ukarofi

12570 Posts
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da tallafin kayan aiki ga mutane 1,162

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da tallafin kayan aiki ga mutane 1,162

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya raba kayan fara sana’a ga matasa 1,169 da suka kammala shirin horaswa kan kanikanci ƙarƙashin shirin Mechatronics Apprenticeship Support Programme (MASP).Shiri ne wanda hukumar bunƙasa kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA) ta gudanar tare da haɗin gwiwar Nigerian Automobile Technicians Association (NATA), na da nufin bai wa matasa ƙwarewar sana’o’in zamani domin dogaro da kai. Da yake jawabi a wajen taron,Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa shirin na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatinsa na bunƙasa sana’o’i da samar da ayyukan yi ga matasa. “Wannan shiri wata muhimmiyar hanya ce…
Read More
Gwamnan Katsina ya taya DC Saulawa murnar samun muƙamin Provost Marshal

Gwamnan Katsina ya taya DC Saulawa murnar samun muƙamin Provost Marshal

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya mataimakin kwanturola na hukumar kwastam ta ƙasa (Nigeria Customs Service), DC Sanusi Tasiu Saulawa, murnar naɗa shi a matsayin Acting Provost Marshal na hukumar. Gwamnan ya bayyana naɗin a matsayin wata babbar shaida ta ƙwarewa, riƙon amana, da nagartar aiki da DC Saulawa ya nuna a tsawon lokacin da yake hidima ga ƙasa. A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a Muhammad Kaula ya sanya wa hannu ya ce Gwamnan ya bayyana cewa wannan karin girma na nuna yadda ake ƙara yarda da ‘yan asalin Jihar…
Read More
Katsina United ta hana ‘yan wasan ta shiga wata ƙungiya ba tare da sanin ta ba

Katsina United ta hana ‘yan wasan ta shiga wata ƙungiya ba tare da sanin ta ba

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar gudanarwar Katsina United ta gargaɗi 'yan wasa da jami’an da ke cikin tsarin karɓar albashin a ƙungiyar,kan hana su shiga ko wakiltar wata ƙungiya ba tare da izinin ta ba a rubuce. Shugaban ƙungiyar Alhaji Surajo Baba Malumfashi, ya faɗi haka a wata sanarwa ɗauke da sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na ƙungiyar Malam Nasiru Gide. Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Katsina United yayi gargaɗin duk ɗan wasan da aka samu da wannan laifi ya kuka da kansa. Sirajo Malumfashi yayi kira ga ɗaukacin 'yan wasan da jami'an ta da su cigaba da…
Read More
Za mu daɗe muna yabon auren ƙabilu muna kushe namu

Za mu daɗe muna yabon auren ƙabilu muna kushe namu

Daga UNCLE LARABI Mata sun fi son a yi musu ƙarya, ko na kalamai ne, a neman aure, amma idan an yi aure cefane da neman abinci ba zai bayar da damar wannan yin ƙaryar ba tunda komai na zahiri ya gama bayyana. To, shi ya sa ake shan wahalar zamantakewa a gidajen Bahaushe na aure, saboda ba ma amfani da zahiri da gaskiya wajen neman auren. Mun fi son ƙarya da burgewa. Za mu daɗe muna cewa auren wasu ƙabilun yafi ƙarko. Misali; idan ku ka ɗauki ƙabilar Edo, Musulmai, ba Kirista ba, idan namiji zai yi aure sai…
Read More
’Yan Nijeriya akwai ƙura fa

’Yan Nijeriya akwai ƙura fa

Daga ALI ABUBAKAR SADIƙ Kimanin sati biyu da suka gabata na yi wani rubutu mai taken "Manaƙisar Amurka Ga Arewa." Abubuwa biyu ne suka faru a wancan lokaci. Na farko shine, sanarwar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran. Na biyu kuma shine, bayanin ƙasar Amurka na umarta ma'aikatan jakadanci da ’yan ƙasarta su bar Nijeriya da kuma nesantar jihohin Arewa. Kamar yadda na bayyana a wancan rubutu cewa, tunda Iran ta gagari Amurka, inda ta kasa cimma muradinta da kuma datse mashigin Hormuz da Iran ta yi, wanda ya janyo tashin gwauron zabi na farashin mai a duniya, yanzu Nijeriya…
Read More
A daina siyasantar da sha’anin tsaro 

