Gwamnan Kano ya sayi fom ɗin takarar zango na biyu

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sayi fom ɗin takara domin neman
takarar gwamna a karo na biyu.

Rahotanni sunce Muhammad Jamo ne ya karɓi fom din a madadinsa a Abuja a ranar Talata.

Muhammad Jamo ya wakilci gwamnan ne wajen karɓar fom din, a wani mataki da ya ƙara jawo hankulan masu bibiyar siyasar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa da ƙulla sababbin dabaru gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda manyan ‘yan siyasa ke fara nuna alamun tsayawa takara da kuma faɗaɗa tasirinsu a fagen siyasa.

By ukarofi