sa’o’i kaɗan bayan gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara, ya janye daga takarar gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2027, wani ɗan siyasa mai ɗauke da sunan Fubara ya shiga fafatawar neman kujerar ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC). Sabon ɗan takarar, mai suna Blessing Fubara Snr., ya karɓi fom ɗin tsayawa takara da nuna sha’awa na jam’iyyar domin neman kujerar gwamnan jihar Ribas a zaɓen 2027. Blessing Fubara ya karɓi fom ɗin ne a hedikwatar jam’iyyar NDC ta ƙasa da ke Abuja ranar Laraba, lamarin da ya sake tayar da sabon zance a siyasar…
Read More
NAHCON ta kammala jigilar maniyyatan 2026 akan kari

NAHCON ta kammala jigilar maniyyatan 2026 akan kari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanar da kammala jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya, domin gudanar da aikin Hajjin 2026 akan kari. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta bayyana cewa an fara jigilar maniyyatan ne tun ranar 3 ga Mayu, 2026, sannan aka kammala aikin da jirgin Maɗ Air na ƙarshe da ya ɗauki maniyyatan jihar Zamfara daga filin jirgin saman Gusau. NAHCON ta ce an gudanar da jimillar jirage 98 cikin kwanaki 18, inda ake gudanar da kusan jirage biyar a kullum yayin aikin jigilar. Nijeriya ta…
Read More
Zaɓukan APC: Wasu sun dara, wasu sun koka

Zaɓukan APC: Wasu sun dara, wasu sun koka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zaɓukan fidda gwani na Jam’iyyar ‘All Progressiɓes Congress’ (APC) da aka gudanar a sassa daban-daban na Niijeriya sun bar baya da ƙura, rikice-rikice, koke-koke, zarge-zargen maguɗi da murnar nasara daga ɓangarori mabambanta, yayin da jam’iyyar ke ƙoƙarin tsara dabarun tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. Yayin da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar suka samu tikitin takara cikin farin ciki da gagarumar nasara, wasu kuwa sun bayyana zaɓukan a matsayin “wasan kwaikwayo” da aka shirya domin fifita wasu ‘yan takara, lamarin da ya haddasa zanga-zanga da kuma barazanar ɗaukaka ƙorafe-ƙorafe zuwa matakin ƙasa. A wasu jihohi, an…
Read More
Masu more tallafin mai da canjin kuɗaɗe ke haddasa matsalar tsaro – Tinubu

Masu more tallafin mai da canjin kuɗaɗe ke haddasa matsalar tsaro – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya zargi waɗanda suka amfana da tsohon tsarin biyan tallafin man fetur da kuma tsari na farashin canjin kuɗaɗen waje daban-daban da hannu wajen ƙara ta’azzarar matsalar tsaro da yunƙurin tayar da zaune tsaye a Nijeriya bayan sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar. Tinubu ya kuma bayyana cewa wasu ƙungiyoyi masu ƙarfin faɗa a ji da suka amfana da damfara a harkar canjin kuɗaɗen waje da cin hanci a tsarin tallafin mai yanzu suna “fatan ya mutu” saboda manufofin da ya ƙaddamar tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023. Shugaban…
Read More