2027: Atiku, Amaechi da Hayatu-Deen sun yanki fom ɗin takarar shugaban ƙasa a ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi sun mallaki fom a jam’iyyar ADC domin neman tsaya wa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

Haka ma Mohammed Hayatu-Deen, wanda shi ma ya mallaki fom ɗin, inda ya ci alwashin fifita harkar tsaro, samar da ayyuka da kuma nuna damuwa akan matsin tattalin arziƙi da al’ummar Nijeriya ke fuskanta.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya tabbatar da haka ga manema labarai a ranar Juma’a, inda ya ce ‘yan takarar uku tuni suka sayi fom ɗin.

Ana sayar da fom ɗin neman tsaya wa takarar shugaban ƙasa ne a jam’iyyar akan Naira miliyan 90.

Hayatu-Deen, wanda ya karɓi fom ɗin nasa daga Sakataren Shirye-shirye na Ƙasa, Chinedu Idigo a ranar Juma’a, ya bayyana cewa wajibi ne zaɓen 2027 a mayar da hankali akan dawo da ɗorewar tattalin arziƙi da inganta tsaron ƙasa.

A wata sanarwa, ɗan takarar shugaban ƙasar ya ce matsin tattali da rashin tsaro sune manyan ababen da suka fi zama barazana ga al’ummar Nijeriya don haka ya zama dole a ɗauki matakan magance su.

Jam’iyyar ADC ta ayyana 6 zuwa 13 ga watan Mayu a matsayin lokacin sayar da fom ɗin nuna muradin tsaya wa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da ke tafe.

By Babaji