Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar APC ta sanar da cewa ta sallami sharuɗɗan tantance Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ba shi damar shiga zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa ba tare da sake bayyana a gaban kwamitin tantancewa ba.
An cimma wannan matsaya ne a taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) karo na 188 da aka gudanar ranar Laraba, 6 ga Mayu, 2026, a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Feliɗ Morka, ya fitar, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bisa ikon da kundin tsarin mulkin APC ya bai wa kwamitin NWC na shirya da kula da zaɓukan fidda gwani tare da bayar da rangwame a lokuta na musamman domin muradun jam’iyyar.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya riga ya samu cikakken goyon baya da amincewa daga manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, ciki har da ƙungiyar gwamnonin APC (PGF), shugabannin Majalisar Tarayya da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar tun a babban taron APC na ƙasa da aka gudanar ranar 22 ga Mayu, 2025.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa kasancewar Tinubu shugaban ƙasa mai ci kuma jagoran APC, wanda aka riga aka tantance kuma aka amince da shi kafin zaɓen fidda gwani na 2022, sake buƙatar ya bayyana a gaban kwamitin tantancewa a yanzu abu ne mara amfani kuma ba dole ba.
