Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dan majalisar dokokin jihar Legas mai wakiltar Surulere I, Desmond Elliot, ya sanar da janyewarsa daga zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC na kujerar majalisar dokokin jihar.
Desmond Elliot ya bayyana hakan ne bayan isa filin wasa na Paddington Mini Stadium tare da magoya bayansa, inda ya zargi jami’an gudanar da zaɓe da hana yawancin magoya bayansa shiga wajen kaɗa ƙuri’a.
Da yake magana da manema labarai, ɗan majalisar ya ce ya yi ƙoƙarin roƙon jami’an zaɓe da su bai wa magoya bayansa damar shiga wurin zaɓen, amma ba a saurare shi ba.
Tun da farko dai an rawaito cewa Desmond Elliot ya bai wa shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, haƙuri kan duk wani abu da ka iya faruwa tsakaninsu a harkokin siyasa.
Jarumin Nollywood ɗin ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Your ɓiew na tashar TɓC, inda ya ce duk wata rashin fahimta da ta taso ba da gangan ba ce, tare da jaddada cewa har yanzu yana biyayya ga haɗin kan jam’iyya da cigaban mazabarsa.
Hakan na zuwa ne bayan Gbajabiamila ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taɓa nuna damuwa kan rahotannin sirri da ke danganta Desmond Elliot da rikicin shugabancin majalisar dokokin jihar Legas wanda ya kai ga tsige tare da dawo da Kakakin Majalisar, Mudashiru Obasa.
A ranar Laraba, magoya bayan Elliot sun gudanar da zanga-zangar lumana kafin daga bisani su fice daga wurin tare da shi.
Desmond Elliot ya ce ya yanke shawarar janyewa daga takarar ne domin kauce wa tashin hankali da zai iya janyo asarar rayuka.
“Ba zan bari a rasa rai saboda wannan zaɓe ba,” inji shi.
Rahotanni sun ce ba a kammala gudanar da zaɓen ba sakamakon tashin hankali da ya biyo bayan zargin hana wasu mambobin jam’iyyar shiga wajen zaɓen.
A cikin wani bidiyo da ya yi jawabi, Desmond Elliot ya nuna damuwa kan irin barazana da matsin lambar da shi da magoya bayansa suka fuskanta yayin zaɓen.
“Ina sanar da janyewata daga wannan takara a hukumance. Ina yi wa kowa fatan alheri, na gode, Allah ya albarkace ku,” inji shi.
