Daga RABIU SANUSI
Shugaban ƙungiyar masu neman takara ta jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress, Hon. Haruna Yahaya Kadana ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da al’ummar jihar Kano da su ci gaba da haɗa kai da goyon bayan ‘yan takara masu nagarta, musamman ɗan takarar gwamna Malam Ibrahim Khalil domin tabbatar da sauyin da ake fata a jihar.
Kadana ya yi wannan jawabi ne yayin wani liyafar daren girmamawa da aka shirya domin tarbar Malam Ibrahim Khalil bayan dawowarsa daga ƙasar Saudi Arabia, inda ya kammala aikin Umrah cikin nasara kwanan nan.
Taron ya gudana ne da halartar manyan jami’an jam’iyya masu neman takara, matasa da ɗimbin magoya baya daga sassa daban-daban na jihar Kano.
A jawabin sa, Hon. Kadana ya bayyana cewa ƙaruwar karɓuwa da Malam Ibrahim Khalil ke samu a tsakanin al’umma, musamman matasa da wasu bangarori na jama’a na nuna cewa jam’iyyar ADC na da damar taka muhimmiyar rawa a siyasar Kano idan aka ci gaba da haɗin kai da gaskiya.
Ya jaddada buƙatar dukkan ‘yan takara a ƙarƙashin ADC daga gwamna, sanata, ‘yan majalisar tarayya da ta jiha da su fifita muradin jam’iyya sama da na kai, tare da mara wa wanda ya fi cancanta baya domin samun nasara.
“Abin da muke buƙata shi ne haɗin kai da fahimtar juna. Wasu daga cikinmu mun san waɗanda suka fi dacewa da jagoranci. Mara wa nagari baya ba laifi ba ne, illa gudummawa ce ga ci gaban jam’iyya da makomar Kano,” in ji Kadana.
Ya ƙara da cewa idan aka samu haɗin kai da jajircewa, ADC za ta iya zama jam’iyyar da za ta kawo sauyi mai ma’ana a fannin shugabanci da ci gaban jihar Kano.
A nasa ɓangaren, Malam Ibrahim Khalil ya tabbatar da cikakken biyayya ga jam’iyyar ADC, yana mai cewa shi da magoya bayansa ba su da niyyar sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya.
“Muna nan daram a ADC. Ba za mu fice daga jam’iyyar ba. Za mu ci gaba da haƙuri, jajircewa da addu’a har sai mun cimma burinmu na siyasa,” in ji shi.
“Idan kaga mun bar wannan jam’iyya sai dai idan yau hukumar zaɓe ta rushe ta to wannan ne zai sanya mu bar ta.
Ya ƙara da cewa nasara a siyasa na buƙatar haƙuri, gaskiya da sadaukarwa tare da kira ga magoya baya da su ci gaba da addu’a da jajircewa a tafiyar siyasa.
A ɓangaren sa shugaban jam’iyyar ADC a jihar Kano, Hon. Musa Shuaibu Ungoggo, ya bayyana cewa an amince da Balarabe Rufa’i da Hajiya Naja’atu domin kula da harkokin jam’iyyar a matakin jihar, har zuwa lokacin da za a kammala shari’o’in da ke gaban kotu.
Ungoggo ya kuma zargi ƙoƙarin mayar da Najeriya tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa hakan barazana ce ga ci gaban dimokuraɗiyya.
“Ba za mu amince da tsarin jam’iyya ɗaya ba. Dimokuraɗiyya na buƙatar jam’iyyu masu ƙarfi da adawa mai inganci. Da zarar an kammala shari’ar jam’iyyarmu, In Sha Allah, ADC za ta fito da ƙarfi ta kuma yi nasara a zaɓe mai zuwa,” in ji shi.
Taron ya ƙare ne da kiran haɗin kai, sadaukarwa da jajircewa daga dukkan masu ruwa da tsaki, domin ƙarfafa ADC a matsayin jam’iyyar da ke neman kawo sauyi mai ma’ana a jihar Kano.
