Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga biyar tare da ceto mutane 32 a Katsina

Spread the love

Gwamnatin Jihar Katsina ta sake samun nasara a sabbin hare-haren tsaro da ake kai wa ’yan bindiga a jihar da maƙwabtan yankuna.

Haɗaɗɗun jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen gudanar da farmaki kan Muhammadu Fulani, wani fitaccen jagoran ’yan bindiga da ke gudanar da ayyukansa a ƙananan hukumomin Matazu, Musawa, Kankia, Charanchi, da wasu sassan Jihar Kano.

A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Danmusa ya ce sabbin hare-haren da aka kai, jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga biyar tare da ƙwato makamai da kayan aikin da suke amfani da su wajen aikata laifuka.

Kayan da aka ƙwato sun haɗa da bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, harsasai guda 10, da babura guda 9 da ƙungiyar masu laifin ke amfani da su.

Daga cikin fitattun ’yan bindigar da aka kashe akwai Samagi makusanci ga Muhammadu Kachalla.

Haka kuma jami’an tsaron sun sami nasara ceto mutane 32 da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su, waɗanda suka haɗa da mata 10, maza tara, da yara 13.

Dr Ɗanmusa ya bayyana cewa,Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya sha nanata matsayan matsayin gwamnatin sa karara cewa ba za ta shiga tattaunawar sulhu da ’yan bindiga ba.

Haka kuma, hare-haren da ake kai wa Muhammadu Fulani na ci gaba da gudana. Jami’an tsaro na ci gaba da farautar sa wuraren da yayi kaka gida.

Kwamishinan sa yayi al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri domin taimakawa ayyukan da ake yi na yaƙi da masu aikata laifuka.

By ukarofi