
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Masu muradin tsaya wa takarar sanata guda shida daga Kano ne suka janye muradunsu domin goya wa tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau baya yayin zaɓen 2027.
An ɗauki wannan mataki ne yayin wani babban zama da ya ƙunshi jiga-jigan ‘yan siyasar jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Da suke ganawa da manema labarai bayan zaman, ‘yan takarar — Usman Bala, Sha’aban Sharada, Muhammad Zango, Ɗan Yaro Yakasai, Abbas Sani Abbas, da Shehu Isa Direba, sun ce sun janye ne don haɗin kai da zaman lafiya a jihar.
A cewarsu, amince wa Shekarau wani bangare ne na aiki tare domin ƙarfafa haɗin kai a siyasance da kuma ciyarwa ɗorewar al’amura a jihar yayin tunkarar babban zaɓen 2027.
A nasa jawabin, tsohon gwamnan ya bayyana hakan ya biyo bayan nazari da shawarwari da aka yi tsakanin masu ruwa da tsaki.
Ya kuma nemi jin ra’ayoyin waɗanda suka halarci zaman, inda kowa ya bayyana amincewarsa da matakin.
Shekarau, wanda tsohon malami ne kuma ma’aikacin gwamnati, ya yi gwamna a jihar Kano daga shekarar 2003 zuwa 2011.
