“A kullum burina shi ne in ga na taimaka wa jama’a”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Hajiya Maimuna Idi fitacciyar ƴar siyasa ce kuma ƴar kasuwa, mai fafutukar inganta rayuwar mata, da ƙananan yara, Ta riƙe muƙamai daban-daban a ciki da wajen Jihar Gombe, musamman a ɓangarorin cigaban al’umma da siyasa. Jajircewarta da gwagwarmayarta ne ya sa aka yi mata naɗin sarautar Jarumar Kaltungo, matsayin da ya ƙara kwarjantata a idanun al’umma, da ƙara mata girma da martaba. A ganawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, jarumar ta bayyana masa burinta a siyasa, da fatan da take da shi nan gaba a siyasar Jihar Gombe.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.
JARUMA: Sunana Hajiya Maimuna Idris, kuma ni ce mai riƙe da sarautar Jarumar Kaltungo. Ni ‘yar asalin Jihar Gombe ce daga ƙaramar Hukumar Kaltungo. Ni ‘yar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa. Mai gwagwarmayar samar da sauyi a rayuwar mata da iyali baki ɗaya.
Ki ba mu tarihin rayuwarki.
Tun tasowa ta na samu gata na kulawar iyaye da ƴan’uwa, musamman a ɓangaren tarbiyya da ilimi. Na fara karatuna na boko a wata makarantar firamare ta Kalaring Primary School da ke Kaltungo. Na yi karatun sakandire a Alkaleri dake Jihar Bauchi. Daga nan na je Kwalejin Nazarin Harkokin Kasuwanci ta College of Business Studies a garin Potiskum dake Jihar Yobe, inda na samu shaidar Diploma a ɓangaren ilimin Raya Al’umma wato Community Deɓelopment. Ina kammalawa ne sai na wuce Jami’ar Maiduguri, inda na yi karatun digirina na farko akan ilimin zamantakewa da tarihin wanzuwar ɗan’adam (Sociology and Anthropology).
Bayan na gama makaranta, na fara aikin gwamnati a matakin ƙaramar hukuma, daga bisani kuma na yi canjin matakin aiki zuwa ƙarƙashin Gwamnatin Jiha. Na ajiye aiki ina matsayin Muƙaddashiyar Darakta a Ma’aikatar Kula da Harkokin ƙananan Hukumomi a 2024. Daga nan ne kuma na shiga harkokin siyasa.
Wacce irin rayuwa ki ka taso a cikin ta wacce yanzu ki ke godewa Allah da ki ka samu wannan ilimi da tarbiyya a rayuwarki?
Na tashi a cikin rayuwa da kulawa ta addinin Musulunci, na kuma samu kyakkyawar tarbiyya daga wurin iyayena. Na samu ilimi irin na addinin Musulunci da kuma ilimin zamani. Ina godiya ga Allah da ya bani iyaye nagari, waɗanda suka bani tarbiyya mai kyau, suka kuma tabbatar da samu ilimin addini da na zamani. Ina ƙara godiya ga Allah da na samu kaina a cikin mutanen kirki da abokan hulɗda nagari.
Yaya ki ke ganin bambanci a rayuwar da da yanzu game da sha’anin tarbiyyar iyali da girmama na gaba?
A gaskiya tarbiyyar iyali na da da yanzu akwai bambanci sosai, ko saboda wayewa ne ya sanya haka? Oho. A tasowarmu mun ga yadda iyalin dake da kula da tarbiyya, ke kasancewa cikin ladabi da biyayya, kuma ba sa ƙetare maganar babba. Amma a yanzu ba haka abin yake ba, matasa na nuna cewa su a yanzu rayuwar ƴanci suke yi.
Wanne abu ne ya taɓa faruwa da ke kina yarinya wanda ya canza miki tunani kan zaman rayuwa, kuma har yanzu ba ki manta ba?
