Jirgin yaƙin sojoji ya yi kuren halaka fararen hula da dama yayin farautar ‘yan bindiga a Neja

Spread the love

Wasu fararen hula da ba a tantance adadinsu ba sun rasa rayukansu sakamakon wani sabon harin bom ta sama da ake zargin sojoji suka kai a ƙauyen Guradnayi da ke kusa da Kusasu a Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Lamarin ya kara jefa al’umma cikin fargaba, yayin da ake ci gaba da samun rahotannin hare-haren jiragen yaki da suka yi sanadin mutuwar fararen hula a yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Najeriya.

Majiyoyi da dama sun shaida wa manema labarai cewa harin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi. Hotunan da aka samu daga wurin sun nuna mummunan barna da ba za a iya wallafawa ba.

“Lamarin ya faru da misalin karfe 5 na safe,” in ji Auta Awododo, wani mazaunin Kusasu, wanda ya ce akalla mutum 12 sun mutu a gidan wani dan uwansa da ke Guradnayi.

Ya ce daya daga cikin wadanda suka mutu shi ne dan dan uwansa.

“Mutum 12 aka kashe a gidansa,” in ji shi. “Sauran kuma mutanen Kusasu ne da suka tsere daga hare-haren ‘yan ta’adda.”

Mazauna yankin sun ce wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun ratsa kauyen ne a kan babura yayin da jiragen yaki ke binsu.

“Da farko jirgin ya jefa bam kusa da kogin Kusasu,” wani mazaunin yankin ya bayyana. “Sai kuma bam na biyu da aka jefa a Guradnayi.”

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

An kuma rawaito cewa an aika sakon neman karin bayani ga kakakin rundunar, Ehimen Ejodame, amma ba a samu amsar saƙonni da kiraye-kirayen da aka masa ba.

A shekarar 2022, wani jirgin yakin rundunar sojin sama ya kashe kananan yara shida a kauyen Kurebe, kamar yadda wani bincike ya nuna. Bayan watanni biyar, wani sabon harin jirgin soji ya sake kashe fararen hula takwas a kauyen.

By Babaji