Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa da shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyarmu.
Kamar yadda muka shafe makonni biyu muna tattaunawa kan wannan darasi mai muhimmanci. A wannan makon ma za mu sake ɗibo wani ɓangare ne daga wannan tsiro mai tarin albarka.
Ana iya amfani da man jojoba ta hanyoyi da dama, waɗanda ke iya taimaka wa wajen inganta fata tare da bata lafiya kan matsalolin ta da dama.
Jojoba oil na da matuƙar amfani a fannoni da dama:
1. A matsayin mai cire kayan kwalliya (makeup remover):
Masana fata sun sha faɗar cewa, kayan kwalliya da muke amfani da su a wannan zamani da yawansu fata ba ta jure zama da su na dogon lokaci, don haka suka bada shawarar kada a kuskura a kwanta da su. Kuma kada a wanke su da ruwa kawai, domin gujewa barin ragowar kayan kwalliyar wanda zai iya yiwa fata illa.
An so a yi amfani da wasu kayan goge Kwalliya don ganin an kawar da kwalliyar baki ɗaya.
Man jojoba kuwa ya shiga a cikin wannan jeri na kayan da ke goge kwalliyar yadda ya kamata tare kuma da samar mata kariya daga ababen da aka yi amfani da su a kayan kwalliyar masu ƙarfi da ka iya cutar da fata.
2. A matsayin sabulun tsaftace fuska (cleanser):
Koda mutum bai yi kwalliya ba yana daga cikin kwalliya da kuma lafiyar fata goge ta da kayan da aka yi musamman don fitar da kowacce irin datti daga fuska. Wannan zai taimaka wurin hana kwayoyin cuta da aka kwaso samun gurin zama da har za su samu damar yin illa.
3. A matsayin man shafa wa jiki (body moisturizer):
Kamar yadda muka ambata a farkon darasin, man na jojoba na da matuƙar tasiri ga lafiya da sheƙin fata. Don haka mayar da shi man shafawa zai kawo sakamako mai kyau.
Abin tambayar anan dai shi ne, shin ya za a iya sarrafa man na jojoba don yin waɗannan abubuwa da muka ambata? Amsar ku tara a mako na gaba.