Lokacin ina ƙarama na taso bana son darasin lissafi, sai da wani malaminmu ya gane duk lokacin da ya shigo aji sai na fara bacci, sai ya kirani ya tambayeni, me yake faruwa kullum ya shiga aji ina barci? Sai na fashe da kuka. A hankali ya rarrashe ni na yi shiru. Ya sake tambayata, sai na ce masa ba na son darasin lissafin ne. Tun daga wannan rana idan aka zo darasin lissafi sai malamin nan ya dawo da ni gaban aji ya zaunar da ni har ya gama darasi. Tun daga wannan lokacin duk koyarwa da ya yi sai ya tabbatar ina zaune a gaban aji. Kuma daga ƙarshe sai ya yi mini tambayoyi, ni kuma ganin ya sani a gaba sai ya zama duk lokacin darasin lissafi ina zama cikin natsuwa sosai. A ƙarshe dai har ya zama a duk darussan da muke yi ba wanda na fi iyawa da fahimta kamar darasin lissafi, wannan shi ya yi min jagora har na kai ga jami’a ban sake samun matsala da lissafi ba.
Yaya ki ke ganin bambancin da ake nunawa a baya game da tarbiyyar ƴaƴa mata da basu ilimi?
A gaskiya a baya can ba kowacce ‘ya mace ce ake yarda a kai ta makaranta ba, sai da kawai a ce ‘ya mace gidan mijinta shi ya fi mata alheri, sai ‘yan tsiraru da ake samu a kai su makaranta. Amma yanzu abubuwa sun canza, ana samun ‘ya’ya mata sosai a makarantu, a wasu makarantun ma mata sun fi maza yawa. A nan Gombe muna da mata masu ilimi, da suka yi karatu har zuwa matakin Farfesa, akwai ƙwararru daban-daban da suke bayar da gudunmawa a harkar cigaban jihar nan.
Kina ganin a yanzu da aka samu cigaba a rayuwa, mata suna samun ƴanci da walwala kamar maza?
Duk da dai yanzu ana damawa da mata a kowane harka, Amma fa mata basu da yanzu sosai kamar maza
Wanne irin goyon baya ƴan’uwanki maza da waɗanda ku ka taso tare suka baki, wajen tallafi da gudunmawa a rayuwarki?
Goyon baya da ‘yan uwana maza da waɗanda muka taso dasu suka bani shine, a kullum suna bani shawaran ki yi karatu kada kice don kinyi aure kice ai bazaki ci gaba da karatu, a kullum kuma suna ‘encouraging’ ɗina a harkan rayuwa da neman na kanki.
Wanne mataki ki ka taka a rayuwarki da ya kawo ki matsayin da ki ke a halin yanzu?
Mataki na farko shine karatu da na yi, mataki na biyu yanayin alakana da jama,a, mataki na uku mutunta jama,a da son jama,a da kuma tallafa wa jama’a.
Ba mu labarin yadda ki ka samu sarautar Jarumar Kaltungo da yanzu ki ke riƙe da ita?
Jarumta ta ce da aiki tuƙuru da nake yi don cigaban al’umma ya sa aka bani wannan sarauta ta Jarumar Kaltungo. Ni a kullum burina shi ne in ga na taimaka wa jama’a, don haka duk abin da zan samu a rayuwata zan yi ƙoƙari na ga na kai garina don wasu su amfana da shi. Idan na samu dubu ɗaya to, a cikin zan kashe 400 ne, zan kuma tabbatar da 600 da ya rage zan raba wa mutum biyu ko uku. Duk abin da na samu ba na iya cinyewa ni kaɗai sai na bai wa wasu su ma su taɓa. Ni mace ce mai son zumunci da kishin ƙasata, a duk inda na je ina alfahari da inda na fito.
Shin kin taɓa riƙe wani muƙami na siyasa a rayuwarki?
Na taɓa riƙe muƙamin siyasa. Yanzu haka ni mamba ce a Majalisar Yaƙin Zaɓen Shugaban ƙasa Tinubu (PCC 2027), a ƙarƙashin masu ƙarfafa gwiwar masu zaɓe. Na kuma riƙe muƙamin Mataimakiyar Sakatare a Kwamitin Yaƙin Neman Sake Zaɓen Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa a Babban Zaɓen da ya gabata. Na kuma zama deliget a Babban Zaɓen 2023.
