Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
‘Yan bindiga sun yi wa matafiya kwanton ɓauna a kan babbar hanyar Magami-Dansadau a jihar Zamfara a yammacin yau, inda suka kashe mutane 30 a ɗaya daga cikin hare-haren da suka fi muni a wannan shekarar.
A cewar Jami’in hulda da jama’a na jami’an kare al’umma na Zamfara, Malam Abubakar Gummi wanda ya tabbatar da lamarin ga Blueprint Manhaja ya ce, maharan sun kai hari kan masu ababen hawa da wasu tsakanin Magami da Gusau, inda suka buɗe wuta kan motoci a wani kwanton ɓauna da suka shirya.
Malam Abubakar ya tabbatar da cewa fararen hula 21, mafarauta 8 na yankin, da kuma wani mai tsaron al’umma ɗaya sun mutu a harin.
Gummi ya ce jami’an tsaro da masu tsaron al’umma sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar bayan harin.
“A lokacin musayar wuta, an kashe ‘yan bindiga da dama,” in ji shi, duk da cewa bai bayar da ainihin adadin waɗanda suka mutu a harin ba.
Babbar hanyar Magami-Dansadau ta daɗe tana zama cibiyar ‘yan ta’adda a yankin Zamfara ta Kudu, inda ake yawan kai hare-hare kan matafiya, manoma, da ‘yan kasuwa duk da ayyukan da sojoji da al’umma ke gudanarwa a yankin.
Hanyar ta haɗa al’ummomi da dama na karkara zuwa Gusau, babban birnin jihar, wanda hakan ya sanya ta zama hanya mai mahimmanci amma mai haɗari ga zirga-zirga da kasuwanci.
Majiyoyin tsaro sun ce an gano gawarwakin waɗanda abin ya shafa kuma an kai su cibiyar lafiya da ke a Garin Magami, yayin da waɗanda suka tsira ke karɓar magani saboda raunukan da suka samu a lokacin harin.
Hakazalika, Gwamnatin Jihar Zamfara har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
