
Aƙalla mutum 29 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kai hari kan al’ummar Guyaku da ke ƙaramar hukumar Gombi a jihar Adamawa.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin ƙauyen ne da daddare ranar lahadi, inda suka riƙa harbe-harbe na sa’o’i da dama, lamarin da ya janyo asarar rayuka tare da lalata dukiyoyi.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya tabbatar da adadin yawan waɗanda suka mutu yayin da ya kai ziyara yankin, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu tare da bayyana harin a matsayin abin takaici da ba za a lamunta da shi ba.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa, gwamnan ya ce gwamnati na ƙara ƙaimi wajen ɗaukar matakan tsaro domin dawo da zaman lafiya, yana mai cewa za a hukunta waɗanda suka aikata wannan ta’asa.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar yankin cewa gwamnati za ta cigaba da tallafa musu tare da sake gina abin da ya lalace.
Har zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai jihar Adamawa na fuskantar irin waɗannan hare-hare tsawon shekaru, musamman daga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ciki har da boko haram.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam na Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan, tana mai kira ga hukumomi da su ƙara ƙoƙari wajen kare rayukan fararen hula da kuma tabbatar da an hukunta masu hannu a lamarin.