A daina siyasantar da sha’anin tsaro 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Rahotanni daga kafafen watsa labarai daban-daban sun rawaito Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio yana danganta ƙaruwar taɓarɓarewar tsaro da ake fuskanta a kasa na da alaƙa da shiga kakar zaɓe da ake ciki, inda yake nuni da cewa abubuwan da ke faruwa an shirya ne domin daƙile ayyukan alherin da gwamnati mai ci ke yi. Yana mai cewa rikice-rikice na ƙaruwa ne saboda wasu 'yan adawa na ɗaukar nauyin hakan, har yana hasashen cewa da zarar an kammala hidindimun Babban Zaɓen 2027 cikin makonni biyu za a ga komai ya dawo daidai.  Waɗannan kalamai na Shugaban…
Read More
Ba alheri a kafa gungun ƙabilanci

Ba alheri a kafa gungun ƙabilanci

 Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Na ga wasu na rubuta wai ana yaƙi da masu kafa ƙungiyar Hausa zalla wanda sam-sam ba haka ba ne. Shin an kafa ƙungiyar ko har yanzu shiri a ke yi? Idan an kafa to me ƙorafin? In kuma shirin kafawa a ke yi wa ya rike wani ya hana shi kafawa? Mutane ne daban-daban kuma ko ƙungiyar za su kafa ba zai taɓa yiwuwa su kafa guda ɗaya ba. Yanzu ma haka su na nan su na cin zarafin juna don ba wani Bahaushe ko mutumin kirki da duniya ta sani a cikin su. Gara…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan bindiga sun kashe mutane 11 tare da raunata mutum 2 a ƙauyen Gurbi da ke ƙaramar hukumar Ƙankara na jihar Katsina. A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce haɗin gwiwar jami'an tsaro ƙarƙashin DPO na Ƙanƙara sun kai ɗauki a ƙauyen. Sai dai acewar sa bayan da yan bindigan suka hango jami'an tsaron sai suka ranta a na kare. DSP ya bayyana cewa a halin yanzu zaman lafiya ya dawo a ƙauyen a dai dai lokacin da…
Read More
Ɗan hidimar ƙasa ya rasu sanadin artabu tsakanin sojoji da ‘yan fashi a Abuja

Ɗan hidimar ƙasa ya rasu sanadin artabu tsakanin sojoji da ‘yan fashi a Abuja

Daga USMAN KAROFI Wani mai wa ƙasa hidima mai suna Abdulsamad Jamiu ya rasu bayan ya shiga tsakiyar musayar wuta tsakanin ‘yan fashi da jami’an tsaro a yankin Dei-Dei da ke Abuja. Lamarin ya faru ne da asubahin ranar 25 ga Afrilu, 2026, a Shagari Estate, lokacin da sojoji suka amsa kiran gaggawa kan harin fashi. A cewar rundunar sojin Najeriya, jami’ansu na sintiri ne lokacin da suka isa wurin kuma suka gamu da harbin bindiga daga ‘yan fashin da ke ƙoƙarin tserewa. Wannan ya janyo musayar wuta mai tsanani tsakanin sojojin da maharan, inda a cikin rikicin Abdulsamad ya…
Read More
Majalisar Kano ta amince da Murtala Garo a matsayin mataimakin gwamna

Majalisar Kano ta amince da Murtala Garo a matsayin mataimakin gwamna

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Majalisar dokokin jihar Kano ta amincewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano. Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar sunan Murtala Sule Garo domin tantance shi ta kuma amince masa ya naɗa shi a kujerar mataimakin gwamnan Kano . A ranar 27 ga watan mayu, 2026 ne dai tsohon mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye muƙaminsa bayan wata rashin jituwa da suka samu da Gwamna saboda ya gaza binsa zuwa jam’iyyar APC…
Read More