Gwamnatin Kaduna ta ware biliyan N50 don yaƙi da ambaliya da zaizaya

Spread the love

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da rattaba hannu kan kwangiloli guda uku da kudinsu ya haura naira biliyan 50 domin aiwatar da manyan ayyukan dakile ambaliya da zaizayar kasa a yankunan Rigasa da Tudun Wada, Kawo da kuma cikin garin Zaria.

An gudanar da aikin ne ta hannun Hukumar Gudanar da Aikin ACReSAL ta jihar, domin magance matsalolin ambaliya da zaizayar kasa da ke barazana ga rayuka, kadarori da muhalli a sassan jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan kammala tsarin tantance kamfanoni da bayar da kwangila cikin gaskiya, an bai wa kamfanonin Mothercat Nigeria Limited, da CGC Nigeria Limited da Spectrum Engineering Limited damar gudanar da ayyukan.

Aikin yankin Rigasa da Tudun Wada wanda kamfanin Mothercat Nigeria Limited zai gudanar ya kai sama da kilomita 17, inda za a gina manyan magudanan ruwa na siminti tare da aiwatar da ayyukan da za su taimaka wajen dakile zaizayar kasa da kuma tafiyar da ruwa yadda ya kamata.

Hakazalika, aikin yankin Kawo wanda aka bai wa Spectrum Engineering Limited zai mamaye sama da kilomita uku, inda za a fadada hanyoyin ruwa tare da amfani da duwatsu da wasu hanyoyin kare kasa daga lalacewa.

Shi kuwa aikin yankin Zaria wanda kamfanin CGC Nigeria Limited zai aiwatar zai zarce kilomita 11, tare da gina hanyoyin kariya domin kare al’umma da kadarori daga illar ambaliya da zaizayar kasa.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ayyukan wani bangare ne na kokarinta wajen kare muhalli, magance sauyin yanayi da kuma tabbatar da dorewar ci gaba a fadin jihar.

Ta kara da cewa ana sa ran ayyukan za su taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyi, bunkasa harkokin tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al’ummomin da abin ya shafa.

Haka kuma gwamnatin ta jaddada kudurinta na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi jin dadin jama’a da kare muhalli a dukkan sassan jihar.

By Babaji