29
Apr
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnonin jihohin Kwara, Sokoto da Yobe za su ƙaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar a jihar Katsina. A wata hira da manema labarai a gidann gwamnatin Katsina, kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango yace gwamnan jihar Yobe Mai Mala Nuni zai ƙaddamar da hanyar Ingawa, Dutsi zuwa Shargalle. Shi kuma gwamnan Sokoto Dr Ahmed Aliyu zai ƙaddamar da hanyar Yan Ɗaki, Shinkafi zuwa Kofar Soro a ƙaramar hukumar Katsina. Sai gwamnan jihar kwara da zai buɗe kafafen makaranta na sakandare na musamman a garin Raɗɗa a karamar hukumar charanchi.…
