27
Apr
Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Jam'iyyar African Democratic Congress ADC a Jihar Zamfara ta zaɓi sabin shugabannin ta na Jiha ta hanyar yarjejeniya da sasanci, inda Alhaji Kabiru Garba Gusau ya zama shugaban jam'iyyar na jiha. An gudanar da taron amincewa a yau Litinin a babban masaukin baƙi watau Command Guest in dake a Gusau. Sauran manyan shugabanin da aka zaɓa sun haɗa da, Kabiru Aliyu Bakura mataimakin shugaban jam'iyya, Sanusi Falalu, sakatare, Abdullahi Dahiru Odita, Ganiya Sani shugabar mata da Abdulkarim Umar a matsayin sakataren yaɗa labarai da sauransu. A jawabinsa na amincewa, sabon shugaban jam'iyya, Kabiru Garba Gusau,…
