Kotu ta ci gaba da sammacin kama tsohuwar minista, Sadiya Farouƙ

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Babbar Kotun Tarayya da ke Apo a Abuja ta ci gaba da tabbatar da sammacin kama tsohuwar Ministar Harkokin Jin ƙai da Agaji, Sadiya Umar Farouƙ, kan zargin almundahanar kuɗi har dala miliyan 1.3 da kuma naira miliyan 746.7.

Mai shari’a Jude Onwuegbuzie ne ya bayyana a ranar Litinin cewa sammacin kama da kotun ta bayar tun ranar 16 ga Afrilu, 2026, zai ci gaba da aiki har sai an gurfanar da ita a gaban kotu.

Hukumar EFCC na tuhumar Sadiya Farouƙ tare da Bashir Nura Alkali da Sani Nafiu Mohammed kan zarge-zargen haɗa baki wajen aikata laifi, cin amanar ofis da karkatar da kuɗaɗen jama’a.

A yayin zaman kotun, lauyan EFCC, Rotimi Jacobs (SAN), ya shaida wa kotun cewa an tsara zaman ne domin gurfanar da waɗanda ake tuhuma, amma tsohuwar ministar ba ta halarta ba kuma babu wani cikakken bayani kan rashin zuwanta.

Jacobs ya tunatar da kotun cewa a zaman da ya gabata ne aka bayar da sammacin kama Sadiya Farouƙ, wanda hakan ya sa ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma ya miƙa kansa ga EFCC domin biyayya ga umarnin kotu.

Lauyan ya roƙi kotun da ta soke sammacin kama wanda aka bayar kan ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma amma ta bar na Sadiya Farouƙ yana nan.

Ya kuma bayyana cewa lauyan Sadiya Farouƙ, Oladipo Okpesheyi (SAN), ya taɓa roƙon kotun ta ba shi wata guda domin gabatar da wacce yake karewa.

Sai dai Jacobs ya nuna takaicinsa cewa duk da alƙawarin da aka yi, har yanzu ba a gabatar da ita a gaban kotun ba.

Da kotun ta tambayi lauyan karewar dalilin rashin halartar Sadiya Farouƙ, ya bayyana cewa tana ƙasar Masar domin karɓar magani.

“Ana kula da lafiyarta a wani asibiti da ke Masar, kuma likitoci sun ce ba ta da ƙarfin halartar kotu a yanzu,” inji shi.

Ya ƙara da cewa akwai rahoton likita da ya samu a wayarsa wanda ya nuna cewa tana buƙatar kusan wata biyu kafin ta murmure.

Sai dai Mai shari’a Onwuegbuzie ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake neman jinkirta shari’ar akai-akai.

“A zaman da ya gabata an yi wa kotu alƙawarin gabatar da wacce ake tuhuma. Ba zai yiwu a ci gaba da bayar da dogon lokaci ba,” inji alƙalin.

Ya ƙara da cewa: “Ba zan amince da jinkiri marar amfani a kotuna ba. Zan bayar da ɗan gajeren lokaci, sannan ku je ku kawo ta, ko da kuwa tana cikin keken guragu. Idan kuma ba ta zo ba, kotu za ta ɗauki matakin da ya dace.”

Daga nan ne kotun ta tabbatar da cewa sammacin kama Sadiya Farouƙ zai ci gaba da aiki, tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 8 ga Yuni, 2026 domin gurfanar da waɗanda ake tuhuma.

A kwanakin baya ne EFCC ta ayyana tsohuwar ministar a matsayin wacce ake nema ruwa a jallo kan zarge-zargen karkatar da kuɗaɗen jama’a da cin amanar ofis.

By ukarofi