
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da umarni da a gaggauta kammala aikin titin Nnamdi Azikiwe domin rage yawaitar aukuwar haɗurra da suke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
Wannan Matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki suka gudanar bisa umarnin Gwamna Uba Sani, wanda ya nuna matukar damuwarsa kan karuwar hadurra a kan titin mai tsawon kilomita 21.5.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana damuwar gwamnan tare da jaddada bukatar daukar matakin gaggawa.
Ya ce, “Mai girma Gwamna ya nuna matukar damuwa kan asarar rayukan da ake yi a wannan hanya. Babu wani cigaba da zai iya zama hujjar rasa ko da rai guda. Wannan lamari ba za a iya jurewa ba, dole ne a dauki mataki nan take,” in ji shi.
Taron ya hada manyan masu ruwa da tsaki ciki har da wakilan Ma’aikatar Ayyuka ta tarayya, hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) hukumar kula ababen hawa ta jihar Kaduna (KASTELEA) da kuma babban kamfanin da ke aikin masana’antun Dangote da kuma kamfanin da suke aikin gina titin wato Dantata & Sawoe. Haka kuma shugabannin kungiyoyin sufuri kamar NARTO, NURTW da ACCOMORAN sun halarta.
Maiyaki ya bayyana cewa duk da cewa an bayar da kwangilar aikin tun a shekarar 2021 kafin zuwan wannan gwamnati, aikin ya yi tafiyar hawainiya har sai da Gwamna Uba Sani ya shiga tsakani.
“Tun bayan sa hannun gwamna kai tsaye, an samu ci gaba mai kyau. Amma hakan kadai bai isa ba yanzu dai kammala aikin cikin lokaci ya zama wajibi,” in ji shi.
Rahotanni daga jami’an kula da hanyoyi na tarayya da kuma masu aikin sun nuna cewa an kammala kusan kilomita 19 na titin. Duk da cewa an tsara kammala aikin a watan Disambar 2026, gwamnan ya bukaci a kawo karshen aikin kafin lokacin.
“Gwamna ya bayyana karara cewa dole ne a kammala aikin kafin wa’adin da aka tsara. Ba za a amince da wani jinkiri ba.”
Domin tabbatar da bin wannan umarni, gwamnatin ta kafa wani kwamitin hadin gwiwa na hukumomi da zai rika sa ido kan aikin da kuma tabbatar da tsaron hanya, musamman a lokacin damina.
Kwamitin wanda Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ke jagoranta ya hada da FRSC, KASTELEA, jami’an Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, masu kwangila, wakilan al’umma, sarakuna da kungiyoyin sufuri. Haka kuma Ma’aikatar Yada Labarai an dorawa alhakin wayar da kan jama’a domin sauya halayen amfani da hanya.
Maiyaki ya jaddada cewa halayen masu amfani da hanya na daga cikin manyan dalilan haddura, inda aka gano wurare masu hadari da ke bukatar kulawa ta musamman.
“Baya ga ingancin titi, halayen mutane na da matukar tasiri. Muna aiki tare da al’umma domin tabbatar da bin ka’idojin hanya. Dole ne a kawo karshen tukin ganganci.”
Ya kuma kara da cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa aikin ya dace da ka’idojin kasa da kasa, ba kawai wajen gina titi ba, har ma da yadda ake amfani da shi.
Wannan mataki na gwamnati ya biyo bayan matsin lamba daga shugabannin al’umma da kungiyoyin matasa, wadanda suka bayyana halin da ake ciki a matsayin matsalar tsaro mai tsanani da ke da illa ga tattalin arziki da zamantakewa.
Gwamnatin jihar ta ce da sabbin matakan da aka dauka, tana da kudurin dawo da tsaro, gaggauta kammala aikin, da kuma tabbatar da cewa titin Western Bypass ya cika manufarsa ba tare da kara asarar rayuka ba.


