Sojoji sun halaka mayaƙan ISWAP 50 da ƙwato makamai a Yobe

Spread the love

Dakarun rundunar Atisayen HAƊIN KAI sun kashe aƙalla mayaƙan ƙungiyar ISWAP 50 tare da ƙwato makamai masu yawa bayan wani hari da aka kai a hedikwatar Birgetta 27 da ke Buni Gari a Jihar Yobe.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin-gwiwa ta Arewa maso Gabas, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce ‘yan ta’addar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 2 na dare daga wurare daban-daban domin kutsawa sansanin sojojin.

Sanarwar ta ce dakarun sun yi amfani da ƙarfin wuta da dabarun yaƙi wajen dakile harin, lamarin da ya jawo mutuwar mayaƙa da dama tare da tilasta wa sauran tserewa daga yankin.

Rundunar ta bayyana cewa an ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda takwas, bindigogin GPMG biyu, harba roka RPG biyu, bama-baman RPG guda biyar da sauran alburusai da kayan yaƙi.

Ta kuma ce jiragen saman rundunar sun taimaka wajen kai hare-haren sama kan wuraren da ‘yan ta’addan suka fake da kuma waɗanda ke ƙoƙarin tserewa.

Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin artabun, yayin da wasu motocin yaƙi suka samu ƙananan lalacewa.

Sojojin sun ce sun fara sintiri da bibiyar ‘yan ta’addan da suka tsere domin hana su sake haɗuwa a yankin.

By Babaji