01
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata mummunar gobara ta yi ajalin wasu mutum biyu ta kuma lalata bukkoki 200 a wani sansanin ’yan gudun hijira da ke Bulabulin Damasak a yankin ƙaramar Hukumar Mobbar ta Jihar Borno. Majiyoyin tsaro sun ce, gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe a ranar 28 ga Afrilu, 2026, a sansanin da ke ɗauke da mutane daga al’ummomi sama da 10. Rahotanni sun nuna cewa gobarar wadda ta riƙa yaɗuwa cikin sauri saboda yanayin bukkokin da aka yi wa rufi da ciyawa, ta yi sanadiyyar mutuwar mata biyu da ba a…