Wane ne ubangidanki a siyasa, kuma wanne cigaba ya kawo a rayuwarki?
Babban ubangidana shi ne Mai Girma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kawo mini cigaba ta harkar siyasa da yawa a rayuwata. Duk wani abu da na zama a siyasa shine dalili. Ina godiya kwarai ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya Danmajen Gombe na farko. Allah Ya sa ya gama da duniya lafiya, Allah ya biya mishi dukkan buƙatunshi duniya da lahira.
Wacce rawa mata a Jihar Gombe suke takawa da yake kawo wa sauran mata cigaba?
A gaskiya mata manya da ƙanana na wannan jiha suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauye-sauye a rayuwar sauran matan Jihar Gombe. Duk a cikin mu kowacce burinta shi ne duk wata dama da aka samu za ta yi ƙoƙarin ganin an sa mata a ciki. Yadda mata suke taka rawar gani a siyasa, yana bai wa mata sha’awa. Shi ya sa za ka ga wacce a baya take ƙyamar siyasa yanzu ita ma ta fito ana damawa da ita. Mu matan Jihar Gombe tsintsiya ɗaya maɗaurinki ɗaya muke. Duk wata mace a Jihar Gombe da ta samu wani abin alheri tana son wata ‘yar’uwarta ma ta samu.
Shin kina ganin ƴan siyasar Jihar Gombe suna tallafa wa cigaban mata?
Babu shakka muna samun kulawa da goyon baya daga wajen ýan’uwanmu maza ‘yan siyasa na Gombe, suna tallafa mana ƙwarai da gaske, musamman wajen samar da tallafin inganta rayuwa ga mata, samar da ƙananan jari, ayyukan yi, da shigar da mu cikin ayyukan da suke tasowa na siyasa.
Idan aka ce za a baki dama wanne irin sauyi za ki kawo a Jihar Gombe?
Ba zan ce sauyi ba, sai dai na nemi a daɗa buɗa wa mata damarmaki, a bai wa mata matsayi sosai a siyasa. A gaskiya ana bai wa mata matsayi sai a gaskiya masayi sosai a siyasa, kuma muna yabawa tare da godiya. Sannan ba za mu gajiya da roƙon a ƙara ba su dama, idan ta samu.
Wacce mace ce ki ke kallo a matsayin madubin rayuwarki?
Madubin kallona a Jihar Gombe ita ce tsohuwar minista Hajiya Dr. Aishatu Jibril Dukku. Gaskiya rayuwar wannan baiwar Allah tana burge ni matuƙa, ina jinjina wa jajircewarta, sadaukarwarta, da kishin da take da shi na son cigaban Gombawa baki ɗaya.
Wacce shawara za ki bai wa matasan mata masu tasowa yadda za su zama abin alfahari ga al’ummarsu?
Shawarata ga matasan mata masu tasowa ita ce su zama masu haƙuri a duk inda suka samu kansu. Ba za ka cimma burinka ba idan baka zama mai haƙuri ba, su zama masu ladabi da biyayya ga na gaba da su. Da haka ne za su koyi aiki da kyau, kada su zama masu saurin fushi, kada su zama masu gaggawa a wurin neman abu. Sannan kuma su sa tsoron Allah a dukkan abin da suke yi.
Mene ne babban fatan ki nan gaba a rayuwa?
Babban fatana a rayuwa shi ne ni ma a ce na bar wani tarihi mai kyau a siyasata, ni ma kuma ya zama na taka rawa sosai a siyasa.
Mene ne saƙon ki na ƙarshe?
Sakona na ƙarshe, mu zauna da juna lafiya. Mu zama masu ƙoƙarin riƙe amana. Duk amanar da aka baka ka yi iya ƙoƙarinka ka riƙe shi bil haƙƙi da gaskiya. Tsoron Allah yana da muhimmanci sosai, mu yi ta ƙoƙarin kwatantawa.
Na gode.
Ni ma ina godiya ƙwarai da gaske.
