
Jam’iyyar adawa ta NDC ta cimma matsaya a hukumance na mayar da tikitin takarar shugaban ƙasa na shekarar 2027 zuwa yankin Kudu na wa’adin shekara huɗu kacal, bayan haka kuma tikitin zai koma yankin Arewa.
Majiyoyin jam’iyyar sun tabbatar wa wakilinmu hakan yayin da babban taron ƙasa na jam’iyyar ke gudana a Abuja yau.
An cimma wannan matsaya ne a yayin taron da ake gudanarwa a Los Angeles Event Centre da ke kan titin Ahmadu Bello Way, inda wakilan jam’iyyar suka amince da shawarar bayan doguwar tattaunawa kan tsarin rabon tikitin takarar shugaban ƙasa.
Bisa ga yarjejeniyar, yankin Kudu ne zai fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027, tare da fahimtar cewa bayan wa’adin shekara huɗu guda ɗaya, tikitin zai koma yankin Arewa.
An ce an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da daidaito da kuma bai wa dukkan yankunan ƙasar damar karɓa-karɓar mulki cikin adalci a tsakanin shiyyoyin siyasar Nijeriya guda shida.
